Kusan duk mako sai hukumar ta NDLEA ta sanar da kamen da take yi a kasar. Hoto/NDLEA

Hukumar da ke yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA ta ce ta kama akalla mutum 534 wadanda take zargin suna ta’ammali da miyagun kwayoyi a wasu jihohin kasar.

Hukumar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ta kama su da dumbin miyagun kwayoyi wadanda suka hada da hodar ibilis da heroin da methamphetamine da kwayar tramadol.

Sauran sun hada da maganin tari na codeine da tabar wiwi da kuma wasu sabbin miyagun kwayoyi.

Hukumar ta bayyana cewa ta kama su ne bayan ta kaddamar da wani shiri na musamman na kai samame mai taken ‘Operation Mop Up’ wanda aka kaddamar domin kama masu laifi da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi kafin rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayu.

NDLEA ta bayyana cewa cikin jihohin da ke kan gaba wurin kamen sun hada da Legas da Kano da birnin Abuja da Kaduna da Bayelsa da Adamawa da Osun da Benue da kuma Filato. Kusan duk mako sai hukumar ta NDLEA ta sanar da kamen da take yi a kasar.

A cikin watan nan na Mayu hukumar ta ce ta kama tireloli biyu dauke da tabar wiwi a Legas da nauyinsu ya kai kilo 8,852.

Sa’annan a watan da ya gabata hukumar ta ce ta gano wani kamfani da ake hada A-kuskura a garin Mubi na Jihar Adamawa da kuma wani kame da ta yi na wani dan kasar Suriname dauke da hodar ibilis har kilo 9.9 da aka kunshe ta cikin kwaroron roba.

TRT Afrika