Mayakan Boko Haram dari biyar da sha daya da suka hada da iyalansu ne suka mika wuya ga rundunar sojin Nijeriya a yankuna da dama na arewa maso gabashin kasar.
Kakakin rundunar sojin kasar Manjo Janar Musa Danmadami ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ranar Alhamis a Abuja, babban birnin kasar.
Ya ce wadanda suka mika wuyan sun hada da maza 99, mata 161 da kananan yara 251 a yankuna daban-daban da sojoji suke gudanar da ayyukansu.
‘Yan Boko Haram 974 sun mika wuya a Nijeriya
A cewarsa, dakarun sojin sun kashe “mayakan Boko Haram/ISWAP 26, an kama mutanen da ke taimaka wa 'yan ta'addan da kayan aiki su 25 da wanda yake musu leken asiri guda daya da kuma wani mayakin kungiyar."
“Kazalika dakarunmu sun ceto daya daga cikin 'yan matan Chibok yayin da jimillar mambobi 511 na kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram/Islamic State of West Africa Province da iyalansu da suka hada da maza 99, mata 161 da kananan yara 251 suka mika wuya ga dakarunmu a yankuna daban-daban,” in ji sanarwar.
Gwamnatin Nijeriya, karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari, ta sha jaddada aniyarta ta kawar da kungiyar Boko Haram tun da aka zabe ta a 2015.
Masana harkokin tsaro sun yaba wa gwamnatin bisa wannan kokari, ko da yake suna sukarta bisa yadda wasu matsalolin rashin tsaro da suka hada da satar mutane don karbar kudin fansa suka addabi kasar.