Jakadan Amurka a Nijeriya, Richard Mills ya yi watsi da zarge-zargen cewa Hukumar Amurka da ke Taimakon Kasashen Waje (USAID) tana ɗaukar nauyin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci.
Mills, wanda ya gana da mambobin ƙungiyar Gwamnoni Ta Nijeriya a Abuja ranar Laraba da daddare, ya ce babu wata hujja da za ta iya tabbatar da zargin hakan.
Ya bayyana cewa babu ƙasar da ta kai Amurka yin tur da Allah wadai da Boko Haram, inda ya tabbatar da cewa idan dai aka gano wata sahihiyar hujja, to gwamnatin Amurka za ta yi aiki da ta Nijeriya don yin bincike.
“Babu wata hujja ko kaɗan kan wannan kawar da hankalin, kuma idan har an taɓa samun hujjar da ke nuna akwai wani shirin tallafi da aka yi amfani da shi ba daidai ba a kan Boko Haram, to za mu yi gaggawar bincike tare da abokan hulɗarmu na Nijeriya,” in ji Mills.
“Muna haɗa kai da gwamnatin Nijeriya wajen bincike. Zan iya tabbatar muku cewa muna da tsauraran ƙa’idoji da matakai na tabbatar da cewa ba a karkatar da duk wani tallafi na USAID ko na Sashen Tsaro ko Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ba, wajen tallafa wa ƙungiyoyi irin su Boko Haram.
“Don haka idan aka zo batun Boko Haram, Amurka na tare da Nijeriya wajen ganin ƙasar ta magance tasiri da ɓurɓushin duk wani abu da ƙungiyar ke wakilta.
“Bari na yi bayani sosai – Nijeriya ba ta da wata ƙawa mai ƙarfi da take taya ta yin tur da ta’addancin Boko Haram kamar Amurka.
"Mun ayyana Boko Harama a matsayin ƙungiyar ta’addanci tun shekarar 2013, inda muka hana ƙungiyar tura kadarori Amurka da kuma ba mu damar kama mambobinta.”
Zargin USAID
Tun da fari a ranar 13 ga watan Fabrairu ne wani ɗan majalisar dokokin Amurka, Scott Perry ya zargi hukumar USAID da tallafa wa ƙungiyoyin ta'addanci da suka haɗa da Boko Haram.
Perry wanda ɗan jam'iyyar Republican ne daga Pennsylvania, ya yi wannan ikirarin ne a yayin wani zama ne kan yadda za a rage kashe kudin gwamnatin kasar.
Kalaman na Scott Perry sun jawo zazzafan martani da muhawara a ciki da wajen Nijeriya.
Ko a ranar Larabar nan sai da Majalisar Dattijan Nijeriya ta nemi ganin Babban Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribado da Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Nijeriya NIA da Sashen Tattara Bayanan Sirri na hedkwatar tsaron Nijeriya (DIA) kan zarge-zargen da aka bijiro da su cewa Hukumar Amurka da ke Taimakon Kasashen Waje (USAID) tana ɗaukar nauyin ta'addanci.
Da ma idan za a tuna a kwanan baya ne Babban Hafsan Tsaron Nijeriya Janar Christopher Musa ya yi zargin cewa wasu kasashen ketare suna taimaka wa kungiyar Boko Haram da kudi da kuma makamai.
Nijeriya ta kwashe tsawon shekara fiye da 15 tana yaki da mayakan kungiyar Boko Haram, abin da ya jawo asarar dubban rayuka jama’a da raba miliyoyin mutane da muhallinsu.
Rikicin Boko Haram ya fi yin kamari ne a shiyyar Arewa maso Yammacin Nijeriya musamman a jihohin Borno da Yobe.
Shi ma a nasa bangaren dan majalisar wakilai daga jihar Borno wato Sanata Ali Ndume ya bukaci gwamnatin Nijeriya da kuma majalisar dokokin kasar da su gudanar da bincike kan wadannan zarge-zarge don gano gaskiyar al’amarin.
Ko da yake wasu ’yan kasar suna cewa kalaman dan majalisar Amurka da na babban hafsan tsaron kasar suna da kamshin gaskiya, wasu kuma suna ganin wadannan zarge-zarge ne kawai kuma sun ci karo da hankali saboda Boko Haram a shekarun 2010 ta fara ne da kashe ’yan sanda da sauran jami’an tsaro a cikin Maiduguri kuma sai ta dauke makaman da jami’an tsaron ke amfani da su.
Daga bisani kuma wasu mayakan kungiyar sun rika kai hare-hare bankuna, inda suke kwashe kudin da ke bankunan.
Siyasa
Shugaban kamfanin tsaro na Beacon Consulting a Nijeriya kuma masanin kan al’amuran da suka shafi tsaro Malam Kabiru Adamu ya ce kalaman dan malisar wakilan Amurkan Scott Perry dan jam’iyyar Republican kalamai ne na siyasa kuma babu wata hujja a kasa da take nuna cewa Amurka tana daukar nauyin Boko Haram.
Masanin tsaron ya ce idan za a tuna tun lokacin yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump yake kokawa kan yadda kasar take kashe makudan kudi da ba su kamata ba kuma ya nuna jam’iyyar da take mulki a lokacin wato jam’iyyar Democrat ta yi kura-kurai masu yawa.
Ya ce saboda haka ne sabuwar gwamnatin Trump ta kafa ma’aikatar da za ta rage yadda ake barnatar da kudin gwamnatin kasar.
Malam Kabiru Adamu ya ce a fahimtarsa kalaman na dan majalisar Amurkan kalamai ne na dan siyasa kawai saboda babu wata hujja da za ta gasgata kalaman nasa.
Kazalika ya ce babu shakka akwai wasu kasashe da suke goyon bayan kungiyoyin ta’addanci a sassan duniya daban-daban, amma kuma babu wata hujja a kasa da take nuna cewa hukumar USAID tana goyon bayan wata kungiya ta ta’addanci a duniya