Rundunar Sojin Nijeriya ta kashe ‘yan ta’adda 358 da kuma kama mutum 431 da ake zargi da ta’addanci a Janairun 2025.
Daraktan watsa labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya Manjo Janar Edward Buba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Janar Buba ya ce jami’an sojin ƙasar sun samu wannan nasara ne a ci gaba da suke yi da yaƙi da ta’addanci a faɗin ƙasar.
Haka kuma ya bayyana cewa jami’an sojin ƙasar sun kama mutum 59 waɗanda ake zargi da satar man fetur da kuma ceto mutum 249 waɗanda aka yi garkuwa da su.
Sanarwar ta bayyana cewa a yankin kudu maso kudancin Nijeriya, jami’an tsaron sun daƙile satar man fetur wanda ya haura fiye da naira biliyan biyu.
Haka kuma sanarwar ta ƙara da cewa jami’an tsaron sun ƙwato makamai 370 da harsasai 4,972 waɗanda suka haɗa da AK45 105 da bindigogin da aka ƙera cikin gida 25 sai kuma bindigar harba-ruga 32.
Janar Buba ya kuma ce jami’an tsaron sun ƙwato bindiga ƙirar pump action 23 sai kuma harsasai na musamman 3,066 na 7.62mm da harsasai 758 na 7.62mm NATO, da kwanson harsasai 980 da bindigogi 72 na musamman da harsasan su 500.
Ana yawan samun matsalolin tsaro a Nijeriya musamman arewacin ƙasar inda ake fama da mayaƙan Boko Haram da kuma ɓarayin daji masu garkuwa da mutane.
Sai dai jami’an tsaron ƙasar na cewa suna samun gagarumar nasara a yaƙin da suke yi da ta’addanci a ƙasar.