Ana yin wani taron kwararru a fannin tsaro daga kasashe 10 na yankin Sahel da Sahara da kuma nahiyar Turai wanda kungiyar Eucap Sahel ta shirya a babban birnin Jamhuriyar Nijar, Yamai.
Taron yana nazari ne kan hanyoyin shawo kan matsalolin tsaro masu nasaba da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Ministan Harkokin cikin Gidan Nijar Malam Hamadou Adamou Souley ya ce batutuwan da taron ya mayar da hankali a kansu sun hada rawar da fararen-hula za su taka a fannin yaki da ta'addaci.
Har ila yau ya ce idan ana so a yi nasara a kan wannan matsalar ta yaduwar hare-haren ta'addacin a kan kasashen yankin Sahel, to sai an hada da matakan kiyaye hakkin dan Adam da kuma bin doka da oda.
"Akwai bukatar samar da wani tsari na fahimtar juna tsakanin al'umma wanda hakan zai sa a yi watsi da tsauraran akidu da ra'ayi a yakin Sahel," in ji shi.
Kungiyar Tarayyar Turai ce ta dauki nauyin shirya wannan taron a karkashin kungiyar Eucap Sahel wacce ke kula da taimaka wa kasashen yankin Sahel wajen yaki da ta'addanci.
Jakadan Kungiyar Tarayyar Turai a Nijar Salvador França ya kwatanta ta'addanci da wata annoba wacce ba ruwan ta da iyaka.
Kuma ya ce nahiyar Turai tana makwabtaka ta kai-tsaye da wannan yankin da ke fama da wannan matsalar ta ta'addanci.
"Abu ne da ke matukar tayar mana da hankali sosai, lalle yaki da ta'addanci shakka babu abu ne da ke da bukatar daukar matakan soji," in ji jakadan.
Hakazalika ya ce taron zai ba mahalartansa damar tattara wasu fasahohi da kuma dabarun yaki da ta'addanci wanda irinsu ne suka sa aka yi nasara a wasu kasashen duniya.
Taron wanda za a kwashe tsawon kwana uku ana yi, zai ba kwararru a fannin yaki da ta'addanci damar gabatar da makaloli 10 a kan girman ta'addanci a yankin Sahel, san nan da irin bambance-bambancen da ke tsakanin ta'addanci a Sahel da wanda ake fuskanta a nahiyar Turai.
Kuma za a gabatar da shawarwari don tunkarar matsalar baki daya.