Kungiyoyin direbobin manyan motocin dakon kaya da na man fetur, SDRN da SNCRN, sun shiga yajin aiki na kwana biyu, daga ranar Alhamis 25 zuwa Juma'a 26 ga watan Mayu.
Da yake tattauna wa da manema labarai, daya daga cikin shugabannin kungiyoyin, Malam Ouseini Maizoumbou ya ce kungiyoyin nasu sun tsunduma wannan yajin aiki ne saboda tarin matsalolin da suke fuskanta.
Daga cikin manyan matsalolin akwai yawan shingayen bincike na ‘yan sanda da ake sawa a kan hanyoyi, “inda ‘yan sandan ke takura wa direbobin da kuma amsar na goro a hannunsu.”
Ya kara da cewa akwai kuma wata matsalar wacce direbobin motocin dakon man fetur ke fuskanta tun wajen yin lodi daga matatar fetur ta SORAZ, inda suka ce ana tauye yawan man da suka saya ta yadda ba a cika tankunan nasu da kyau.
Kafin kungiyoyin su shiga wannan yajin aikin sun gana da Ma'aikatar Harkokin Sufiri, sai dai ba su samu fahimtar juna ba.
Kungiyoyin sun ce wannan yajin aikin na kwana biyu tamkar na jan kunne ne matsawar ba su samu biyan bukata ba to a gaba za su yi na kwana uku.