Kungiyoyin kwadagon sun ce janye tallafin man fetur ya jefa 'yan Nijeriya cikin mawuyacin hali. Hoto/Festus Keyamo

Kungiyoyin kwadago a Nijieriya na NLC da TUC sun dakatar da yajin aikin da suka yi niyyar shiga a ranar Laraba sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi a kasar.

Sun dauki matakin ne bayan tattaunawar da wakilan kungiyoyin suka yi da wakilan gwamnatin Nijeriya a fadar shugaban kasar da ke Abuja ranar Litinin da tsakar dare.

Haka kuma kafin bangarorin su cimma matsaya, wani umarni na Kotun Ma’aikata ya dakatar da kungiyoyin kwadagon daga shiga yajin aiki bayan karar da gwamnatin tarayyar kasar ta shigar.

Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, wanda kuma a halin yanzu shi ne sabon shugaban ma’aikata na shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya fitar da sanarwa kunshe da bayanai kan tattaunawar da kuma yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangaren ‘yan kwadagon da gwamnatin tarayya.

Ga abubuwa bakwai da aka cimma matsaya kansu da suka sa kungiyoyin na NLC da TUC suka janye yajin aikin:

- Gwamnatin tarayya da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC su kafa kwamitin hadin gwiwa domin duba bukatar karin karancin albashi da kuma tsara lokacin da za a aiwatar da hakan.

- Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin NLC da TUC su sake bitar tsarin tura kudi na Bankin Duniya wanda ake ba marasa karfi da kuma kokarin saka masu karamin albashi cikin tsari.

- Gwamnatin Nijeriya da kungiyoyin kwadago su sake farfado da tsarin CNG na motoci masu amfani da iskar gas wanda aka amince da shi tun a 2021 da kuma fitar da tsarin aiwatar da shirin.

- Kungiyoyin na kwadago da kuma gwamnatin Nijeriya su sake duba matsalolin da ke yin tarnaki a bangaren ilimi da kuma shawarwari kan yadda za a shawo kan lamarin.

- Kungiyoyin kwadago da gwamnatin tarayya su sake bita da aiwatar da tsarin da zai tabbatar an gyara matatun man fetur na kasar.

- Gwamnatin Nijeriya ta samar da tsari domin gyara hanyoyin kasar da kuma fadada layin dogo a fadin kasar.

- Haka kuma duka sauran bukatu wadanda TUC suka bayar ga gwamnatin tarayya kwamitin na hadin gwiwa zai sake duba su.

Wakilan kwadagon za su ci gaba da aiki da gwamnatin tarayya domin ganin aiwatar da wadannan bukatun. Hoto/NLC

Bayan cimma wannan matsaya, duka bangarorin na kwadago sun amince su janye yajin aikin domin su ci gaba da tuntuba.

Kazalika kungiyoyin na NLC da TUC za su ci gaba da aiki da gwamnatin tarayya domin ganin an cimma wadannan bukatu.

Kungiyoyin na kwadago za su sake tattaunawa da gwamnatin tarayya a ranar 19 ga watan Yuni domin amincewa da yadda za a aiwatar da tsare-tsaren.

Tun da farko sabon shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ne ya kafa kwamitin da zai tattauna da ‘yan kwadagon sakamakon yajin aikin da suka kudiri yi a ranar Laraba.

Duka wannan na zuwa ne bayan cire tallafin man fetur a kasar inda ake sayar da fetur din sama da naira 500 a duk lita.

Matakin da Shugaba Tinubu ya dauka na cire tallafin fetur na daga cikin alkawuran yakin neman zabensa kuma shi ne mataki na farko da ya soma dauka bayan rantsar da shi.

TRT Afrika