Wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda biyu a Karamar Hukumar Ngor Okpala ta Jihar Imo da ke kudancin Nijeriya.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Imo ASP Henry Okoye ya tabbatar wa TRT Afrika cewa lamarin ya faru ne a daidai kwanar Okpala inda ‘yan bindigan suka bude wa ‘yan sandan wuta.
Ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun je wurin cikin motoci biyu inda suka soma bude wuta, amma a cewar Mista Okoye, jami’an ‘yan sandan sun yi musayar wuta da ‘yan bindigan inda har suka kwace mota daya.
“’Yan sandanmu biyu sun rasa ransu sakamakon wannan harin, daya ya samu rauni,” in ji Mista Okoye Ya kuma bayyana cewa ana kyautata zaton ‘yan kungiyar da ke fafutukar kafa kasar Biafra wato Ipob ne suka kai harin.
Mista Okoye ya ce maharan sun gudu amma suna ci gaba da bincike yayin da ake farautar su.
Wannan harin na zuwa ne wata guda bayan da ‘yan bindigan suka kashe ‘yan sanda biyar da wasu ma’aurata a Karamar Hukumar ta Ngor Okpala da ke Jihar Imo.
Haka ma a kwanakin baya ‘yan bindigar sun yi kwanton bauna inda suka kashe jami’an hukumar civil defence biyar a yankin.