Shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka AU sun ja kunne game da yiwuwar mayar da nahiyar wani fagen yaki tsakanin manyan kasashen duniya.
Nahiyar, wacce ke da mutane biliyan 1.3, ta tsinci kanta a tsakiyar rikicin neman iko tsakanin manyan kasashen duniya, wanda ya rubanya tun bayan da Rasha ta soma yaki da Ukraine watanni 15 da suka gabata.
A daidai lokacin da kungiyar AU ke bikin tunawa da ranar da aka kafa kungiyar hadin kan kasashen Afirka a shekarar 1963, a wannan rana kasar Ukraine da kanta ta sanar da cewa tana son bunkasa alaka da Afirka.
"A cikin wannan yanayi na kasa da kasa da ake taho-mu-gama kan alkiblar siyasa mabambanta, muradin kowane bangare na iya mayar da Afirka fagen yaki," in ji shugaban Kungiyar AU Moussa Faki Mahamat.
"A wannan yanayi, da ribar da wasu za su samu za ta zama asara ga Afirka, dole ne mu bijire wa duk wata dabara ta amfani da mambobin kasashenmu don cimma wata manufa ta siyasa," in ji shi,i a wani jawabi da ya yi a hedkwatar AU da ke Addis Ababa babban birnin Habasha.
Moscow na neman zurfafa dangantakar siyasa, tattalin arziki da harkokin soji a Afirka da Asiya yayin da Rasha ke kara zama saniyar ware a fagen siyasar duniya sakamokon rikicinta da Ukraine.
Duk idanu na kan Afirka
Ministan harkokin wajen Ukraine, Dmytro Kuleba, wanda a yanzu haka ke rangadi zuwa nahiyar Afirka, a ranar Laraba ya bukaci wasu kasashen nahiyar da su kawo karshen rashin nuna halin “ko-in-kula” kan yakin.
A watan Fabrairu, kasashe 22 mambobin kungiyar AU suka kaurace ko kin kada kuri'a kan kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya bukaci Rasha ta janye daga Ukraine.
Biyu daga cikinsu - Eritrea da Mali - sun kada kuri'ar kin amincewa da kudurin.
A cikin wata sanarwa da ya fitar don bikin zagayowar ranar kasashen Afirka, Kuleba ya jaddada batun yunkurin karfafa huldar diflomasiyya tsakanin Ukraine da nahiyar.
"Muna son samar da wani sabon yanayi na hadin gwiwa bisa ga wasu ka'idoji guda uku: mutunta juna da moriyar juna da kuma moriyar ribantuwa da juna," in ji shi, yayin da yake bayyana shirin kafa sabbin ofisoshin jakadanci a Afirka da kuma gudanar da taron koli na Ukraine da Afirka.
Moscow da kanta ta shirya wani taron Rasha da Afirka da za a yi watan Yuli, bayan ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sergey Lavrov ya yi a wasu kasashen Afirka a farkon wannan shekara.
A wannan shekara ne kasar China da Amurka su ma suka aika ministocin harkokin wajensu zuwa nahiyar don inganta dangantakar diflomasiyya da ake gani wani mataki ne na nuna kishin gaba da suke da juna.
'Rikici da hare-haren ta'addanci na karuwa'
Faki ya yaba da nasarorin da kungiyar ta AU, mai wakilan kasashe 54, ta samu wacce ta gaji kungiyar hadin-kan Afirka ta OAU a shekarar 2002.
"Yancin kai da nasarar yaki da wariyar launin fata da samun gagarumin ci-gaban tattalin arziki da kimiyya da wasanni da fasaha na daga cikin gagarumar rawar da Afirka ke takawa a duniya da dai sauransu," in ji shi.
Ko da yake, Faki ya kuma bayyana koma-bayan da nahiyar ke fama da shi kamar rashin bin tsarin dimokuradiyya ta hanyar juyin mulki da yawan take 'yanci da cin zarafin jama'a da rashin tsaro da yaduwar ayyukan ta'addanci da bazuwar makamai da kuma illar sauyin yanayi.".
Duk da wahalhalun da ake fama da su, Faki ya ce a halin da ake ciki Afirka ta kasance "Jarumar nahiya", inda ya yi misali da matakin da ta dauka wajen yaki da cutar Covid-19.
Jagorar kungiyar ta Tarayyar Afirka AU na yanzu, Shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, ya yi Allah wadai da yadda ake gudanar da "harkokin mulki ba bisa ka'ida ba" lamarin da ya karu sosai a Afirka a 'yan shekarun nan.
"Da rikicin kasa da tsakanin kasashen Afirka, sannan har yanzu ayyukan ta'addanci na ci gaba da wanzuwa duk wadannan yanayi na kara barazana ga zaman lafiya da tsaro da tsarin demokradiyya da ci gaban nahiyarmu da ma wasu kasashenmu da dama."
Kazalika Assoumani ya tabo batun rikicin da ke tsakanin Janar-Janar din Sudan, wanda ya barke a tsakiyar watan Afrilu kuma ya ke ci gaba da wanzuwa duk da wasu yarjejeniyoyin sulhu da aka yi.
"Dole ne mu shawo kan 'yan'uwanmu a Sudan su amince da tattaunawa domin kawo karshen yakin 'yan uwantaka da kasar ke fama da shi a yanzu." In ji shi