Hukumomi a jihar Filato da ke arewacin Nijeriya sun sanya dokar hana fita ta awa ashirin da hudu a karamar hukumar Mangu sakamakon tashin hankalin da ke aukuwa a yankin.
Shugaban karamar hukumar Markus Artu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin din nan.
Hakan na faruwa ne yayin da rikici tsakanin manoma da makiyaya ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 13 a karshen makon, kamar yadda hukumomi da shugabannin al'umma suka tabbatar.
Markus Artu ya ce “an dakatar da duk wata zirga-zirgar ababen hawa. Jami'an tsaro da ma'aikatan gaggawa ne kawai za a bari su rika zirga-zirga."
Ranar Juma'a, wasu da ake zargi "matasan kabilar Berom" ne sun tare makiyaya biyar sannan suka kashe su a kauyen Rawuru, a cewar wani shugaban Fulani Nuru Abdullahi, a hirarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Lahadi.
A wani mataki da ake gani na ramuwar gayya ne, wasu da ake zargi Fulani ne sun kashe manoma 'yan kabilar Beron takwas a yankin na Rawuru, in ji wakilin 'yan kabilar ta Berom Pius Dalyop Pam kamar yadda ya yi wa AFP karin bayani.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Alfred Alagbo ya tabbatar da hare-hare na baya bayan nan da kuma adadin mutanen da aka kashe.
Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon kashe wasu makiyaya, sai dai bai bayyana takamaimai yawan mutanen da aka kashe ba a harin na farko.
An kashe fiye da mutum 120 a makonni kadan
Bayanai sun nuna cewa an kashe fiye da mutum 120 tun daga tsakiyar watan Mayu sakamakon hare-hare a jihar ta Filato.
Kazalika an raba sama da mutum 3,000 da muhallansu.
Hukumomi sun aika da karin jami'an tsaro "domin tabbatar da zaman lafiya" a yankunan da lamarin ke faruwa", a cewar Alagbo.