An kafa tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a DRC a shekarar 1999. Hoto: Getty Images      

Daga Brian Okoth

Tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (MONUSCO) ta fara janye aikinta a kasar.

A yayin wani taron manema labarai da aka yi a Kinshasa babban birnin DRC a ranar Litinin, Shugabar kungiyar ta MONUSCO Bintou Keita ta fada cewa ficewar tawagar ta biyo bayan nasarar matsayar da aka cimma kan yanayin shirin mika mulki.

Keita ta ce ba ta da tabbaci kan yaushe tawagar ta MONUSCO za ta bar DRC, amma tana gannin yiwuwar tafiyar tasu daga watan Agusta.

"Zuwa karshen watan Yuli, bisa bukatar Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, za mu aika da rahoto wanda zai ba da damar ba da sabon tsarin aiki a DRC," a cewarta.

Shugabar ta ce tana fatan "da zarar mun tafi, ba za mu dawo ba".

"Saboda muna fatan lamuran tsaro a kasar zai dawo gaba daya," in ji Keita.

Ta kara da cewa: “An soma dukkan wasu shirye shirye na ficewar MONUSCO daga DRC, sai dai muna bukatar janyewar cikin mutunci da lumana. Ba a warware wani aiki cikin yini daya ba."

Dadadden rikici

DRC dai ta sha fama da tashe-tashen hankula da aka dade ana yi, musamman a yankunan gabashin kasar inda kungiyoyin 'yan tawaye da suka hada da na M23 suka kwace ikon kasar.

Yankin ya dade ba zaman lafiya inda aka sha fuskantar kashe-kashe na gilla da fyade da sauran laifukan yaki a yankin da ba a samu zaman lafiya.

Tawagar ta MONUSCO ta musanta zargin da wasu bangarorin suka yi na cewa tana tausayawa 'yan tawayen M23.

“Wannan kungiya tuni ta taba kai mana hari. Ban san me ya sa kuke ganin muna da alaka da kungiyar ba. Ba mu da alaka da M23," in ji Keita.

Kungiyar ’ ADF na kara fadada'

Wakilan na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, wata kungiyar 'yan tayar da kayar baya, Allied Democratic Forces ADF, wacce a baya-bayan nan aka zarga da kai hari kan wata makarantar sakandare a yammacin Uganda tare da kashe mutum sama da 37, tana samun kudaden shigarta da ke bi ta wasu kasashe.

Keita ta ce kungiyar ADF na fadada zuwa wasu kasashe, inda ake ci gaba da daukar ma'aikata.

Gwamnatin DRC ta yi marhaba da ficewar MONUSCO daga kasar, tana mai cewa ya kamata a ''tsara'' ficewar don ba da damar mika dabaru da fasahar da ke tsakanin ma’aikatan wanzar da zaman lafiya wadanda ke kokarin barin aiki da jami’an tsaron yankin.

Patrick Muyaya, mai magana da yawun gwamnatin DRC, kana Ministan Sadarwa na kasar ya ce ba za su iya sanya wa MONUSCO wa'adin barin kasar ba, saboda "wasu abubuwa na ba zata wadanda ba za a iya mantawa da su ba" za su iya tasowa.

Muyaya ya yi maganar hakan ne yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da shugaban MONUSCO, Keita.

An kafa MANUSCO a 1999

An kafa MONUSCO ne a watan Yulin 1999 bayan rattaba hannu kan wata yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Lusaka tsakanin DRC da kasashe biyar na yankin wadanda suka hada da - Angola da Namibiya da Rwanda da Uganda da kuma Zimbabwe.

Bayan kisan kiyashin da aka yi a kasar Rwanda a shekarar 1994, wasu daga cikin wadanda suka haddasa rikicin sun tsere zuwa yankin Kivu mai makwabtaka da gabashin DRC.

A shekarar 1998 wasu daga cikinsu suka kaddamar da tawaye ga shugaban kasar ta DRC na lokacin Laurent Kabila.

Angola da Chadi da Namibiya da Zimbabwe sun yi alkawarin ba Kabila goyon baya na soji, sai dai ‘yan tawayen sun ci gaba da mamaye yankunan gabashin kasar.

An ba da rahoton cewa Rwanda da Uganda sun ba da goyon bayansu ga yunkurin ‘yan tawayen, wato ''Congo Rally for Democracy RCD''.

A wani mataki na kaucewa rikicin yankin mai hatsarin gaske, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a tsagaita wuta tare da janye dakarun kasashen waje.

Ya kuma bukaci sauran kasashen kan da kada su tsoma baki cikin harkokin cikin gida na DRC.

A sakamakon tsagaita wutar aka kai ga kafa MONUSCO.

TRT Afrika