Rundunar 'yan sandan Jihar Filato da ke yankin arewa ta tsakiyar Nijeriya ta ce abubuwa sun lafa bayan rikicin da ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 85 a farkon makon nan.
Kakakin 'yan sandan jihar, Alfred Alabo ya ce "an tura jami'an tsaro masu yawa yankin. Ya zuwa yanzu dai an samu kwanciyar hankali a yankin gaba daya."
‘Yan sanda sun ce an kama mutum biyar da ake zargi da hannu a tayar da rikicin.
Alkaluma sun tabbatar da cewa an kashe mutum 85 a rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma.
Kazalika bayanai sun ce sama da mutum 3,000 ne suka rasa matsugunansu sakamakon rikicin.
Lamarin ya faru ne a kauyen Mwaghavul da ke karamar hukumar Mangu ranar Talata.
Wasu mazauna yankin sun ce mahara sun kai farmaki kauyuka kusan 17, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 85.
A ranar Alhamis aka binne mutanen da suka mutun a wani katon rami.
“An gano gawarwaki 85,” kamar yadda shugaban karamar hukumar, Daput Daniel ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Shi ma Joseph Gwankat, shugaban al’umma daga kungiyar ci gaban ‘yan kabilar Mwaghavul, ya bayar da irin wannan adadi.
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA, ta ce dubban mutane ne suka rasa matsugunansu sannan an lalata gidaje da dama sakamakon rikicin.
"Mun samu jumullar mutum 3,683 da suka rasa matsugunansu," a cewar wani jami'in NEMA, Eugene Nyelong da ya shaida wa AFP, yana mai cewa za a kai wa mabukata agajin gaggawa.
Ya ce fiye da gida 720 ne suka lalace ko kuma aka rusa gaba daya.
Har ya zuwa ranar Alhamis ba a san adadin mutanen da suka ji rauni ba.
Gwankat ya bayyana cewa, mutum 57 ne suka ji rauni ana kuma jinyarsu a asibiti, yayin da Nyelong ya ce kimanin mutum 216 ne suka jikkata sakamakon hare-haren.
Ba a dai san ainihin abin da jawo hare-haren na wannan makon ba har zuwa yanzu.
Sai dai dama an saba rikicin kabilanci da kuma rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar.
Tsare wadanda ake zargi
Duk da cewa kakakin 'yan sandan Alfred Alabo ya ce komai ya lafa, wani dan majalisa da ke wakiltar Mangu da makwabciyarta Bokkos a majalisar wakilan tarayya, Solomon Maren ya ce har yanzu ana fama da tashe-tashen hankula a yankin.
“An yi ta harbe-harbe har tsawon sa’o'i biyu sannan mutane sun yi ta gudu don tsira da ransu” a cewar Mista Maren a hirarsa da kamfanin dilancin labarai na AFP
Ya ce “daruruwan mutane dauke da makamai” wadanda ba daga cikin al’ummarmu suka fito ba, su suka tayar da fitinar.
"Muna da kauyuka 17 da aka shiga aka lalata su gaba daya... kuma ya zuwa yanzu sama da mutum 100 ne suka mutu," in ji Maren.