Rundunar sojin Nijeriya ta ce wasu sojojinta da ke yin sintiri a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar sun yi hatsari.
Wata sanarwa da gidan talabijin na kasar, NTA, ya wallafa da safiyar Alhamis, ta ambato rundunar soji na cewa "dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun yi hatsari a yayin da suke sintiri a Arewacin Borno.
Runduna ta 3 da rundunar MNJTF sun tabbatar da cewa a cikin sojoji 30 da suka gamu da hatsarin babu wanda ya mutu."
Sanarwar ta kara da cewa yanzu haka sojoji bakwai da suka jikkata suna samun kulawa a asibitin 7 Div. da ke Maiduguri.
Kakakin runduna ta 3 Operation Hadin Kai kuma kyaftin na Multinational Joint Task Force, Babatunde Zubairu, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a Gajiram wanda ya rutsa da motar daukar kaya da ke dauke da sojoji kusan 30 da ke sintiri tsakanin Baga a arewacin Borno, in ji NTA.