Rundunar Sojin Somaliya wadda ke samun goyon bayan mayaƙan sa-kai ta daƙile wannan babban hari da 'yan ta'addan Al Shabab suka kai, inda sojojin suka kashe 'yan ta'adda fiye da 130, kamar yadda jami'an Somalia suka tabbatar.
Ƙungiyar ta kai harin ne da asuba a wurare da dama da sojojin Somaliya suke a yankin Middle Shabelle, daga ciki har da ƙauyukan El Ali Ahmed, Ali Fooldheere, Alkowsar da kuma Daarunimca.
“Jaruman sojojin kasa da mazauna yankin sun kashe Khawarij fiye da 130 a samamen,” in ji ma’aikatar yada labaran Somaliya a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Khawarij kalma ce da gwamnatin Somaliya ke amfani da ita wajen bayyana kungiyar ta'addanci ta Al Shabab.
Mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu ta wayar tarho cewa sun ji karar harbe-harbe da fashe-fashen abubuwa na tsawon sa'o'i bayan harin ta'addancin.
Ma'aikatar ta ce sojojin sun kuma kwace makamai masu yawa daga hannun 'yan ta'addan da suka tsere zuwa cikin dazuzzuka.
Fiye da wata guda kenan jami'an tsaro suna gudanar da farmaki kan 'yan ta'addan tare da ƙwato manyan yankuna daga hannunsu.
Kasar Somaliya dai ta shafe shekaru tana fama da matsalar rashin tsaro, inda babbar barazanar tsaron ke fitowa daga kungiyoyin ta'addancin al Shabab da Daesh.
Tun a shekara ta 2007, Al Shabab ke yakar gwamnatin Somaliya da kuma dakarun wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Somalia (ATMIS)—wata tawaga mai dimbin yawa da Tarayyar Afirka ta ba da izini kuma Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da umarni.
Kungiyar ta'addancin dai ta kara ƙaimi wurin kai hare-hare tun bayan da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya ayyana "yakin fito-na-fito" da a kanta.