Rundunar ‘yan sandan Nijeriya reshen Jihar Imo ta kashe ‘yan ta’addda shida na ƙungiyar Eastern Security Network ESN, inda uku daga cikinsu jagorori ne a ƙungiyar.
Mai magana da yawun ‘yan sandan Nijeriya Olumuyiwa Adejobi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
Daga cikin jagororin uku akwa Ifeanyi Anayo wanda aka fi sani da Zuma De Rock mai shekara 28 da Chukwuemeka Odionyenfe wanda aka fi sani da Nmimi mai shekara 22 da Kingsley Sunday mai shekara 21 waɗanda dukansu ‘yan asalin Ogube, Ihube ne da ke Ƙaramar Hukumar Okigwe da ke Jihar Imo.
Adejobi ya bayyana cewa ‘yan ta’addan shida da aka kashe su ne suka kai hari a gidan gyaran hali na Owerri a ranar 5 ga Afrilun 2021 haka kuma su ne suka kashe ‘yan sanda biyar a Umunna Okigwe a ranar 12 ga Disambar 2022.
Haka kuma ya bayyana cewa mutanen su ne suka ƙona ofishin ‘yan sanda na Arondizuogu a ranar 8 ga watan Fabrarirun 2022.
Haka kuma sanarwar ta bayyana cewa ‘yan ta’addan na da hannu a jerin garkuwa da mutane ciki har da wasu ma’aikatan hukumar shirya jarabawa ta WAEC a ranar 5 ga watan Yunin shekarar 2023, da wasu malaman coci mata huɗu masu muƙamin rabaran a ranar 21 ga Agustan 2022 da kuma sace wasu ‘yan ƙasar China huɗu a ranar 6 ga Disambar 2023.
Haka kuma rundunar ‘yan sandan ta ce ta gano bindiga ƙirar AK-47 biyar da harsasai 552 da bama-bamai da kayayyakin sadarwa da dama da kuma babura takwas waɗanda ‘yan ta’addan ke amfani da su.