Duk da cewa maharan sun yi ƙoƙarin guduwa amma sojojin sun kama tare da kashe 15 daga cikinsu. / Hoto: ArmeesNiger

Wani harin kwantar ɓauna da ‘yan ta’adda suka kai ya yi sanadin mutuwar sojojin Nijar goma a kusa da iyakar ƙasar da Burkina Faso, kamar yadda gwamnatin sojin ƙasar ta tabbatar.

A wata sanarwa da gwamnatin sojin ƙasar ta karanto a Laraba da dare, ta bayyana cewa an tura jami’ai zuwa yammacin ƙasar a ranar Litinin domin kama ɓarayin shanu a ƙauyen Takzat.

“A lokacin wannan aikin ne wani gungun masu laifi ya yi wa jami’an tsaron kwanton-ɓauna wanda hakan ya kai ga rasa sojojinmu goma,” in ji sanarwar.

Duk da cewa maharan sun yi ƙoƙarin guduwa amma sojojin sun kama tare da kashe 15 daga cikinsu.

Jamhuriyar Nijar tare da makwabtanta Burkina Faso da Mali sun kwashe fiye da shekaru 10 suna gwabza fada da kungiyoyin 'yan ta'adda da suka hada da wasu masu alaka da al-Qa’eda da kuma kungiyar Daesh.

Bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a dukkanin kasashen uku a shekarun baya-bayan nan, mahukuntan kasar sun kori sojojin Faransa tare da karkata zuwa ga rundunonin sojojin haya na kasar Rasha domin neman taimakon tsaro.

Kasashen uku sun sha alwashin karfafa hadin gwiwarsu ta hanyar kafa sabuwar kawancen tsaro, wato kawancen kasashen Sahel ta AES

TRT Afrika