Daga Mazhun Idris
A watan Maris din shekarar 2021, yayin Babban Taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 75 an ayyana shekarar 2023 a matsayin shekarar gero.
A farkon wannan shekarar ne Hukumar Abinci da Aikin Gona (FAO) ta Majalisar Dinkin Duniya ta "bayyana dalilai shida na kawo gero kasuwa”.
Nahiyar Afirka waje na gwajin abubuwa kuma hakan zai iya zama dalili na bakwai wanda watakila hakan zai sa duniya ta karbi wannan abincin mai tarin amfani da ba a kulawa da shi.
Hukumar FAO ta bukaci a bunkasa noman nau'ukan irin gero wadanda ake nomawa a sassan duniya daban-daban a matsayin hatsi ko abincin dabbobi ko kuma matsayin cimakar dan Adam, muhimmin abinci ne da ake samarwa don ci gaban tattalin arziki da kuma kara lafiyar jiki.
Ko an ci shi haka a matsayin hatsi ko kuma an sarrafa ya zama gari, amfanin da yake samarwa ga lafiyar jiki ya wuce na sauran hatsi kamar farar shinkafa.
Dokta Muhammad Baba Bello, wani masani ne kan aikin gona wanda yake da kwarewa a yankin Afirka ta Yamma, ya ce za a iya yaki da matsalar karancin abinci mai gina jiki a Afirka da kuma bunkasa tattalin arzikin iyalai a yankunan karkara.
Dokta Bello, wanda yake aiki da cibiyar kasa da kasa ta aikin gona a kasashe masu zafi wanda ke Nijeriya (International Institute of Tropical Agriculture in Nigeria), ya ce duk da cewa gidaje da dama a yankunan karkara suna cin gero ta hanyoyi daban-daban, amma wasunsu ba su san amfanin da yake bayarwa ga lafiyar jiki ba.
"Za a iya kara inganta sinadaran da ke cikin gero. Amma da farko yana da kyau ka fara da habbaka kasuwanci gero don ya kara daraja kwatankwacin darajar masara da waken soya wadanda ake sarrafa su ta fuskoki da dama a masana'antu," kamar yadda ya bayyana wa TRT Afrika.
Gero a matsayin abinci
Kamar yadda hukumar FAO ta bayyana gero ya kunshi sinadarai kamar foxtail, barnyard da kuma fonio.
Shirin wayar da kan da ake yi ya mayar da hankali ne kan amfanin da ake samu daga gero idan aka dauke shi a matsayin abinci kamar rashin jawo matsala ga muhalli da kara lafiya da samar da sana'a ga mazauna yankunan karkara da samar da abinci da kuma amfani da shi wajen hada magunguna.
Ba kawai cewa gero yana rayuwa a wuraren da wasu nau'ikan hatsi ba sa iya rayuwa ba, kuma yana gyara amfanin kasa da muhalli, a cewar masana.
Bayan cewa gero yana girma ko babu isasshen ruwa kuma rayuwa na'ukan kasa iri-iri, kowane nau'in gero yana samar da sinadarai kamar calcium da manganese da phosphorous da potassium da copper da fiber da sauransu.
Gero a matsayinsa na abinci ba ya kunshe da sinadarin gluten wanda ake samu a sauran hatsi. Galibi na samun gero iri-iri ciki har da dauro da jan gero.
Bayanai daga hukumar FAO ya nuna cewa anbfi noma gero a nahiyar Afirka da Asiya, inda Indiya ce kasar da ta fi nomansa daga nan sai Nijeriya da Nijar da kuma China.
A kasashen yankin Sahel kudu da hamadar Sahara gero abincin gargajiya ne. A kasashen Yammacin Afirka kamar Nijeriya da Nijar ana amfani da gero wajen yin abinci da abubuwan sha iri-iri kamar Tuwo da Biski da Waina da Kunu da Fura da Tumu da sauransu.
Nasiru Baita, wani manomin gero ne a garin Jahun da ke arewa maso yammacin Nijeriya, kuma ya ce yana tuna yadda iyaye suke ba 'ya'yansu gunba wadda ake yi daga gero don ta taimaka musu su girma kuma ta karfafa musu garkuwar jiki. Wasu mutane musamman wadanda suke yankunan karkara har yanzu suna yin hakan.
Ya yi imani da alherin da ake samu daga gero, Nasiru manomi ne da ya mayar da hankalinsa kan babban abin da ya sa a gaba.
"Duk da cewa na noma gero kakar da ta wuce, yanzu na gyara gonata a shirye-shiryen shuka wani abu a bana. Na tanadi tifa cike da takin gida saboda zan bukaci taki bayan kammala shuka," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika.
Kamar sauran manoma a yankin wadanda suke farin cikin shirye-shiryen fara shuka wanda ake saran farawa a karshen watan Mayu ko farkon Yuni, Nasiru ya yi fatan samun damina mai kyau.
"Muna jiran saukar ruwan sama a bana. Geronmu kwana 90 yake yi," in ji shi.
Sabanin a baya, yanzu manoman gero suna samun iri na zamani cikin farashi mai ragusa daga ma'aikatun aikin gona a gwamnatin jiha.
Sai dai yawancin manoma a yankinsu Nasiru suna amfani da iri ne da suke ajiye da bayan kowane girbi.
Akwai bukatar kara bunkasa gero
Kamar yadda Dokta Bello ya ce babbar matsalar noman gero a Afirka shi ne rashin bunkasa irin gero. " Yawancin binciken da ake yi yanzu yana mayar da hankali ne kan samar da nau'ukan iri da yanayin kasar, wanda hakan bai wadatar ba," in ji shi.
Abbas Zubairu, wani karamin manomi ne a arewacin Nijeriya, ya ce babban kalubalen noman gero shi ne tsadar takin zamani.
Hakan yana tilasta wa manoma dogaro a kan takin zamani mai tsada da ake samu a kananan kasuwanni.
A bara, Abbas ya noma buhu 30 na gero, kowane yana da nauyin kilogram 50, amma saboda makudan kudin da ya kashe kan takin zamani ya sa bai ci ribaund ba sosai.
"Na sayi buhu daya na takin zamanin NPK a kan naira 18,000 ($40) saboda ban samu takin da gwamnati ta sayar a rangwayen farashin naira 15,000 ($33). Na kuma sayi takin Urea kan naira 27,000 ($60) a kasuwa, wanda kuma gwamnati ta sayar a kan naira 22,000 ($48)," in ji shi.
A bana farashin gero a kasuwar Jahun ya yi sama wato fiye da naira 25,000 ($55) kan kowane buhu mai nauyin kilogram 50. Haka kuma galibi farashin yake a kasuwannin Gujungu da Kafin-hausa duka a jihar Jigawa.
Dokta Ayuba Ibrahim Adamu, wanda ake wani shiri kan abinci da shi a wata tashar rediyo a arewacin Nijeriya, ya ce akwai bukatar gero ya zama wani abu da kowa zai iya saya saboda muhimmancinsa ga lafiyar jiki.
"Gero yana taimaka wanda ya ci wajen daidaita ciwon siga da hawan jini da adadin cholesterol. Amma ya kamata su kara ilmantar da mutanenmu," in ji shi.
"A jerin abincin gargajiya masu kara lafiya babu wanda ya zo ko kusa da gero ta fuskar amfanin da yake samarwa ga lafiyar jiki da saukin farashinsa. Ina cinsa a kullum hatta a wasu lokuta na musamman," in ji shi.
Dokta Bello ya ce gero yana da muhimmanci ga Afirka ta fuskoki da dama. "Gero ya kasance abinci ga wasu yankuna a Afirka kafin shinkafa da masara su zo mana. A wuraren da masara ta kasa girma, gero yana yin haka da taki kayan."
Baki ya zo daya tsakanin masana inda suke cewa idan aka iya bunkasa noman gero, hakan zai iya taimaka wa wajen maganin matsalar karancin abinci kuma hakan zai samarwa gwamnati da manoma karin kudin shiga, musamman a kasashen Afirka da suke da yanayin da za a iya noman wannan abincin mai tarin amfani.