Hukumomi sun bukaci jama'a da su kasance masu taka tsantsan su daina amfani da wannan nau'in madarar /Hoto: OTHERS

Hukumar da ke sanya ido kan abinci da magunguna a Jamhuriyar Nijar ta bayar da umarnin dakatar da amfani da madarar jarirai ta kamfanin Nestle mai sunan NAN 1 a duk fadin kasar.

Ta ce ta dauki wannan matakin ne bayan gano cewa madarar ba ta cika wasu sharudda ba kuma an shigo da ita kasar ba tare da izini ba.

Hukumar ta bukaci jama'a da su daina amfani da wannan nau'in madarar.

Nau'in madarar na kamfanin Nestle yana da lambobi kamar haka: 21.95.77.6.10 da aka samar a cikin watan bakwai na shekarar 2022, wadda kuma za ta gama aiki a watan hudu na shekarar 2024, in ji daraktar hukumar a wata takarda da ta sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce binciken da aka gudanar kan wannan madarar ya nuna cewa tana kunshe da sinadaran protein da kuma wasu sinadarai da suka wuce kima.

Akwai kuma sinadarai masu maiko da aka hada madarar da su wadanda ba a saka su wadace ba kamar yadda ya dace.

Wannan ya sa hukumar ta ce ya zama tilas a janye wannan madara daga kasuwa.

Kuma hukumar ta bukaci jama'a su sanar da zarar sun ga irin wannan nau'in madara a kasuwa, ko kuma idan sun ji canji a jikinsu bayan amfani da wannan madara, to su yi gaggawar sanar da hukuma.

TRT Afrika da abokan hulda