Hakan Fidan (daga hagu) ya yi taron manema labarai na haɗin gwiwa da mataimakin Firaministan Iraƙi da Ministan Harkokin Wajen Iraƙi Fuad Hussein (daga dama) a Bagadaza. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce babban abin da Turkiyya ke so daga Iraƙi shi ne ta ayyana ƙungiyar ta’addanci ta PKK a matsayin ta ‘yan ta’adda.

Ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara da ya kai birnin Bagadaza.

Fidan wanda ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Iraki Fuad Hussein a ranar Asabar, ya jaddada buƙatar Turkiyya, Iraki, da Syria su haɗa kai don kawar da kungiyoyin ta'addanci na Daesh da na PKK.

Ganawar ta biyo bayan harin da aka kai ranar Juma'a inda 'yan ta'addan PKK suka kashe wasu jami'an tsaron kan iyakar Iraƙi biyu.

A watan Maris din shekarar 2024 ne Iraƙi ta ayyana ƙungiyar ‘yan ta'addar PKK a matsayin haramtacciyar kungiya, matakin da Turkiyya ta yi maraba da shi.

Bayan haka ƙasashen biyu sun rattaɓa hannu kan yarjejeniyoyin yaƙi da ta'addanci da suka haɗa da kafa cibiyoyin haɗin gwiwa a Bagadaza da Bashika.

TRT World