Daga Yusuf Kamadan
Kungiyar 'yan ta'adda ta Fethullah (FETO) a karkashin jagorancin wanda ya kafa kungiyar Fethullah Gulen da ya yi gudun hijira, an daɗe ana lulluɓe ta a matsayin wata kafa mai kyau ta cibiyoyin ilimi da jinƙai.
Duk da haka, hujjoji sun nuna cewa tana aiki ne a matsayin ƙungiyar asiri mai kama da ƙungiyar nan ta Osho ta shekarun 1980.
Kamar Rajneeshpuram, wanda a zahiri ya haɓaka wayewar ruhaniya amma yana aikata laifuka kamar ta'addanci da zamba na kuɗi, FETO ta gina daula mai yaɗuwa, musamman a Amurka.
Ko da bayan mutuwar jagoran Gulen a cikin 2024, ƙungiyar ta ci gaba da aiki a Amurka, tana ci gaba da yin tasiri ta hanyar hanyar sadarwa mai zurfi.
Ƙarƙashin ɓad-da-kama a tsarin samar da makarantu da ƙungiyoyin sa-kai, da ƙungiyoyi masu fafutuka, tana cin gajiyar dukiyar jama'a yayin da take ci gaba da yaɗa ɓoyayyun manufofinta.
Kama da ƙungiyar leƙen ashiri da ta fafutukar Osho
Ayyukan FETO suna nuna abubuwa da yawa na ƙungiyar asiri mai haɗari. An saka wa mambobinta sharadi na kallon Gulen a matsayin shugaba ma'asumi kuma ana sa ran za su bi umarninsa tare da biyayya ba tare da wata shakka ba.
Kamar yadda kungiyar Osho ke aiwatar da tursasawa, ana zargin FETO da yin amfani da sarrafa tunanin mutane da ɓatanci, da kuma saka munanan aƙidu domin ci gaba da samun iko a kan mambobinta.
Babban makasudin shi ne kutsawa cikin cibiyoyin gwamnati da kuma ƙarfafa ikon siyasa - wani buri da ya bayyana a fili a yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya a shekarar 2016.
Ayyukan da kungiyar ke nunawa tana yi a matsayin mai tallafa wa ilimi ya yi kama da dabarun hulda da jama'a na kungiyar Osho.
Duk da haka, kamar yadda a ƙarshe asirin Rajneeshpuram ya tonu saboda munanan ayyukansa, ɓoyayyun manufofinFETO na zamba da cin hanci da rashawa sun fito fili.
Bude makarantu don ɓoye aikinta na cin hanci
Daya daga cikin fitattun ayyukan FETO a Amurka shi ne yadda take gudanar da makarantu sama da 150, wanda hakan ya sa ta zama cibiyar sadarwa mafi girma mai makarantun bogi a kasar.
Kamar yadda hukumar leken asirin Turkiyya ta gano, wadannan makarantu wadanda galibi aka kafa su da sunaye na yaudara domin a ɓoye alakarsu da Gulen, sun shiga rigingimu da suka hada da almubazzaranci da kudade da nuna son kai, da cin dukiyar jama'a.
Wata sananniyar dabarar da FETO ke amfani da ita ta haɗa da cin gajiyar shirin biza na H-1B.
Daruruwan mambobin kungiyar ta'addanci, wadanda yawancinsu ba su da cancanta, an shigo da su Amurka don cike ayyukan koyarwa da gudanarwa a wadannan makarantu.
An ba da rahoton cewa ana buƙatar waɗannan ma'aikatan su ba da gudunmawar wani yanki na albashinsu ga FETO, tare da shigar da kuɗin masu biyan haraji yadda ya kamata a cikin hanyar sadarwar ƙungiyar ta duniya.
Bugu da ƙari kuma, makarantun da ke da alaka da FETO na da hannu wajen yin magudin zabe da bayar da ƙarin kwangila ga kamfanonin da ke da alaka da FETO, tare da karkatar da miliyoyin dalolin da aka tanada na ilimi cikin ayyukansu na ɓoye.
A cikin wani rahoto na 2019, Forbes ta ba da haske game da waɗannan kura-kuran kuɗi waɗanda ke bayyana yunƙurin shigar da kuɗin masu biyan haraji cikin babbar hanyar sadarwar ƙungiyar.
Waɗannan binciken, sun yi daidai da irin wannan tsarin da aka gani a ƙungiyar Osho, inda aka ba da fifikon ribar kuɗi a kan manufa ta ruhaniya ko ilimi.
Yin amfani da tsarin ilimi don ɓad-da-kama
Makarantun FETO sun fi mayar da hankali ga al'ummomin da ba a kula da su sosai, suna gabatar da kansu a matsayin cibiyoyi masu ba da ingantaccen ilimin Kimiyya da Fasaha STEM da shirye-shiryen shiga kwaleji.
Wannan yana ba su damar samun kuɗin jama'a da kuma samun amincewa tsakanin iyaye da jami'an ƙasa.
Sai dai bincike da masu fallasa bayanai sun nuna cewa wadannan makarantu galibi suna aiki ne a matsayin cibiyoyin daukar ma'aikata na 'yan ta'addar FETO.
Ana koyar da ɗalibai a hankali ta hanyar shirye-shiryen al'adu da ayyukan karin karatu. Wadannan tsare-tsare, wadanda aka tallata a matsayin damarmaki na wadata, galibi suna zama hanyoyin yaɗa ra'ayi da aƙaidar FETO a duniya da ƙarfafa tasirinta.
Barazana ga tsaron ƙasar Amurka?
Ayyukan FETO sun zarce fannin ilimi. Ta hanyar sadarwa na cibiyoyin bincike da ƙungiyoyin sa-kai, da roƙo, ƙungiyar tana yunƙuri don neman tsara manufofin Amurka da jan ra'ayin jama'a don samun tagomashi.
Sau da yawa tana nuna kanta a matsayin wadda aka zalinta a siyasance a Turkiyya, tare da kawar da hankalin mutane daga haramtattun ayyukanta da kuma samun goyon baya a tsakanin 'yan siyasa da masana na Amurka.
Wannan kutsawa cikin tsarin Amurka yana haifar da babban haɗarin tsaron ƙasa.
Ta hanyar cin zarafin tsarin shari'a da kudi na kasar, FETO na ɓata amincewar da ake da ita a kan cibiyoyin gwamnati yayin da take samar wa kanta kudade masu yawa.
Tarihi na tasirin kungiyar a Turkiya ya zama babban gargadi kan hadarin da zai iya haifarwa idan ba a magance shi ba a Amurka.
FETO na adawa da Trump a fili
Shigar FETO a siyasar Amurka ya kai ga yakin da ake yi da mutanen da ta dauka a matsayin cikas ga manufofinta.
Shugaba Donald Trump dai na ci gaba da sukar kungiyar ta FETO, inda fitattun mambobinta ke amfani da kafafen sada zumunta da kafafen yada labarai wajen bata masa suna.
Misali, a cikin watan Agustan 2024, Ergun Babahan, mamba na FETO ya rubuta cewa, "Trump ya haukace kuma yana iya faɗuwa a zaben."
An tattara jerin rubutun rashin kunyar da Babahan ya yi wa Trump, ciki har da sakon da ya rubuta a shekarar 2023 yana mai cewa, “Alkalai masu ra’ayin riƙau da Trump ya nada suna kashe Amurka,” da kuma wani sakon twitter na shekarar 2020 wanda ya yi Allah wadai da yunkurin Trump na yin tasiri kan kirga kuri’u, yana mai cewa abin kunya ne a tarihin dimokradiyya.
Kuzzat Altay, wani fitaccen dan ta'addar FETO, ya bayyana cewa, "Trump ne shugaban kama-karya da aka taba yi," yayin da Nedim Hazar ya yi shelar cewa, "Tare da Trump, tasirin farkisanci a duniya zai kai kololuwa!"
Bugu da ƙari, saƙon Said Sefa ya ma fi kaushi. Ya bayyana Trump a matsayin "wawa, daƙiƙi, marar kan-gado" ya kuma bayyana shugabancinsa a matsayin "abin karfafa wa jahilai da masu ra'ayin riƙau gwiwa.
Sevgi Akarcesme ya yi na'am da irin wannan ra'ayi, yana mai kiran Trump da "mai son kai wanda ke ci gaba da zagon kasa ga dimokiradiyya ta hanyar siyasa".
Akarcesme ya kuma kara kambama labaran ƙyamar Trump ta hanyar sake buga wasu kalamai masu yawa na sukar shugabancinsa.
Marubucin da ke da alaka da FETO, Ugur Tezcan ya rubuta a wata makala cewa, "Dukkan shugabannin masu mulkin kama-karya da magoya bayansu, na hannun dama, da masu fasikanci a duniya suna dakon sabon shugabancin Trump."
A halin da ake ciki, Adem Yavuz Arslan ya ci gaba da sukar Trump a cikin wallafe-wallafe da shirye-shiryensa, yana mai kara nuna adawar da FETO ke yi wa shugaban na Amurka.
Taka tsantsan na da muhimmanci
Kasancewar FETO a Amurka misali ne ƙarara na yadda kungiyoyin asiri masu fakewa da addini za su yi amfani da tsarin dimokuradiyya don cim ma burinsu.
Duk da yake a zahiri yana haɓaka ilimi da tattaunawa tsakanin addinai, tarihin da aka rubuta na cin hanci da rashawa da magudi, da kuma zagon ƙasa yana ba da wani labari daban.
Domin kare dukiyar jama'a da tsaron kasa, tilas ne hukumomin Amurka su sanya ido sosai kan ayyukan kungiyar ta FETO tare da ɗorawa kungiyar alhakin munanan ayyukanta.
Ta hanyar fahimtar kamanceceniya da sauran ƙungiyoyin asiri da kuma daidaitattun kalaman adawa da Trump, masu tsara manufofin za su iya fahimtar ainihin manufar FETO tare da ɗaukar matakan da suka dace don hana ci gaba da cin zarafin.
Matakin na FETO ya kasance gargadi ne kan hatsarin ikon da ba a kula da shi ba, yana mai jaddada muhimmancin yin taka tsantsan wajen kare martabar dimokradiyya.