Bello Turji ya tsere ya bar ɗansa da sauran mayaƙansa, in ji hedkwatar tsaron Nijeriya./Hoto:Hedkwatar Tsaron Nijeriya

Sojojin Nijeriya sun tabbatar da kashe wasu makusantan Bello Turji ɗaya daga cikin ɓarayin dajin da suka addabi arewa maso yammacin Nijeriya.

Wata sanarwar da daraktan watsa labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba, ya fitar ta ce samamen da sojin ƙasar suka kai Shinkafi da Kagara da Fakai da Moriki da Maiwa da kuma Chindo sun yi sanadiyyar kashe gomman ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji da aka kashe a Fakai.

“Ƙarfin wutar da sojojin suka buɗe ya janyo mutuwar ‘yan ta’adda da yawa tare da lalata cibiyar adana kayayyakinsu. Harin ya kuma yi sanadiyyar ‘yanta wasu mutane da Bello Turji ya yi garkuwa da su. Kuma shugaban ‘yan ta’addan, Bello Turji, ya tsere ya bar ɗansa da sauran mayaƙansa,” in ji sanarwar.

Bello Turji yana cikin ɓarayin daji da suka yi ƙaurin-suna wajen garkuwa da mutane da kisa a arewa maso yammacin Nijeriya.

Sai dai a ƙarshen shekarar da ta gabata dai hedikwatar tsaron Nijeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta kashe Bello Turji.

Kuma a ƙarshen makon jiya ne rahotanni suka ce ɗan ta’addan yana tsere wa harin sojojin Nijeriya.

Kazalika sojin ƙasar sun lalata dabar wani ɗan ta’adda da ake kira Idi Malam a kan hanyar dajin Zango Kagara, in ji sanarwar.

“A lokacin arangamar, dakarun sun kashe ‘yan ta’adda uku tare da kama mutum uku da ake zargi da haɗa baki da su,” in ji Janar Buba.

Baya ga haka sanarwa ta ce dakarun Nijeriyar sun kwace bindigogi iri-iri da kuma harsasai da alburusai da kuma shanu 61 da tumaki 44 da aka sace.

TRT Afrika