Tanzania ta jaddada kudurin inganta tashar jirgin ruwan Dar es Salaam. Hoto: Tanzania Port Authority

Daga Peter Nyanje

Akwai wata zazzafar muhawara da ake ta yi a Tanzaniya bayan da gwamnati ta sanar da cewa ta cimma yarjejeniya "ta baki da baki" da Dubai, don bai wa kamfanin aika kaya ta tashar jiragen ruwa na Dubai, DP World damar tafiyar da wasu ayyukan tashar jiragen ruwa ta Dar es Salaam.

Muhawarar ta fara ne bayan da bayanai suka bayyana kan yarjejeniya tsakanin Tanzania da Dubai inda wasu 'yan Tanzania ke cewa babu bukatar gwamnati ta bar lamarin tafiyar da tashar jiragen ruwanta a hannun wanda ba dan kasa ba.

Bayan da gwamnati ta sanar da cewa a yanzu ba ta da abubuwan da ake bukata wajen tafiyar da tashar yadda ya kamata, wasu sun yarda cewa bai wa kamfani mai zaman kansa damar ci gaba da kula da tashar abu ne mai kyau, amma da kamfanin cikin gida aka bai wa, maimakon na kasar waje irin su DP World.

Yayin da ake ci gaba da muhawarar, a bayyane yake cewa mika ragamar tashar jiragen ruwa ta Dar es Salaam ga kamfani mai zaman kansa abu ne da ba za a iya hanawa ba ganin yanayin da ake ciki yanzu.

An shafe gomman shekaru kula da tashar jiragen ruwa ta Dar es Salaam na karkashin Kamfanin Tanzania International Container Terminal Services (TICTS) har zuwa lokacin da kwantiragin ya kawo karshe a farkon shekarar nan, kuma gwamnati ta nuna ba ta da niyyar tsawaita ta.

A farko dai, gwamnatin Tanzania ta sanar da cewa tana burin gudanar da tashar da kanta, ta hannun kamfaninta na Tanzania Ports Authority (TPA).

Tattaunawa da kamfanin DP World, ya janyo hankalin wasu kasashen gabashin Afirka da na kudanci, wadanda suka dogara kan tashar gabar ruwa ta Dar es Salaam.

Wasu kasashe a yankin wadanda suke da tashoshin jirgin ruwa suna kallon tashar Dar es Salaam a matsayin mai gasa da su.

Dar es Salaam daya daga cikin manyan biranen kasuwanci ne a gabashin Afirka . Hoto: Getty 

Inganta hada-hada a tashar jirgin ruwan Dar es Salaam zai haifar da tasiri mai yawa, ba wai ga Tanzania kawai ba, har da mambobin kungiyoyin hadin kan tattalin arziki na gabashin Afirka, wato EAC, da kuma na yammacin Afirka, wato SADC.

Zuba jari da inganta ayyuka da kamfanin TICTS ya aiwatar a Dar es Salaam sun janyo habakar ayyuka, amma bai kai matakin karfafa gogayya da sauran tashoshi ba a yankin.

Sakamakon haka, a shekarun baya-bayan nan tashar tana rasa kwastomomi wadanda suke zabar tashar Mombasa a Kenya da tashar Durban a Afirka ta Kudu, wadanda suke cigaba da inganta ayyukansu.

A wani shiri na kwanan nan don inganta tashar Dar es Salaam, wanda aka sanya wa suna Shirin Dar es Salaam Maritime Gateway Project (DMGP), wanda ya kunshi kara zurfin gabar saukar jirage ta 1 zuwa ta 7, da gina sabbin gabar saukar jirgi don sauke motoci, da kuma fadada hanyoyin shigowa tashar.

Sai dai, Ministan Ayyuka da Sufuri na Tanzania, Farfesa Makame Mbarawa ya fada wa majalisar kasar cewa duk da matakan inganta ta, ayyuka a tashar ba su kai cigaban na kasashen duniya ba.

Ga misali, lokacin dakon jirgi yakan kai kwana biyar, inda a tashar Mombasa da Durban ba ya kai wa kwana biyu.

Duk kwana daya da jirgin ruwa yake a tasha yana biyan dala 25,000, sannan idan jirgi ya kwashe kwana biyar kafin saukewa da loda kaya, duk da cewa a kyakkyawan tsarin duniya kwana daya ne.

Wannan ya tilasta wa da yawan kamfanonin safarar jiragen ruwa sun kaurace wa tashar Dar es Salaam, wanda hakan ke janyo asara ga tattalin arzikin Tanzania.

Tashar Dar es Salaam tana da damar samar da kudaden shiga ga gwamnati. Hoto: Tanzania Port Authority

Wannan matsala ta haifar da tashin farashin kudin shigo da kaya, inda shigo da kaya zuwa Congo DRC ta tashar Dar es Salaam yake kai wa tsakanin dala 8,500 da dala 12,000, wanda ya haura farashin sauran tashoshi a yankin matuka.

A wani rahoto da Bankin Duniya ya wallafa a 2013 ya nuna cewa a 2012, asarar da aka samu ta dalilin rashin ingancin ayyuka a tashar Dar es Salaam ya kai kiyasin dala biliyan 1.8 ga tattalin arzikin Tanzania, da dala miliyan 830 ga tattalin arzikin kasashe makwabta da suke dogara da tashar.

A cewar Bankin Duniya, asarar ta kai kashi 7% a ma'aunin GDP. 'Yan Tanzania da 'yan gabashin Afirka suna biyan karin kudade kan kayayyakin da aka shigo da su, wanda suka hada da mai, da siminti da takin zamani, sakamakon karin farashin shigo da kaya ta tashar.

Tsawaitar lokacin jira a tashar Dar es Salaam shi ne babban dalilin. A tsakiyar shekarar 2012, jirage sukan yi jiran har kwana 10 kafin su shiga tashar, da karin kwana 10 kafin su fara sauke kaya.

Tashar Dar es Salaam tana samar da mashiga ga kashi 90% na kasuwanci a Tanzania, kuma ita ce hanyar shigo da kaya ga kasashe shida marasa gabar teku, wadanda suka hada da Malawi, Zambia, Burundi, Rwanda, Uganda, da Congo DRC.

Wani zabin

Dalilin wannan, wasu kasashen kungiyar SADC suna iya bin ra'ayin cewa matakin Tanzania na shiga yarjejeniya da kamfanin DP World ya zo a daidai, saboda su ma za su amfana.

Kamfanin DP World ya shahara wajen gudanar da tashar jirgi a fadin duniya. Hoto: AP

Rashin ingancin aiki a tashar Dar es Salaam yawanci sakamakon babu kayayyakin aiki na zamani ne don gudanar da tashar.

Tanzania ta ce ta zabi kamfanin DP World ne don ya gudanar da tashar saboda tsarin kamfanin na yin aiki gaba da baya, wanda ke nufin baya ga kwarewar gudanar da tasha, yana kuma hada-hadar kaya daga inda aka siyo zuwa inda za a kai.

A yanzu DP World yana aiki a tashoshi shida a Afirka da kuma sama da tashoshi 30 a fadin duniya.

Har yanzu tashar Durban ta Afirka ta Kudu ita ce babbar tashar jirgin ruwa wajen yawan hada-hada a Afirka.

Tana gudanar da kusan kashi 60% na kasuwanci a Afirka ta Kudu, kuma tana yi wa babban kaso na yankin tsibirin Afrika ta Kudu aiki

Amma Durban, da kuma sauran tashoshin kasar Afirka ta Kudu da na kasashe makota, kamar Mozambique, da Namibia da Angola su ma sun gaza, bayan daukar shekaru ba a inganta su.

Tashar Dar es Salaam za ta iya zamowa sabon zabi matukar an inganta ta.

A baya-bayan nan, Amurka ta sanar da shirin zuba dala miliyan 250 don farfado da babban titin jirgin kasa da ya hada kasar Congo DRC da Angola, don inganta sufuri.

Safara a fadin nahiya

Karkashin wannan shiri, za a gina layin dogo da zai hada tashar jirgin ruwan Lobito ta Angola, wadda take bakin gabar Tekun Atlantic, zuwa birnin Dar es Salaam, ta cikin birnin Kapiri Mposhi na Zambia.

Tashar jirgin ruwan Dar es Salaam a yanzu ta yi kaurin suna da rashin saurin aiki. Hoto: Tanzania Port Authority

Wannan shiri zai haifar da mahada tsakanin tekun Atlantic Ocean da na Indian Ocean.

Inganta ayyuka a tashar Dar es Salaam yana da muhimmanci don safarar kaya gaba.

Tanzania ta ce kudaden shigarta na hukumar shige da fice, ta tashar Dar es Salaam za su tashi daga kudin Shiling din Tanzania daga triliyan 7.76 (dala biliyan $3.25), zuwa tiriliyan 26.7 (dala $11.13) a 2032/2033.

Wannan adadi ya kai sama da rabin kasafin kudin Tanzania na shekara.

Ana sa ran ayyuka su kara sauri, kuma farashi ya sauka ga kasashe makota, da kuma farashin sufurin kaya tsakanin kasashen Afirka, da sauran yankunan duniya har ma da Turai da Asiya.

Saboda haka, kasantuwar tashoshin jirgin ruwa masu nagartar aiki a gabashi da kudancin Afirka, kamar tashar Dar es Salaam, yana da matukar alfanu ga hada-hadar tattalin arziki.

Marubucin, Peter Nyanje, mai sharhi ne kan siyasa da tattalin arziki, wanda ke zaune a Dar es Salaam, Tanzania.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana a nan ba sa wakiltar ra'ayi, ko mahanga, ko tsarin hukumar TRT Afrika ba.

TRT Afrika