Bukatun al'ummar Kiristoci a Gaza, Yammacin Kogin Jordan, da kuma na baya-bayan nan Lebanon, ya zama babban batu na gaggawa a lokacin da ake gwabza babban yaki a Gabas ta Tsakiya.
A yayin da Isra'ila ke ci gaba da aikata kisan kiyashi da aiwatar da manufofin mamaya, Larabawa Kiristoci na fuskantar zalunci, matsin tattalin arziki, da raba su da matsugunansu.
Tare da rikicin jin kai da rikicin ya kawo, ana smaun ruguza cibiyoyin addini da raya al'adu na jama'a.
A kudancin Lebanon, dakarun isra'ila sun lalata wata coci a kauyen Deir Mimas na Kiristoci, a inda hare-haren bam ta sama ya rugurguza cocin Evangelical mafi tsufa a SIriya da Lebanon.
Wadannan ayyuka wani bangare ne na Firaminista Benjamin Netanyahu da yake amfani da su wajen kai wa Kiristoci hari, jama'a marasa rinjaye da ke da tsohon tarihi a yankin.
Bethlehem, nan ne aka tabbatar a matsayin wajen da aka haifi Annabi Isan Alaihissalam kuma wajen alama ce babba ta tarihin Kiristanci, waje na bayar da misali.
Falasdinawa Kiristoci da ke garin suna shan wahala daga matsalolin tattalin arziki da zamantakewa saboda kawancen da Isra'ila ta yi wa yankin.
A 2024, gwamnatin isra'ila ta kara yawan haraji kan coci-coci da cibiyoyin Kiristoci da ke birnin Kudus da sauran garuruwan Falasdinawa.
Wadannan haraji, da suka saba wa dokokin kasa da kasa, sun kara ta'azzara gwagwarmayar tattalin arziki da Kiristoci ke yi, anda ke tirsasa da dama barin gidajensu na gado.
A yayin da hakan ke faruwa, Yahudawan Isra'ila 'yan kama guri zauna na kwace yankunan Falasdinawa Kiristoci a Yammacin Gabar Kogin Jordan, suna raba iyalai da dama da gidajensu.
Wannan ya kara munana saboda rashin tallafin kasa da kasa, an bar Kiristoci Falasdinawa su ji da kawunansu don magance raba su da gidaje da wargaza su.
Shirin Netanyahu kan zamantakewa
Manufofin Netanyahu sun sanya damuwa game da nuna wariya da gan-gan .
Wani shirin samar da matsugunai na 2024 da Ministan Kudi Bezalel Smotrich ya kaddamar na da manufar alakanta yankunan Isra'ila da ba sa bisa ka'ida da ke Gush Etzion da Kudus, ana cinye kasar Falasdinawa, ciki har da 'yan kauyukan Kiristoci da suka rage a Yammacin Gabar Kogin Jordan.
A Lebanon, inda Kiristoci ba su kai rabin jama'ar kasar ba, ayyukan sojojin Isra'ila sun illata mafi yawan yankunan Kiristoci a hare-haren da suke kai wa na shekara guda, musamman yadda aka tsananta hakan a watanni biyun da suka gabata har zuwa makon nan d aaka tsagaita wuta.
Gabashin Beirut da gabar arewacin Tsaunin Lebanon sun fuskanci matsanantan hare-hare da rusau sakamakon bama-baman Isra'ila. Coci-coci, muhimman wuraren raya al'adu da ibada duk sun lalace.
Kuma wadannan hare-hare ba su da alaka da kai wa mayaka hari irin su Hezbollah saboda yankuna ne da fararen hula ke zama a cikin su.
Kiristocin Labanan da dama, ciki har da manyan 'yan siyasa irin su Samir Geagea na jam'iyyar LFP, sun soki ayyukan Hezbollah.
Wannan ya kawo cikas ga ikirarin da ake yi na cewa wajibi ne a kai hare-haren don tsaron kasar isra'ila, ba wai hare-hare da gan-gan kan Larabawa Kiristoci ba.
Zaluncin cikin gida a Isra'ila
Kalubalen da Larabawa Kiristoci ke fuskanta na shafar wadanda ke rayuw a iyakokin Isra'ila. Rahoton 2024 da wata Cibiyar Bincike a Kudus ta bayyana ya nuna ana samun cin zarafi da lalata dukiyoyin Kiristoci 'yan Isra'ila, mafi yawancin su Larabawa.
An samu Yahudawa masu tsaurin ra'ayi da laifin zalunta da rikici kan Kiristoci, ciki har da lalata wuraren bauta.
Gwamnatin Isra'ila ta nuna rashin damuwa don magance wadannan matsaloli. Gwamnatin netanyahu ba ta dauki wani mataki kan masu aikata laifukan ba, wanda ke nufin ta aminta da su kenan ta bayan fage.
Nuna halin rashin damuwa na nufin akwai wani shiri na Yahudawa masu rajin kafa kasar Isra'ila da ke nuna wariya ba ga Musulmai kawai ba, har ma da Kiristoci.
Shirin nufar Larabawa Kiristoci wani bangare ne na babban shirin tabbatar da karfin iko da fifikon Yahudawa a yankin ta hanyar kakkabe wadanda ba Yahudawa ba da raba su da matsugunansu.
A wajen kasashen duniya, wannan na gabatar da wajabcin tuhumar Isra'ila kan ayyukan da take yi.
Ware ta a yyukan diplomasiyya, takunkumin tattalin arziki da daina ba ta makamai da tallafin soji sun zama waibi don kawo karshen wannan zalunci da kuma tabbatar da adalci.
Abin takaici, martani da matakin da kasashen duniya ke dauka ba ya isa. Bukatun Kiristoci Larabawa da ke Gaza, Yammacin Kogin Jordan, da Lebanon na cikin yanayin taimakon gaggawa.
Wadannan jama'a ba ciwukan yaki kawai suke da shi ba, sun zama mutanen da manufofin da aka tsara ke kakkabe su daga ban kasa.
Tsawon karni da dama, Larabawa Kiristoci sun ksance wani bangare na al'adu, addini da zamantakewar Gabas ta Tsakiya.
Kare wadannan al'ummu ba batu ne adalci kawai ba, shaida ce ta dimbin tarihin da yankin ke da shi.
Tambayar ita ce ko kasashen duniya za su tashi tsaye su fuskanci wannan kalubale ko kuma su ci gaba da zama a makance ba sa kallon wahalar da Kiristocin na Gabas ta Tsakiya ke ciki.
Marubuci: Hamzah Rifaat ya yi digirin farko a fannin nazarin Zaman Lafiya da Rikici a Islamabad, Pakistan, da kuma nazarin Pakistan da Duniyar Diflomasiyya, daga Cibiyar Diplomasiyya ta Bandaranaike da ke Colombo, Sri Lanka. Hamza kuma babban mamba ne a Cibiyar Stimpson da ke Washington a 2016.
Togajiya: Ra'ayoyin da marubucin ba sa wakiltar ra'ayoyin editocin TRT Afrika ba.