Mutanen kasar Philippines suna zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin Quezon na kasar Philippines. Hoto: Reuters      

Daga Dr. Sami A Al-Arian

Za a cigaba tunawa da ranar 7 ga Oktoban 2023 a tarihi, a matsayin lokaci mai muhimmanci a gwargwarnayar Falasdinawa na tabbatar da adalci da kwatar 'yancinsu.

Tun bayan yarjejeniyar birnin Oslo ta shekarar 1993, gwamnatocin Isra’ila da suka biyo baya suke watsi da asalin batun da yarjejeniyar ta kunsa kamar da kasar Falasdinu mai cikakkiyar 'yanci.

Haka kuma shugabannin na Isra'ila sun ɗora a yunkurin mayar da yankin na Yahudawa ne ta hanyar sanya sojoji a wuraren da ta mamaye, tare da yunkurin zagaye Gaza da sojoji, inda a sanadiyar hakan suka tauye wa Falasdinawa hakkinsu na 'yan Adam da mulki.

Daga cikin salon Isra'ila akwai kafa kananan garuruwan Yahudawa kadai, da amfani da shingen sojoji da sanya katange garuruwan Falasdinawa da cigaba da mayar da birnin Jerusalem na Yahudawa kadai tare da hana Musulmai da Kirista damar ibada, da kuma yin amfani da kisan gilla da kamawa da tsarewa a matsayin hanyoyin da za su dakatar da fafutukar da Falasdinawa ƙwatar garuruwansu da aka ƙwace.

Tun farkon mulkin Firaiminista Benjamin Natanyahu da kuma karin goyon bayan da yake samu a bayyane daga masu mulkin kama-karya irin nasa, sai hare-haren da suke kai wa Falasdinawa ya ƙara ƙaimi.

Misali, a shekarar 2023-kafin wannan rikice-rikicen na kwanan nan- an kashe sama da Falasdinawa 250 a yankin Yammacin Kogin Jordan, ciki har da kananan yara 40.

Bayan haka kuma, fadawa Masallacin Kudus da sojojin Isra'ila suke yi da garuruwan baƙi ya zama ruwan dare a kokarin Isra'ilawa na nuna wa Musulmai cewa Masallacin, wurin ibadar Yahudawa ne ba nasu ba.

A lokacin da yiwuwar samun maslaha a game da Falasdinawa a siyasance a gomman shekaru da suka gabata ke neman zama abu mai wuya, ita gwamnatin Isra'ila ta yanzu yunƙuri take ta karasa rikicin cikin gaggawa ta hanyar assasa wasu sababbin ƙulle-ƙullen.

Ta hanyar gina sababbin garuruwa da ƙwace na Falasdinawa da mayar hukumomin Falasdinu mayar da hankali wajen kare kanta, da rage karfin gwargwamaryarsu, hakan ya jefa rayuwar Falasdinawa a yankin Gaza cikin kunci, sannan kuma ya fara nesanta burin Falasdinawa na kwatar 'yancinsu.

Fafutikar da Falasdinawa ke yi a karkashin jagorancin kungiyar Hamas a Gaza ta nuna wa Isra'ila cewa akwai sauran aiki a gabansu musamman ma abubuwan da suka wakana a birnin Jerusalem a 'yan makonnin nan.

Duba da haka, bayan kashedin da suka dauki kusan shekara suna yi, Rundunar Al-Qassam, wato sashen soji na Hamas sai ta kaddamar da hare-hare da ta sanya wa suna "Operation Al-Aqsa Flood".

Hare-haren na ba-zata a Isra'ila sun shafi barikin sojoji, garuruwan bakin boda da kuma wasu wurare masu muhimmanci na kasar irin su filin jirgin sama da kutse a intanet.

Daga cikin makasudin wadannan hare-haren, wadanda aka yi domin mayar da martani ga cin kashin da Isra'ila ke yi, akwai:

(a) Dakatar da yunkusin shiga da kwace Masallacin Kudus da keta alfarmarsa.

(b) Kawo karshen farmakin yankin West Bank na Gaza da garuruwa irin su Jenin da Nablus da Tulkarm da Huwara da Al-Khalil inda aka sace aka kuma kashe daruruwan Falasdinawa.

(c) Kama mayakan Isra'ila da dama domin yin amfani da su wajen musayar fursuninin yaki bayan Isra'ila ta ki amincewa ta saki Falasdinawa kusan 5,500 da suke zaune a gidajen yarin kasar ana gana musu azaba.

(d) Fitar da Gaza daga kewaye ta da Isra’ila ta yi, wadda ta jefa sama da mutum miliyan biyu cikin kuncin rayuwa tsawon shekara 16 da suka gabata; wadda watakila ita ce babbar manufar.

(e) Nuna wa duniya cewa fafutika da shirin Falasdinawa na kwatar 'yancinsu duk kuwa da kokarin da ake yi na danne su.

Hare-haren na ba-zata na Hamas da sauran kungiyoyin fafutikar ya matukar girgiza Isra'ila. Tun da aka kafa kasar a shekarar 1948, ba a taba daga mata hankali kamar wannan lokacin ba.

Sojoji da sauran jami'an tsaron Isra'ila sun yi mamakin yadda mutane 'yan daruruwa suka shirya tare da aiwatar da hare-haren a dan kankanin lokaci, wanda ya daga musu hankali tare da karfafa gwiwar kungiyoyin masu fafutikar.

Gazawar hukomomin leken asirin Isra'ila da sojojinsu ya sa masana suke bayyana nasarar hare-haren a matsayin daya daga cikin manyan gazawar kasar, har suke tunanin ya fi muni a kan gazawarta a karawarta da Masar da Syria na shekarar 1973.

Sai dai a wancan rikicin, ta gwabza ne da kasashen Larabawa biyu manya masu dubban sojoji, amma a wannan lokacin, da wasu 'yan daruruwan sojoji ne kawai.

Bayan haka, kasashen Yamma, ciki har da Amurka sun nuna goyon bayansu ga Isra'ila da nuna baki biyu ga Falasdinawa da fafutikarsu.

Shugaban kasar Amurka Joe Biden da sauran jami'an gwamnatinsa sun bayyana goyon bayansu a bayyane ga Isra'ila, tare da yin watsi asalin batun da ya haifar da rikicin domin karfafa gwiwar Isra'ila.

Gwamnatin Amurka ta kuduri aniyar goyon bayan tsare-tsaren Isra'ila na kisar gilla ta hanyar taimaka mata da makamai na biliyoyin Daloli domin taimaka mata wajen danne Falasdinawa da fafutikarsu.

Babban manufar Amurka da kawayenta ta taimakon Isra'ila ita ce dusashe nasarar da masu fafutikar suka samu wadda ta kunyata babbar abokiyarsu.

Ta hanyar yin amfani da yarjejeniyar Abraham ta 2020, Amurka ta dage wajen ganin ta jagoranci wata hadaka tsakanin Saudiyya da Isra'ila wadda zai sa ta kulle ido daga batun Falasdinu.

Sai dai yarjejeniyar ta shiga tsilla-tsilla bayan wadannan hare-haren na cin kashi da ke wakana a Gaza ya bata komai, wanda hakan ya sa kafin a murmure a cigaba da batun yarjejeniyar, zaben Amurka na 2024 ya karato.

Amma duk da haka, gwamnatin Isra'ila ta ce ba za ta gajiya ba har sai karar da kungiyoyin fafutikar a ban kasa, sannan ta kwato gomman sojojinta da suke tsare, ko kuma ta sake yin wani sabon mamayar a Gaza ta kore Hamas da shugabanninta.

Ta kuma fara yunkurin neman sojojin sa kai guda 360,000. Amma ana ganin yunkurin akwai matsaloli da dama, ba wai na rasa sojoji kadai ba, har da yiwuwar fadada yakin domin hakan zai sa Hezbollah daga Yemen da ma Iraƙi da ma wasu kungiyoyin yankin su shigo a yakin.

A cewar jami'an gwamnatin Amurka, wannan shi ne dalilin da ya sa Amurka ta tura jirajen yakinta na sama da na ruwa da sauran kayan yaki zuwa yankin.

Haka kuma gwamnatin Amurka din ta yi gargadin cewa kada kowace kasa daga yankin ta taimaki Falasdinawa a yakin, domin ba Isra'ila damar aiwatar da mummunar manufarta.

A daidai lokacin da Isra'ila da kawayenta na Yamma suke kokarin batar da masu fafutikar Falasdinawa da goge nasarar da suke samu, kasashen yankin irin su Turkiyya da Iran da Qatar da Masar suna ta kokarin yi wa tufkar hanci.

Amma dai ko ma me ya faru, a bayyane yake cewa masu fafutikar Falasdinawa suna da abin da za su yi alfahari da shi.

Duk da kasancewarsu a gidajen yarin da sansanonin tsarewa, amma duk da haka Falasdinawan Gaza suka shirya tserewa daga gidan yari, inda suka samu nasarar tserewa, suka kuma kunyata masu tsare su, sannan suka nuna wa duniya cewa goguwar fafutikar kwatar 'yancinsu ba za ta taba lafawa ba.

Marubucin, Dr Samu A. Al-Irian, Darakta ne a Cibiyar MusUlunci da Al'amuran Duniya da ke Jami'ar Istanbul Zaim.

Togaciya: Ra'ayin marubucin ba dole ba ne ya zama ya yi daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na kafar TRT Afrika.

TRT Afrika