Bin diddigi da danniya: Wahalar da Falasdinawa ke sha a Ingila

Bin diddigi da danniya: Wahalar da Falasdinawa ke sha a Ingila

Mu da muke zaune a kasashen waje suna kira da cikin gaggawa a tsagaita wuta a rikicin Gaza.
Hadil da mahaifinta na daga cikin Falasdinawa d ake fuskantar bin diddigi a Ingila Hoto: Hadil

Daga Hadil Louz

Yawan tsoron ɓata matsala ce da ba a iya jurewa. Tun bayan 7 ga Oktoba, rayuwata, tare da ta iyalina a Gaza ta birkice, kuma babu alamun za a tsagaita wuta a rikicin.

Dukkan iyalina na kusa da na nesa na rayuwa a Gaza, mafi yawan su ma na zaune ne a sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia da ke arewacin Zirin Gaza.

An tirsasa musu guduwa zuwa Kudancin Zirin Gaza bayan da Isra'ila ta bayar da sanarwar lallai su bar yankin. Sai dai kuma, babu wani waje a Gaza da yake da aminci.

Tsawon shekaru biyar kenan da na bar gida nake gudun hijira, ina karatun digiri na biyu kuma ina shirin fara digirgir. Sakamakon hanin tafiya da takunkuman da aka sanya wa Gaza tun 2007, ban samu damar ziyartar Gaza ba tun bayan zuwa na Ingila a 2018.

A yayin zama na a Ingila, na fuskanci hari daga Isra'ila har sau uku ta hanyar kai hari kan iyalina.

Na farko ya afku a ranar 21 ga watan Maris din 2021, dayan kuma a ranar 9 ga Mayu 2023, sai na kwanan nan da aka fara a ranar 7 ga Oktoban 2023, wanda shi ne mafi muni.

Wahalar da ba a taba tunani ba

Na tsira a yake-yake uku a lokacin d ana ke Gaza, amma ban taba tunanin saboda ina nesa da iyalina zan kasance cikin halin ɗimauci da damuwa fiye da sanda na ke tare da su, a yayin da ake kai musu hare-haren bam.

Kowanne yaƙi ya jefa ni a halin tsoro, amma wannan karon ya bar ni a cikin firgici mai tsanani da bakin ciki da ɓacin rai da fushi da ƙunar zuci da zabura.

Ba kamar sauran rikici na baya ba, babu wani Bafalasdine da zai koma ƙalau garas da shi bayan fuskantar wannan ibtila'i.

Wannan yaki da ke da manufar tirsasawa Falasdinawa barin matsugunansu, wanda ke kama da sabuwar Nakba (Balahira), a yayin da jami'an tsaron Isra'ila suke bayar da shawarar a bar Gaza a koma Tsibirin Sinai.

Nakba ta farko ta afku ne a 1948, kuma tun wannan lokacin, Falasdinawa da dama ba su samu damar komawa matsugunansu ba.

Wannan yaƙi na kuma da gangan yake koma wa ma kare dangi, kisan gilla ga yara ƙanana da raba mutane da matsugunansu, ƙasƙantar da mutanenmu da yaɗa labaran ɓata suna a duniya.

A fadin duniya na gudanar da zanga-zanga da dama don goyon bayan Falasdinawa tun bayan da Isra'ila ta fara kai musu harin bama-bamai a Gaza. Hoto: AA

Farfagandar da kafafan yada labarai ke yi da labaran ƙarya, ciki har da na Ingila, ya sanya ni shiga halin tsananin damuwa.

'Yan siyasa masu nuna wariya

Falasdinawa da dama da suka hada da ni na jin ba sa samun nutsuwa saboda yawaitar bin diddigi da tauye haƙƙoƙin magana da ake yi musu a Ingila.

Mafi yawan kanun labaran kafafan yada labarai na Ingila, wadanda ake haskawa a jiragen kasa, kan tituna ko yanar gizo, duk sun mayar da hankali kan Isra'ila, wanda da wahala ka ga an kawo batun rasa rayuka da Falasdinawa ke yi ba.

Ya zama sai ka ce kafafan yada labarai na Ingila suna halasta kisan kare dangin da ake yi da gan-gan.

Duk da cewa ana yada yadda ake kashe Falasdinawa kai tsaye a kafafan talabijin, amma kafafan yada labarai na Ingila sun ci gaba da bayyana ai Isra'ila ake kashewa.

Ya kamata a ce ana nuna yadda Isra'ila ke kai hare-hare, sannan a bai wa ra'ayi, buƙatu da shaidarmu muhimmanci kamar yadda mu Falasdinawa ke bukata.

Tun 7 ga Oktoba, mafi yawan manyan 'yan siyasar Ingila sun dinga bayani kan nuna ra'ayin karkata ga bangare daya, suna rera taken "Muna Goyon Bayan Isra'ila" kamar matsayin Firaminista Rishi Sunak.

Mazauna Gaza na ci gaba da fuskantar ruwan bama-bamai daga Isra'ila tare da kashe dubunnan su. Hoto: AFP

A yayin ziyarar da ya kai Isra'ila, Sunak ya bayyana goyon bayansa ga Isra'ila ba tare da la'anta ko sukar munanan hare-haren da ake kai wa kan jama'ar Zirin Gaza ba a yaƙin da ake yi.

Ƙarara, bai ma umarci wakinin Ingila a MDD ya bukaci da a tsagaita wuta ba, wanda mataki ne mai muhimmanci na kubutar da rayuka da dakatar da rikicin.

Abun takaici, sama da Falasdinawa dubu bakwai da suka hada da yara dubu uku, sun rasa rayukansu.

Sunak ya nace kan cewa wannan 'yancin Isra'ila ne na kare kanta, inda ya yi watsi da batun Isra'ila na keta dokokin kasa da kasa suna aikata kisan kare dangi kan Falasdinawa.

A wasu lokutan ya yi kira ga isra'ila da ta yi aiki da dokokin kasa da kasa wajen mayar da martani da take yi, wajen kisan kiyashi ga dubunnan iyalan Falasdinawa da ke Gaza.

Da yake kara rura wutar lamarin, Suella Braverman, Sakataren Cikin Gida na Ingila a ranar 10 ga Oktoba 2023, ya rubuta wasiƙa ga shugaban Jami'an tsaron Ingila da Whales.

Ya dinga umartar 'yan sanda da su yi amfani da duk wani ƙarfi wajen murƙushe wadanda suka fito suna nuna goyon baya ga Hamas, amma abun da yake nufi shi ne masu nuna goya baya ga Falasdin.

Lamarin ya wuce yadda ake zato

Wannan ya haɗa da ɗaga tutar Falasdinu, wanda ake kallon wani nau'i na "tsangwama" ga jama'ar Yahudawa, da kuma zanga-zangar kira ga 'yantar da Falasdin.

Dadin dadawa, kalamai da ayyukan Braverman sun zama masu goyon bayan bangare daya, wanda ke bayyana goyon baya da taimakon jama'ar Yahudawa a Landan ba tare da duba ga jama'ar Falasdin da ke zaune a kasar ba, wadanda su ma wani bangare ne nata.

Wannan ya kirkiri yanayin rashin adalci, inda muke jin kamar mu ba mutane ba ne da ke da daraja da 'yanci.

Misali, wata kawata wadda ta zo Ingila daga Falasdin amma ta biyo ta kasar Jordan, kuma a cikin jirgin sama dauke da Falasdinawa.

Ƴan kasar Jordan da Yahudawa, ta lura da cewa a filin tashi da saukar jiragen saman akwai wani waje da ake bayar da taimakon lafiyar ƙwaƙwalwa ga Yahudawa. Amma an yi biris da mummunan halin da Falasdinawa suka shiga.

Abun da yake afkuwa a Gaza ya yi daidai da 'Bala'i', Wata kawata da ke Gaza ta bayyana haka ta shafin X inda ta ce "Kalmar 'bala'i' ba za ta bayyana irin yanayin da ake ciki a Gaza ba.

Abubuwan fashewa masu nauyi sun dinga fada wa Gaza dare da rana. Mun jure duk wani nau'i na rashi wanda ba a taba tsammanin sa ba.

An ƙarar da iyalai

Ba ma iya ganin sararin samaniyar garinmu, kasarta a yanzu ta zama ruwan toka, baka kirin saboda kwararar jinin wadanda aka kashe.

Ko ina tsit, an ɗimauta kowa. Kalmar da kowa ke fadi na iya zama ta ƙarshe, kuma duk wani kira da ake yi na bankwana ne."

A ranar 7 ga Oktoba ka fara rikici a Gaza. Hoto: AA

Irin yadda ta yi bayanin abubuwan da ke faruwa, ya tattara yadda komai yake afkuwa a yankin.

Na ji labarai marasa dadi masu tayar da hankali daga bakunan mutanen da ke zaune a yankin, kuma dangina sun rasa mutane biyar, ciki har da 'yan'uwan matata da wasu yara ƙanana huɗu da abokai, ciki har da masu zama a Ingila.

Mu da muke zaune a kasashen waje muna kira da babbar murya kan a tsagaita wuta a Gaza don kawo karshen rikicin. Mun rasa 'yan uwa da abokai da dama, kuma ba za mu yarda mu ci gaba da rasa su ba.

Dadin dadawa, ana shafe irin tunanin da muke da shi na yarinta, inda fasalin yankin ke sauyawa saboda ruwan bama-baman da ake yi, ana rushe gidaje da makarantu da asibitoci da sauran manyan wurare da ke yankin Gaza.

Babu abun da zai ba mu tsoro

Wannan ne ya sanya ni, tare da wasu karin Falasdinawa daga Gaza, muke yin kiran da a tsagaita wuta cikin gaggawa.

Matasan Falasdinawa da ke kasashen katare sun fitar da sanarwa, suna kira ga kasashen duniya da su dauki matakin nuna goyon baya ga tsagaita wuta, dawo da bayar da ruwa da ake bukata cikin gaggawa da aika kayan abinci da fetur da magunguna da taimakon jinƙai, tare da bayar da damar fita da wadanda aka jikkata daga yankin Gaza.

Haka zalika, ga Falasdiwan da ke rayuwa a Ingila, ni ina son na ji ni cikin yanayi mai tsaro, sannan ina so a fahimci irin yadda muke shan wahala, sannan a bayar da tarihinmu yadda yake.

Me ya sa saboda kawai mu Falasdinawa ne hakan zai hana mu samun girmamawa?

Kasancewar mu Falasdinawa ba zai hana mu bayyana ra'ayi, halin tsananin da muke ciki, ko kuma nuna goyon baya ga 'yan uwanmu ta hanyoyi daban-daban ba, ko hakan zai faru ta hanyar daga tutar Falasdin ko saka kaya masu dauke da alamar kasar Falasdinawa.

Marubuciya, Hadil Louz 'yar kasar Falasdin ce da ke karatun digirgir a Ingila.

Togaciya: Ra'ayoyin da mawallafin ya bayyana ba dole ba ne su zo daidai da ra'ayoyi, hange ko manufofin TRT Afrika.

TRT Afrika