A yayin da Isra'ila ke tsaka da kai munanan hare-hare Gaza, Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya yi adawa da farfagandar ayyana Hamas a matsayin 'kungiyar ta'addanci'.
A maimakon haka sai ya bayyana ta a matsayin "kungiyar neman 'yanci da ke fafutukar kare yankunan Falasdinu." Piers Morgan, mai gabatar da wani shahararren shiri na talabijin mai taken "Uncensored," ya bayyana kalaman Erdogan a matsayin "bai wa Hamas kariya mai ban tsoro."
Morgan ya ci gaba da cewa "Ina goyon bayan manufar Isra'ila ta kawar da Hamas. Su (Hamas) masu shan jini ne, gungun 'yan ta'adda masu tasowa."
Wannan ita ce matsayar galibin ƙasashen Yammacin Duniya da ƙawayensu masu biyayya kamar Indiya, waɗanda ke sanya 'yan kasarsu cikin duhu game da gaskiyar mamayar da Isra'ila ke yi wa Falasdinu.
A wata hirar daban, Morgan ya tambayi jakadan Falasdinu Husam Zomlot ko ya "yi tir da hare-haren Hamas na ranar 7 ga Oktoba."
Iyayen tafka shirme
A bayyane yake cewa, Morgan yana bin ra'ayin abin da manyan Yammacin Duniya suka yaɗa a tarihi game da Falasdinawa da Hamas: shirmammu. Masanin Falsafa Harry Frankfurt yana kallon shirmen a matsayin batun da bai damu da gaskiya ba.
Saboda haka, shirme ya fi ƙarya haɗari. Yayin da yake ɓoyewa, maƙaryaci yana damuwa game da gaskiya. Mai cin zarafi kuwa sai akasin haka, yana watsi da gaskiya ne kawai.
Magance shirme ba shi ne amsa tambaya mai tabbatar da rashin adalci kamar ta Morgan ba, amma a maimakon haka sai a yi magana ta samar da adalci: a samu ƙawayen Isra'ila su yi Allah wadai da mamayar Falasdinu - mai hade da aƙidar ƙabilanci ta tsananin son kafa ƙasar Isra'ila - da yawan cin zalin Falasdinawa da ake yi.
Yin irin waɗannan tambayoyin ita ce gaskiya ga tarihi, wacce masu mulki ke yawan yin adawa da ita. A cikin littafinsa, Rashid Khalidi, wani masani Ba’amurke Bafalasɗine, ya rubuta yadda “Masu mulkin mallaka ƴan kama wuri zauna” Isra’ila, da farko tare da Birtaniya da Faransa, daga baya kuma tare da Amurka, suka ƙaddamar da yaƙi na tsawon karni a kan Falasdinu daga shekarar 1917 zuwa 2017.
Wata hanyar da ake yaɗa wani nau'in ta'addanci game da Falasdinu ba ta hanyar ma'aikatan kafofin watsa labarai na yau da kullum ba ne, sai ta hanyar wasu ƴan amshin shata na ƙarya da aka yi hayarsu daga waje.
Wata kafar watsa labarai a Indiya ta taɓa rubuta wani ra'ayi mai taken: "Ko da za a wayi gari babu Isra'ila, Musulmai za su ci gaba da zame wa Yahudawa barazana — Wannan ita ce matsalar."
An yi amfani da sunan bogi Khaldun Bharati, a matsayin na marubucin ra'ayin. A cikin ɗan gajeren bayani a kan marubucin an rubuta cewa "a matsayin ɗalibin Musulunci ... (wanda)... yake kallon tarihin Musulunci daga mahangar Indiya."
Wallafa wannan ra'ayi mai cike da ƙiyayya da wata kafar yaɗa labarai ta Indiya ta buga da sunan maruubuci na bogi, na nuna irin yaɗuwar aƙidar son kafa ƙasar isra'ila a cikin nahiyar Asiya, da kuma tsabar tsaurin aƙida ta marucubin da kuma kafar yada labaran.
Irin wadannan ayyukan rashin ɗa'a na 'yan kasuwar buƙata da 'yan amshin shata na ƙarya, suna matuƙar taka rawai wajen ci gaba da mamayar Falasdinawa da kuma ɓata sunan gwagwarmayar neman 'yanci.
Babu wani babban ɗalibin tarihi - ciki kuwa har da sanannun malamai Yahudawa irin su Ilan Pappe da Norman Finkelstein - balle wanda ya yi iƙirarin yin nazarin tarihin Musulunci, da zai rubuta ra'ayi a game da batun "Isra'ila da Falasdinawa" kuma ya shafe tarihin mulkin mallaka da danniya, kamar yadda Bharati ya wallafa nasa ra'ayin mai cike da ƙarairayi na rashin kunya.
Gaza a 2023 da Warsaw Ghetto a 1943
Isra'ila ta ba da hujjarta ta ci gaba da kai hare-hare a Gaza a matsayin ramuwar gayya ga harin da Hamas ta kai a watan Oktoba.
Amma gaskiyar magana, in ji Emad Moussa, wani mai bincike ɗan Falasdinu da Burtaniya, ita ce "tun shekarar 1948, Isra'ila ke shirin mamaye Gaza da korar Falasɗinawa.
Wannan muhimmin batu yana danganta abin da ake ciki yanzu tare da tushen muradin aƙidar tabbatar da ƙasar Isra'ila ta hanyar korar da kawar da waɗanda ba Yahudawa ba.
Yaƙe-yaƙen da Isra'ila kan yi daga lokaci zuwa lokaci a kan Gaza a shekarun 2008-9 da 2012 da 2014 da 2021, suna yi ne ba tare da la'akari da ayyukan Hamas ba.
A ajiye batun sunaye na yaudara na waɗannan yaƙe-yaƙe (wanda ke nuna manufofin faɗaɗa Isra'ila a matsayin kariya), a Gaza: A cikin littafin An Inquest Into Its Martyrdom, Finkelstein ya rubuta cewa "Isra'ila sau da yawa ba ta mayar da martani ga gazawar Hamas" kuma Hamas "ta ƙi bai wa Isra'ila damar nuna ta a matsayin ƙungiyar ta'addanci yadda za ta ta samu dama sosai ta ƙaddamar da yaƙinta.
Don haka ba a iya fahimtar aikin Hamas ba dangane da siffanta ta a matsayin "masu shan jini ko gungun 'yan ta'adda" da Morgan ya siffantata ko kuma a matsayin "gungun mahaukata" da Yossi Beilin, tsohon ministan Isra'ila ya bayyana su.
Kwatanta Falasdinawa da tsohon jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya, Dan Gillerman ya yi a matsayin "dabbobi a siffar ƴan'adam" shi ma babban misali ne na shirme.
Wani bayani mai cike da tarihi na aikin Hamas zai yi kyau wajen kwatanta halin da Falasdinawan suke ciki da na Yahudawa a yankin Warsaw.
A shekarar 1943, Yahudawa sun bijirewa mamayar ƴan Nazi wadda a ƙarƙashinta rayuwarsu ta yi matuƙar ƙuntata.
Morgan, Beilin, Gillerman da sauransu suna tsoron wannan kwatancen daidai domin ya rusa iƙirarin da Isra'ila ke yi a matsayin wadda aka azabtar har abada.
Bugu da ƙari, ya kuma nuna su a matsayin masu kisan ƙare dangi fiye ko ƙasa da yadda Ƴan Nazi na Jamus suka kafa ta a farkon ƙarni na 20.
A matsayin wani yanki, baki ɗayan tsawon Gaza kilomita 40 ne sai faɗinta kuma kilomita tara. Daga cikin al'ummarta miliyan 2.3, mafi yawansu zuriyar 'yan gudun hijirar Falasdinawa ne da aka kora daga gidajensu cikin wulaƙanci a yaƙin shekarar 1948.
Gaza da yake kewaye da wani katafaren yanki, Isra'ila ta rufe sararin samaniyarta da ruwan yankinta don hana Zirin amfana. Yana ɗaya daga cikin yankunan da ke da yawan jama'a a duniya.
An hana Falasdinawa 'yancin shiga da fita daga cikin ƙasarsu, tare da zagaye su da shingayen binciken sojoji, Falasɗinawa na zama cikin tsananin sa ido da takura.
A ɗaya daga cikin abubuwan da suka taɓa faruwa, a shekarar 2008 kawai aka bai wa kashi 20 cikin 100 na mutanen da ke fama da cututtuka kamar ciwon daji da matsalolin zuciya "izinin" su fita waje don neman magani, kuma ko da samun kashi 20 cikin 100 na wasu muhimman magungunan ya yi "matuƙar wahala."
A cewar Bankin Duniya, a shekarar 2021 talauci a Gaza ya kai kashi 59 cikin 100, wanda ya yi matukar ƙaruwa daga kashi 39 a shekarar 2011.
Adadin marasa aikin yi a halin yanzu ya kai kashi 45 cikin 100 sannan adadin magidanta da ke fama da ƙarancin abinci ya kai kashi 64 cikin 100.
A bayyane yake, waɗannan abubuwan ban mamaki sakamako ne kai tsaye na takunkuman tattalin arziki da suke ciki.
A shekarar 2007 ne Isra'ila ta ƙaƙabawa Gaza takunkumai ta sama da ta ƙasa da ta ruwa, bayan nasarar da Hamas ta yi a zaɓukan Falasɗinu.
Sai dai, a cewar Khalidi, tun shekarun 1990 aka fara ganin matakan hana zirga-zirgar mutane da kayayyaki da gina katangar tsaro da sauransu, a lokacin “yarjejeniyar zaman lafiya ta Oslo.”
A shekarar 2008, wata hukumar Majalisar Dinkin Duniya ta tattara bayani cewa takunkuman da Isra'ila ta saka sun haifar da mummunan rikicin taɓa mutuncin ɗan'adam, wanda ya haifar da taɓarɓarewar yanayin rayuwa.
Tun kafin wannan takunkuman, a shekarar 2003, Baruch Kimmerling, wani masanin ilimin zamantakewa a Jami’ar Hebrew, ya kwatanta Gaza a matsayin “sansani mafi girma da cunkoso da ya taɓa wanzuwa.”
A cikin halin da ake ciki na kai hare-hare ba ƙaƙƙautawa, an ga wata yarinya ƴar Gaza a cikin wani bidiyo a shafukan sada zumunta tana tambaya: shin mutanen Gaza “wata bola ce”? Muna fuskantar abin da masanin falsafa ɗan Italiya Giorgio Agamben ya kira "rayuwa tsirara", wuraren da aka kwatanta su ne sansanonin ƴan Nazi a Jamus.
Kwatanta Gaza da hedikwatar Yahudawa. Bayan sun mamaye Poland, ‘yan Nazi sun kafa sansanin Warsaw a shekarar 1940. Don a gane manufar Reich ta zama "ƴantacce daga Yahudawa,’ an umurci Yahudawan da aka tarwatsa su ƙaura zuwa wani yanki da aka keɓe.
Ba kamar Gaza a matsayin sansani mai cunkoso ba, wanda ke Warsaw ya kasance ƙarami: mai girman kusan murabba'in kilomita 2.5, inda Yahudawa kusan rabin miliyan suka rayu a wajen. Kamar Gaza, an kewaye shi da katanga mai tsayin mita uku.
An sa dokar hana zirga-zirga a ciki da wajen sansanin Warsaw ghetto. Kamar a Gaza, a sansanin Warsaw ma, mazaunan da ke da izini na musamman ne kawai za su iya fita daga cikinsa. Ana raba kayan abinci.
Da aka kai matakin cin mutuncinsu da kuma tafiyar da rayuwarsu tamkar ba mutane ba, a lokacin da aka fara korar Yahudawa zuwa sansanonin mutuwa, sai aka bar waɗanda suka rage a cikin sansanin na ghetto ya kasance ba ta zaɓin su mutu ko su yi rai suke yi ba, suna cikin yanayi ne na fatan su mutu a mutunce maimakon a kashe su kamar dabbobin farauta.
Da suka zaɓi tsira da mutunci, sai Yahudawan suka kafa wata ƙungiyar ƙwatar ƴanci mai suna Jewish Combat Organization, ZOB. A watan Afrilun 1943, kowane mutum daga cikin mayaƙan ƙungiyar ZOB 500 yana da bindiga da wasu gurneti.
Sai kuma mambobi 400 na wata ƙungiyar gwagwarmaya da suke da manyan bindiga 31 da kuma ƙananan bindigogi 21. Irin waɗannan makaman, duk da haka, ba su ko kamar ƙafar na sojojin Nazi ba.
A cikin watan Mayun 1943, an murƙushe gwagwarmayar tasu. An kashe Yahudawa ko dai a wajen faɗan ko kuma da aka kore su zuwa sansanonin mutuwa, sannan kuma aka rushe sansanin da suke cunkushe mai fadin murabba'in kilomita 2.5 ya koma ɓaraguzai.
Yahudawan da suka tashi tsayin daka don kare kansu ba ’yan ta’adda ba ne; sai dai kamar Falasdinawa a yanzu, a wancan lokacin mamayar Nazi ta tsoratar da su.
Kamar rayuwar yawancin Falasdinawa a yanzu, ta Yahudawa a cikin Warsaw ghetto ma tamkar sun sanya hannu ne kan wata hanyar ƙasƙantar da su da jin tsoron "fuskantar wulaƙanci" a kowane lokaci".
A cikin rubutunsa, Primo Levi, wanda ya tsira daga kisan kiyashi, ya kwatanta Yahudawan da ke sansanin fursuna da Musulmai. Ya rubuta: “Ni, mai magana, kamar Musulmi ne nake, wato, wanda ba ya iya magana ta kowace hanya.
A cikin ragowar abin da Auschwitz ya bari, Agamben ya sake fasalin ra'ayin Lawi don danganta shi da ainihin tsarin mulkin zamani. Amma da alama Agamben ya fi sha'awar yin magana fiye da batun saurare.
Tambayar da muke fuskanta ita ce: shin duniya tana sauraron ’yan'adam a sansanin Gaza da ke cikin ƙawanya, waɗanda har yanzu aka hana su walwalar samun ƙauna da adalci da mutunci, suka yi magana? Abu mafi muhimmanci, shin duniya za ta ji? Kuma idan za ta ji to sai zuwa yaushe kuma ta yaya?