Avinoam Emunah ya yi kaurin suna wajen yakin da Isra'ila ta kaddamar kan Gaza a shekarar 2014/ Hoto: TRT World

Isra’ila ta kafa Rundunar Tsaron Kasa ta ‘National Guard’ karkashin ikon Ministan Tsaron Kasa mai ra’ayin rikau Itamar Ben-Gvir.

Masu rajin kare hakkin dan adam na kallon rundunar a matsayin "ta mayakan sa-kai mai zaman kanta " wadda aka samar don kai wa Falasdinawa hari kawai.

Hasali ma, sunayen unguwannin Falasdinawa kawai Ben-Gvir ya bayyana a matsayin inda za a tura dakarun National Guard, da kuma kan iyakokin Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye.

Amma, wane ne Ben-Gvir zai zaba ya jagoranci rundunar, wadda ke da jami'ai 2,000?

Da alama wanda ke kan gaba a cikin wadanda yake tunanin bai wa aikin shi ne Kanal Avinoam Emunah mai ritaya, mai shekara 43, wanda aka fi sani kan tsauraran ra’ayoyinsa game da Falasdinawa.

A lokacin aikinsa na soji, Emunah ya yi aiki a cikin gogaggun sojoji masu dirar mikiya, kuma ya samu damar jagorantar runduna ta 101 wadda ta yi kaurin suna cikin sojin Isra’ila, da aka bai wa aikin kai farmaki da hare-hare kan Falasdinawa tsakanin 1953 zuwa 1954.

A matsayinsa na sojin rundunar ta 101, Emunah yana da hannu a “kazamin fada da kuma yake-yake na danne Falasdinawa a lokacin Intifada na biyu, harin da aka kai Lebanon a 2006 da kuma yakin da aka kaddamar kan Gaza a 2014,” in ji dan Isra’ila mai sharhi, Shir Hever.

Hever, mamban gudanarwa na kungiyar Yahudawa mai neman zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya (Jewish Voice for a Just Peace in the Middle East), ya ce aikin sojin Emunan “ya saka shi a turbar samun ci gaba cikin gaggawa”.

Emunah ya yi kwamanda a makarantar koyar da dabarun yakin sojin Isra’ila, kuma ya jagoranci bangaren Hermon a Tuddan Golan na Siriya da aka mamaye.

Amma an fi saninsa da jagorancin da ya yi a lokacin da Isra’ila ta kai hari kan Gaza a shekarar 2014, harin da aka yi wa lakabi da “Operation Protective Edge”, wanda ya kashe Falasdinawa tsakanin 2,125 zuwa 2,310, kuma ya samar wa Emunah lambar yabo ta janar mai jagoranci.

An san Emunah da tsattsauran ra’ayin addini, kuma sunansa na karshe na nufin “Imani” a harshen Yahudanci.

Ya kuma alakanta nasarorin da yake samu a hare-hare da ababen al’ajabi, kamar yadda marubuci Rogel Alpher ya ce a cikin wata makala ta bayyana ra’ayi da aka wallafa a wata kafar watsa labarai ta Isra’ila.

Ya kuma taba jan hankalin kafafen watsa labarai don kin yarda da mace a matsayin kakakin rundunar saboda akidarsa ta addini.

Zafafan kalamansa na tayar da hankali kan Falasdinawa masu kaurin suna sun bayyana cikin bidiyoyin bayanin da ya yi ga dakaru a Gaza a lokacin farmakin 2014.

“Balarabe ba zai ji dadi da daddare a nan ba,” kamar yadda aka ji Emunah yana fada cikin dariya da tafi.

Ya ce dakarun za su ga Falasdinawa suna guduwa, kuma ya ba su umarni cewar su “kashe su a lokacin da suke tserewa .” Dakarunsa sun tafa kuma suka amsa da cewar, “Haka ne, mai gida”.

Don ya ba su kwarin gwiwa, Emunah yana karfafa wa dakarunsa gwiwa su yi “dariya” kuma su yi kokari su “ji dadin” kisan “Larabawa”.

Sha’awar amfani da karfi

Alpter ya ce umarnin “kisa” da Emunah ya bayar ya bayyanar da halayyarsa a fili, yana yaki ne tamkar farautar namun daji ba tare da la’akari da dokar kasa-da-kasa ba.

“Ana yaki ne bisa dokar kasa-da-kasa, wanda ke bukatar wani mataki na mutunci, tausayi da kuma girmamawa. Idan babu wannan, kisan zai kasance ba bisa ka’ida ba, kuma zai zama kisan kai kawai,” kamar yadda Alpter ya rubuta.

Alpter ya yi bayanin cewar wadannan dokokin sun ce da zarar soja ya mika wuya, ba za a iya kashe shi ba, kuma ana ganin dukkan wani abun da ya saba wa wannan laifin yaki ne, wanda shi ne Emunah yake ciyar da shi gaba.

Hasali ma, shaukin da Emunah ke da shi ga amfani da karfin tuwo ka iya kasancewa abin da ya sa aka hana shi karin girma kuma ya sa ya bar sojin Isra’ila a shekarar da ta gabata bayan ya shafe shekara 24 yana aiki, kamar yadda jaridar masu ra’ayin rikau ta Arutz Sheva ta ruwaito tana mai ambaton manyan sojin Isra’ila.

"A fahimtata, labarin tsoro da zafin rai da tsaurin zuciya da ke fitowa daga gare shi ne wani abu ne da ke da dan ban tsoro, wani mutum mai ban tsoro ne a cikin wannan yanayin," kamar yadda aka ambato wata majiya ta soji na cewa.

Majiyar ta ce Emunah ya kira Falasdinawa da sunan “beraye” kuma yana hukunta duk sojan da bai yi amfani da karfi sosai ba a kan 'yan Gaza da aka yi wa kawanya.

Duka da cewar ya yi “tsauri sosai”, majiyoyin sun ce, “da ya gama aikinsa jami'ai sun zub da hawaye kan tunanin wa zai maye gurbinsa”.

Murabus din Emunah ya janyo zanga-zanga, kuma ‘yan siyasa sun fara kare shi, kamar yadda dan majalisar dokoki na adawa Matan Kahana, wanda ya taba aikin soji, ya yabi kanal din a wata budaddiyar wasika.

“Kanal Avinoam, kamar yadda aka ambato, ba mu san juna ba. Amma daga duk abubuwan da na karanta kuma na ji game da kai, akwai abubuwa da yawa da ya kamata mu gode maka sosai a kai,” kamar yadda ya rubuta, yana mai karawa da cewar yana jin bacin rai ko tausayi a lokacin da ya tuna duk abubuwan da Emunah ya yi.

“An zabe ka don ka zamaabin kwaikwayo ga wadanda za su zo a baya cikin kwamandoji."

‘Yi murmushi-ji dadi-kashe’ wani misali ne kawai

Taken Emunah na “yi murmushi-ji dadi-kashe,” wani misali daya ne kawai na wuce gona da iri na sojojin Isra’ila wajen tunani na rashin tausayi da kuma yadda suke yi da Falasdinawa, kamar yadda labaran da tsofaffin sojojin Isra’ila suka bayar suka nuna.

Yahuda Shaul ya yi aiki a Yamma da Kogin Jodan da aka mamaye na shekara biyu, kuma bayan abin da ya gani, ya yanke shawarar kafa Breaking the Silence, wata kungiya da ke tattara bayanai daga sojojin Isra’ila don fallasa mawuyacin halin mamayar.

“Na yi aikin soji ina da imanin cewar ni mutumin kwarai ne kuma mu ne muke bangare na kwarai," kamar yadda ya fada a wata hira da France 24.

Shaul ya yi magana game da yadda aka koya wa dakaru su rinka gallaza wa Falasdinawa”.

Ya ce a lokacin da yake aiki na wata 14 a Hebron, ana sintirin soji biyu wanda aikinsu ne su “sa a san muna nan” da kuma “sa mutane su ji cewa ana zaluntar su”.

Daya daga cikin hanyoyin da suka yi wannan shi ne sun rinka zaban gidajen Falasdinawa don su bai wa iyalan da ke ciki tsoro, in ji Yahuda.

TRT World