A wata sanarwa da ta gabata, Ma'aikatar Lafiya ta ce akalla yara 143 da mata 105 aka kashe a hare-haren Isra'ila kan Gaza. / Hoto: AFP / Photo: AA

Daga Burak Elmali

Idan ka auna rikicin da ke faruwa a 'yan tsakanin nan, inda yaki ya turnuke, ga kuma yadda ra'ayoyi ke shan bamban daga bangarori biyu, abin yana da wahalar gano yadda alaka take tsakanin sassan rikicin.

Sai dai kuma, abubuwa da yawa sun faru cikin gomman shekaru ta yadda za ka iya fahimtar abin da ke faruwa dangane da dadadden batun Falasdinawa, da abin da rikicin ke nufi ga masu ruwa da tsaki a batun.

Amsar wannan matsala tana cikin tarihin abubuwan da suka faru a baya, kuma matukar ba a yi nazarin tarihin ba, to kuwa za a sake tafka kuskure wajen fahimtar abin da zai faru gobe.

A safiyar ranar 7 ga wata Oktoba, dakarun Rundunar Hamas Qassam sun kaddamar da wani kutse daga cikin Gaza, inda suka far wa kudancin Isra'ila, ta sama da kasa da ruwa, a wani hari da suka kira da "Ambaliyar Al-Aqsa".

Hamas ta yi amfani da dubban makamai masu linzami. Wannan yaki ya janyo gagarumar asarar rayuka a duka bangarorin biyu. Yayin da Hamas take rike da 'yan Isra'ila da suka hada da jami'an soji, don neman musaya a tattaunawa nan gaba.

Tasirin wannan rikici kan dubban 'yan Isra'ila a fili yake. Wani abu da yake a bayyane shi ne: jami'an leken asiri na Isra'ila da jami'an tsaron kasar sun sha kunya.

Wannan yana tilastawa mu yi tambaya kan wani babban kalubale: mene ne asalin abin da ya kawo mu zuwa ga wannan mataki? Wadanne batutuwa ne ke binne a karkashin kasar rikicin Isra'ila da Falasdinawa?

Har sai mun nemo amsar kafin duk wani mai sharhi ya iya zama mara nuna son-kai, kamar yadda kasashen Yamma ke kokarin nuna dacewar laifukan da Isra'ila take yi, suna yin watsi da makomar Falasdinawa da ke rayuwa a Gaza, karkashin yanayi na budadden gidan yari.

Musabbabin rikicin yau za a iya gano shi daga halayyar Isra'ila, da suka hada da kokarin mulkin mallaka, duk da irin Allah wadai da kuma kudurorin Majalisar Dinkin Duniya kan laifukanta.

Halayyar mulkin mallaka yanzu ta koma wani irin tsari na kafa zalunci, domin yin tarnaki kan hadin-kan duniya bisa batun Falasdinawa, don samar da kasashe biyu bisa iyakokin shekarar 1967.

Kasar Isra'ila da 'yan kama-wuri-zauna da ke far ma fararen hula, suke korar Falasdinawa daga gidajensu, da hana kayayyakin jinkai daga kasashen waje, duka sun saba wa 'yanci da hakkokin al'ummar Falasdinu da aka mamaye cikin killataccen yankin da bai wuce 'yan kilomita ba.

Ba za a yi tunanin cewa irin wannan kokarin turjiya na al'ummar Falasdinawa na ci gaba da jure fitinar Isra'ila ba, ya dore har abada.

Fahimtar wannan gaskiya ba ya nufin cewa hari kan farar hula daga kowane bangare sabon abu ba ne. Gano dadadden tasirin rikicin kan tunanin al'umma, shi zai sa a fahimci ainihin matsalar ta yau.

Cikin 'yan kwanaki na baya-baya nan, masu ruwa da tsaki na ciki da waje, da masu rikicin siyasar cikin-gida a Isra'ila, da karuwar tasirin kasar Iran a yankin, da zargin tallafawa Hamas da kayan yaki, da kuma yiwuwar shigar Hezbollah ta Lebanon da Syria idan Iran ta ga alamun babbar barazana — duka wadannan ana duba yiwuwarsu a cewar 'yan jarida.

Amma kuma, wani abu guda a bayyane yake: amsar yadda aka yi muka kawo wannan mataki ba za a same ta ba, ba tare da ambato abin da ya faru a tarihi ba.

Ba tare da samar da 'yancin siyasa ba ga Falasdinu, tare kuma da shigar kasar lamuran duniya ta hanyar dimukradiyya, da hukumomi masu dorewa, da cigaban tattalin arziki, duka masu ruwa da tsaki za su ci gaba da neman mafita ba tare da waiwayar sauran bangarori ba.

A zahiri, matsalar da ke ci yanzu a yankin ita ce gamuwar tarnakin da aka saka a shirin Falasdinu na zamowa cikakkiyar kasa, wanda wani dalili ne da ya haifar da rikicin kwanan nan.

Don saka shirin zaman lafiya a turbar cigaba, yana da muhimmanci a karfafa dabarun da za su lura da hakkin al'ummar Falasdinawa, don tabbatar da ba a manta da su ba.

Koma dai me ne, su ne ke shan wahalar wannan rashin adalci, don haka dole a saurari korafinsu. Don haka, zabin diflomasiyya shi zai shige gaba, ko da kuwa masu sharhi sun ci gaba da dagula abin ta hanyar raina batun Falasdinawa.

A takaice, diflomasiyya ita ce hanyar samun cigaba, ko dai a fara ta yau, ko gobe. Kuma ana bukatar masu shiga tsakani da suka san aiki, duk sanda wannan yaki ya tsagaita.

Hukumar Tarayyar Turai da farko ta nuna cewa za ta dakatar da tallafin jin-kai ga Gaza, amma hakan bai faru ba.

Hatta cewa sun duba yiwuwar daukar wannan mataki, hujja ce ta cewa suna da nuna son-kai a zahiri, kuma ba su da niyyar adalci. Kenan, ba sa bukatar kasanacewa a teburin shawara.

Tun da fari, matsayar Turkiyya ita ce neman mafita. Shugaba Recep Tayyip Erdogan yana jaddada samar da kasashe biyu, tare da dakatar da wuta da nuna takatsantsan.

Yana ci gaba da tunkarar bangarorin biyu, sannan matakinsa na bijiro da shirin zaman lafiya na yankin wata dabara ce mai hikima.

Haka nan kuma, kasar Qatar tana sane da wannan hadari, kuma ta fito da wani shirin diflomasiyya kamar yadda matakanta na sasantawa tsakanin Hamas da gwamnatin Isra'ila na musayar fursunonin yake nunawa.

Sauran kasashen yankin Gulf su ma za su mayar da hankali kan batun Falasdinu daga yanzu, sabanin yadda suka wofantar da batun da yin zancen fatar baka. Wasunsu, kamar Saudiyya, za su iya shiga tsakani don sasantawa.

Dakatar da maimaituwar rikicin da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa, ita ce hanya daya da za ta biya wa kowa muradunsa, da rage tunzura juna a yankin, da janyo cigaban tattalin arziki ga kowane bangare.

Saboda haka, zabin hanyar diflomasiyya da zama teburin shawara tsakanin bangarorin ita ce hanya mafi a'ala.

Marubucin, Burak Elmali, Manazarci ne a Cibiyar Bincike ta TRT World a Istanbul. Yana da digiri na biyu a fannin Alakar Kasa da Kasa, daga Jami'ar Boğaziçi. Bincikensa ya kunshi batutuwan tsarin diflomasiyyar Turkiyya da gogayyar siyasa tsakanin Amurka da China, da tasirinsu a yankin Gulf.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba sa wakiltar mahanga da ra'ayoyin editocin TRT Afrika.

TRT Afrika