Sojojin Isra’ila suna ragargazar Falasdinawan Gaza ta sama da ta kasa. Hoto: Others 

Daga Yahya Habil

A daidai lokacin da ake cigaba da gwabza sabon yakin nan Falasdinawa da Isra’ila, daya daga cikin babatuwan da ake kawowa domin kare Isra’ila shi ne wai tana da ’yancin kare kanta da mutanenta daga hare-hare.

Matsalar wannan tunanin da ma’aunin ita ce ana auna Isra’ilar ce kadai, wadda ita kuma kasa ce da aka assasa ta hanyar korar dubban Falasdinawa, kamar yadda ake auna wasu kasashen kanana.

Abin da ake nufi a nan shi ne, abin da mutane da dama suka kasa fahimta shi ne, Isra’ila ba kamar kowace kasa ba ce, kasa ce da asali aka gina ta daga danniya ko kuma shirin “Nakba” inda aka kora asalin kabilun Falasdinawa a yankunan da suke zaune.

Irin wannan kasar, duba da yadda ta samo asali, ya kamata a tambaye ta ne wane hakkin kare kan take magana.

A daya bangaren kuma, bai kamata a yi mamaki ba idan Faladinawan da aka kora, aka mamaye musu garuruwa sun fito gwagwarmayar kwatar ’yancinsu, domin suna fada ne domin kasarsu wadda sojojin masu hankoron kafa kasar Yahudawa zalla da ’yan ta’adda suka kwace.

Shugaban Amurka Joe Biden tare da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a Tel Aviv. Hoto: Reuters

Wannan lamari shi ne abin da kasashen Yamma suka kasa fahimta. A wata sanarwa da ya fitar kwanan baya, tsohon Shugaban Kasar Amurka Barrack Obama ya bayyana cewa an raba Falasdinawa da dama da gidajensu a kokarin kafa kasar Isra’ila.

Abin shi kan shi Obama bai fahimta ba a nan shi ne, ta hanyar bayyana wannan tarihin kadai, ya tabbatar da cewa akwai matsala tun a farkon hanyar da aka bi wajen kafa kasar Isra’ila, wanda shi ne aka kira da “Nakba”

Amma duk da haka, a wajen kafafen yada labarai na Yamma da sauran magoya bayan masu hankoron kafa kasar Yahudawa zalla da kawayensu, Isra’ilar ce ke da alhakin kare kanta, ba Falasdinawa ba.

Haka kuma a wajensu, Hamas ce kungiyar ’yan ta’adda, ba Haganah ko Stern ba.

Shin ko dai saboda tambayar asalin kafa Isra’ila na da alaka ne da tambayar asalin kafa Amurka? Wato jagorar kasashen Yamma, wadda ita kanta asalinta an gina ta ne bisa danniya da korar asalin mutane garuruwan?

Isra’ila ta farmaki asibitoci da dama a Gaza tun bayan da aka fara wannan rikicin. Hoto: Reuters.

Su Falasdinawa, ciki har da kungiyar Hamas sun amince cewa Isra’ila ta riga ta samu wajen zama a yankin, wanda hakan ya sa suka amince da tsarin kasashe biyu na Majalisar Dinkin Duniya, amma ita Isra’ilar ta ki amincewa.

Maimakon haka, Isra’ila sai take cigaba da kokarin kutsawa ta Gabashin Jerusalem da West Bank (Yankunan da ko kadan ma babu Hamas) su kora Falasdinawa daga gidajensu, sannan su gina nasu gidajen.

Idan za a faro daga tushe, garuruwan Isra’ila tun na 1948 kamar su Haifa da Acre da Nazareth duk kwata suka yi.

Don haka, shin akwai laifi idan ka ce tsarin da aka assasa Isra’ila a kai, wanda shi ne tabbatar da kafa kasar Yahudawa zalla, shi ne yake kawo cikas ga samar da zaman lafiya mai dorewa?

Shin akwai laifi laifi idan ka ce idan har da gaske ana so a samu zaman lafiya, dole Isra’ila ta gyara dokokinta a game da Falasdinu, sannan ta yi watsi da son kai da fifita kai a kan kowa?

Marubuci, Yahya Habil, dan jarida ne mai zaman kansa daga Libya, wanda ya fi mayar da hankalinsa a kan harkokin da suka shafi Afrika. Yanzu haka yana aiki da wata kungiyar kwararru da ke Gabas ta Tsakiya.

Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridarTRT Afrika.

TRT World