Tashin hankali na baya-bayan nan ya fara ne a ranar 7 ga watan Oktoba inda Isra'ila ta yi ta kai ruwan bama-bamai a Gaza a wani martani na harin da Hamas ta kai mata. Hoto: Reuters  

Daga Aaliyah Vayez

A ranar 22 ga watan Nuwamba, aka cika kwana 46 a rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Falasdinu, wanda ya samo asali daga wani harin ba-zata da Hamas ta kai a ranar 7 ga Oktoban 2023.

Kawo yanzu an kashe sama da Falasdinawa 14,100 tare da jikkata sama da mutane 27,000, sannan Falasdinawa mutum miliyan 1.5 ne suka rasa matsugunansu.

Ci gaba da kawanyar da Isra'ila ke yi wa yankin Falasdinu da kuma kai hare-hare a zirin Gaza ya zama batun kisan kiyashi, wanda ya haifar da tashin hankali mafi muni na rikicin jin kai da duniya ta shaida a cikin 'yan shekarun nan.

Bayan haka, karin tashe-tashen hankula da yankin ke fuskanta ya farkar da duniya game da irin mamayar da Isra'ila ta yi ba bisa ƙa'ida ba na tsawon shekaru a Falasdinu, wanda a tarihi ya bijirewa dokokin kasa da kasa da na jinƙai.

Martanin Afirka game da rikicin

Kasashen Afirka sun gabatar da jawabai iri-iri na martani a hukumance game da abubuwan da suka faru tun daga a ranar 7 ga Oktoba, wadanda za a iya cewa sun yi daidai da matsayinsu kan rikicin Isra'ila da Falasdinu.

A wani bangare kuma wasu kasashe ma sun bayyana goyon bayansu ga samun ‘yancin kariyar kai wa Isra’ila, yayin da wasu kasashen suka fi nuna goyon bayansu kai tsaye ga samun ‘yancin kai na Falasdinawa da kuma tsayin daka kan mamayar Isra’ila.

Hamas da Isra'ila sun cimma matsaya a ranar Talata 21 ga watan Nuwamba wacce ta tanadi kai agajin jin kai yankin Gaza. Hoto: AA

Ko da yake, akwai wasu kasashe kadan da suka dauki matsayar tsaka tsaki tare da mayar da hankali kan a ba da fifiko kan kare hakkin dan'adam da bukatar tsagaita wuta da kuma matsayar samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu.

Bambancin da aka samu na wadannan ra'ayoyi da martani suna nuna alakar da ke tsakanin kasashen da Isra'ila da Falasdinu, da kuma muradunsu na siyasa da tattalin arziki da kuma dangantakarsu da kasashe, irinsu Amurka, wadanda suka bayyana matsayinsu kan rikicin.

Lamarin ya taka rawa matuka wajen nuna rudani da siyasar da ta shiga daga kasashen waje a bayanan baya-bayan nan da wakilan kasashe a Majalisar Dinkin Duniya (MDD) suka yi game da sharuddan daftarin kudurori da aka gabatar game da rikicin.

Duk da kudurin da kowacce kasa ta gabatar na neman a magance wannan rikici, da bukatar a gaggauta tsagaita bude wuta zuwa ga ba da fifiko wajen ayyukan jinƙai, ana ci gaba da kai hare-haren bama-bamai a zirin Gaza,

Kazalika ana ci gaba da take ka'idojin da tsarin kasa da kasa ta gindaya- kama daga kare hakkin 'dan adam da yancin kai da kuma dokokin kasa da kasa.

Ajandar Zaman Lafiya ta Afirka

Kasancewar sun fuskanci mulkin mallaka da kuma rikice-rikicen jinƙai, akwai bukatar a karfafa wa kasashen Afirka gwiwa ba wai ta hanyar ba gudummawa kawai ga wata matsaya ba ko kuma bin hanyoyin diflomasiyya da aka saba ba.

Kara tsanantar wannan rikici na baiwa kasashen Afirka dama ta nan take wajen samun madogara a sabon ajandar samar da zaman lafiya wanda ke kara karfafa lamiri amincewar duniya kan kare hakkokin bil'adama da dokokin kasa da kasa da na ɗan'adam da samar da zaman lafiya.

Irin wannan ajanda na bukatar samar da tsarin matakai daban-daban da suka soma daga kasashen Afirka da ke kira kan a gaggauta tsagaita bude wuta a dukkan yankunan Falasdinawa da aka yi wa mamaye.

A halin da ake ciki, zabin dake kan gaba shi ne tsagaita bude wuta don dakatar da asarar rayukan fararen hula da bala'in jinƙai da ake fuskanta.

Yayin da matsayar diflommasiyya daga kasashen Afirka za ta iya karfafa kiran da ake yi na tsagaita wuta na dindindin, akwai yiwuwar hakan ya yi tasiri idan har kasashen na Afirka suka hada kai ta hanyar amfani da kungiyoyin irin su Tarayyar Afirka da na yankin da kuma hadin gwiwar samar da zaman lafiya da tsaro.

Bugu da kari, kasashen Afirka za su iya daukar nauyi zaman samar da sulhu tare da kada kuri'ar amincewa da kudurin da ke neman tsagaita wuta a babban taron MDD.

Bayan haka, kasashen Afirka su ke rike da babbar kungiya ta masu kada kuri'a, don haka suna da damar da za su iya rike madafun iko na gama gari a Majalisar.

Kasashen duniya da dama sun yi ta zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinu domin mayar da martani ga farmakin da Isra'ila ke kaiwa Gaza. Hoto: Reuters

Kiran neman a tsagaita bude wuta zai samar da dama ta rage rikicin da kuma magance muhawarar siyasa da ake tafkawa a kasashen duniya tare da jaddada irin mummunan yanayin da aka shiga na jinƙai, kuma samun hakan zai yiwu ne kawai idan Isra'ila ta kawo karshen hare-haren da ta ke kaiwa.

Wannan ya haifar da babi na biyu a ajandar samar da zaman lafiya - dole ne kasashen Afirka su jagoranci hanyoyin kira da kuma samar da agajin jin-kai ga daukacin yankunan Falasdinawa da aka mamaye, musamman Gaza.

Ta hanyar yin haka, kasashen Afirka za su iya karfafa kasancewarsu a duniya ta hanyar inganta amincinsu da kuma nuna himmarsu ga ayyukan jin kai da kuma kiyaye ka'idojin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa.

Kazalika, akwai bukatar mai da hankali kan yunkurin sake gina Palasdinu bayan rikici wanda ke bukatar gayya kuma hakan zai bai wa kasashen Afirka damar ba da gudumowar albarkatu da lokaci da kuma kokarinsu wajen farfado da Falasdinu.

Baya ga wadannan abubuwa da aka ambato a baya, babi na uku ya kunshi matsin lamba na diflomasiyya da samar da matakan kariya diflomasiyya .

Dole kasashen Afirka su ci gaba da matsa lamba kan kasashe biyun da suke rikici da juna don tabbatar da cimma matsayar tsagaita wuta tare da karfafa ayyukan agajin jin kai.

Matsi na diflomasiyya na iya zuwa ne ta hanyar gabatar da bayanai ta diflomasiyya akai-kai da kuma samun babban matsayi da ayyuka na tallafawa shiga tsakani.

A bangare guda kuma, matakan kariya ta diflomasiyya na da matukar mahimmanci musamman ganin yadda ake samun karuwar rashin zaman lafiya a yankin yayin da kasashe makwabta ke shiga cikin rikici.

Dukka matakan biyu na matsin lambar diflomasiyya da na kariyar diflomasiya za su iya samar da yanayi na shiga tsakani da kuma hanyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali na tsawon lokaci.

Babi na karshe shi ne sulhu ko shiga tsakani, akwai dai bukatar kasashen Afirka su mika kansu don shiga tsakani a hukumance tare da zama a teburin tattaunawa tsakanin dukkan bangarorin da ke rikici da juna.

An dade da amincewa da matakin yin sulhu a matsayin inda dukkan bangarorin da ake magana akai za su zauna don su samu tattaunawa mai ma'ana, ta hanyar bin ka'idar diflomasiyya.

Fiye da Falasdinawa 14,000 Isra'ila ta kashe tun daga ranar 7 ga watan Oktoba kawo yanzu. Hoto: AA Reuters

Kasashen Afirka da suka taba zama a teburin sulhu bayan rikice-rikice da suka fuskanta za su fi dacewa wajen shiga tsakani tare da goyon bayan kungiyoyin kasashen waje kamar MDD ko kungiyoyin da aka gina su wajen samar da zaman lafiya da tsaro, kamar kwamitin sulhu da tsaro na Tarayyar Afirka.

Idan har aka samu yin hakan, kasashen Afirka za su iya nunawa ga kasashen duniya cewa wannan rikici ya wuce kasashen biyu da abin ya shafa, ko ma yankin - a maimakon hakan, zaman lafiya da yin sulhu su ne muradin samun maslaha ga daukacin al'ummar duniya.

Ajandar zaman lafiya na Afirka na iya zama muhimmiyar gudummawa ga sauya yanayin rikicin da ake ciki da kuma kiyaye tsarin ka'idojin kasashen duniya da ya sanya ayar tambaya akan wannan rikicin.

Yayin da tashe-tashen hankula da Isra'ila ke ci gaba da haifarwa a baya-bayan nan a yankunan Falasdinawa da ta mamaye da kuma hare-haren da take kaiwa ta kasa da sama da kuma ta ruwa a zirin Gaza, a yanzu haka ba tambayar ta ya za a kawo karshen yakin amma mai yasa ba ta zo karshe ba - yanzu ne lokaci aiki.

Marubucin, Aaliyah Vayez, ɗan asalin Afirka ta Kudu kuma kwararre ne kan dangantakar kasa da kasa, sannan mai ba da shawara ne kan harkokin duniya da harkokin gwamnati akasar Birtaniya.

Ya wakilci Afirka ta Kudu a fannin diflomasiyya da ci gaba a matakin kasa da kasashen waje.

TRT Afrika