Duniya
MDD Duniya ta caccaki Isra'ila kan shirin ƙara mamayar Yammacin Kogin Jordan
Al Qassam Brigades ta jaddada amincewarta da yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza bayan Isra'ila ta kwashe kwana 472 yaƙi a yankin inda ta kashe Falasɗinawa aƙalla 46,913 da jikkata 110,750+. A Lebanon, Isra'ila ta kashe mutum 4,068 tun Okotoban 2023.Duniya
Yarjejeniyar tagaita wutar Gaza za ta fara aiki ranar Lahadi 6:30 na safe agogon GMT — Qatar
Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar Gaza inda aka shafe kwanaki 470 ana kisan kiyashi a Gaza, inda aka kashe Falasɗinawa 46,876 da kuma jikkata fiye da 110,642. A Lebanon kuwa Isra'ila ta kashe fiye da mutum 4,068 tun daga Oktobar 2023.Duniya
Isra'ila za ta saki Falasɗinawa 95 a ranar farko ta tsagaita wuta a Gaza
A cewar Hukumar Falasɗinawa mai Kula da Walwalar Waɗanda aka Tsare, yanzu, haka akwai Falasɗinawa 10,400 a gidajen yarin Isra’ila, da suka haɗa da mutanen da aka kama a Gaza lokacin yaƙin da Isra’ila ta shafe watanni 15 tana yi a Gaza.Duniya
Ana sa ran gwamnatin Isra'ila za ta kada kuri'a kan yarjejeniyar Gaza a ranar Alhamis: sanarwa
Yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra'ila take yi a Gaza — wanda a yau ya shiga kwana na 467 — ya kashe Falasɗinawa fiye da 46,645 tare da jikkata mutum 110,012. A Lebanon, Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 4,063 tun watan Oktoban 2023.Duniya
Rahotanni na cewa masu shiga tsakani sun samu ci-gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, amma har yanzu ba a cim ma matsaya ba
Qatar da Amurka da Masar suna wani gagrumin yunƙuri na ganin an cim ma matsaya don dakatar da yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza da kuma sakin ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su kafin Joe Biden ya bar ofis.
Shahararru
Mashahuran makaloli