A halin da ake ciki, Masar da Denmark sun yi kira da a aiwatar da cikakken aikin tsagaita wuta a Gaza. / Hoto: AA

Talata, 11 ga Fabrairu, 2025

1720 GMT — Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya yi barazanar cigaba da yakin Gaza matukar ba a sako fursunonin da ke cikin Gaza ba.

An saka alamar tambaya kan tsagaita wutar yayin da Hamas ke ikirarin Isra’ila ta keta wasu muhimman tanade-tanade, lamarin da ya sa ta dakatar da sakin wasu mutane uku da aka yi garkuwa da su a ranar Asabar.

Shugaban Amurka Donald Trump ya jajircewa Isra’ila ta yi kira da a saki sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, maimakon ukun da aka tsara za a sako su a musayar na gaba.

1519 GMT — Houthi ta shirya kai hari Isra'ila idan yaƙin Gaza ya sake komawa

Houthis na Yemen da ke iko da galibin yammacin Yemen ciki har da babban birnin kasar, a shirye suke su kai hare-hare kan Isra'ila idan har ta koma kai hare-hare a Gaza kuma ba ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ba, in ji shugaban kungiyar Abdulmalik al-Houthi.

'Yan Houthi sun kai hari kan jiragen ruwan Isra'ila da wasu jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya, lamarin da ya dagula hanyoyin sufurin jiragen ruwa a duniya, a wani mataki da suka ce na nuna goyon baya ga Falasdinawa na Gaza a yakin da Isra'ila ta yi da Hamas.

Al-Houthi a wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin ya ce "Hannunmu na kan gaba, kuma a shirye muke mu yi gaggawar kai farmaki kan makiya Isra'ila idan har ta koma kai hare-hare a Gaza."

0715 GMT — Sojojin Isra'ila sun zafafa kai hari a Yammacin Gabar Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun fadada kai farmaki a yankin Jenin da ke arewacin Gabar Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye.

A cewar shaidu, sojojin Isra'ila sun kai farmaki a unguwar gabashin Jenin, inda suka jibge maharba a saman rufin gine-gine, tare da lalata kayayyakin more rayuwa da dukiyoyin jama'a.

Shaidu sun kara da cewa, Jiragen yakin sojin Isra'ila sun lalata motoci da shaguna da dama a unguwar Jenin da ke gabashin kasar.

Sun kuma ce an yi arangama tsakanin sojojin Isra'ila da mayakan Falasdinawa a yankin.

0702 GMT — Hamas ta nemi a mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, ta yi fatali da barazanar da Trump ya yi

Wani babban jami'i a ƙungiyar Hamas ya ce dole ne shugaban Amurka Donald Trump ya tuna cewa hanya ɗaya tilo da za a bi domin mayar da Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su gida ita ce a mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

"Dole ne Trump ya sani cewa akwai yarjejeniyar da ta zama wajibi kowane ɓangare ya mutunta, kuma wannan ce hanya ɗaya tilo da za a iya dawo da fursunoni gida. Barazanar da yake yi ba ta da amfani kuma tana cakuɗa halin da ake ciki," in ji babban jami'in Hamas Sami Abu Zuhri a hira da Reuters.

Trump ya yi barazanar saukar da "babban bala'i" idan ba a saki Isra'ilawa da aka yi garkuwa da su a Gaza ba nan da ranar Asabar mai zuwa.

Ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta ɗage shirnta na sakin mutanen da ta yi garkuwa da su, bayan ta zargi Isra'ila da keta yarjejeniyar tsagaita wuta.

2253 GMT — Trump ya yi barazanar soke yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza idan ba a saki mutanen da aka yi garkuwa da su ba

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce zai soke yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza sannan ya bari "koma mai zai faru ya faru" idan ba a saki Isra'ilawa da sauran mutanen da aka yi garkuwa da su ba daga yanzu zuwa ranar Asabar.

"A ganina, idan ba a saki mutanen da aka yi garkuwa da su ba daga yanzu zuwa ranar Asabar da ƙarfe 12 na rana, zan soke yarjejeniyar sannan na bari duk abin da zai faru ya faru," in ji Trump.

"Muna so a dawo da su. Ina magana ne a ƙashin kaina. Isra'ila tana iya ƙin amincewa da hakan, amma dai ni a ganina, ranar Asabar da ƙarfe 12 na rana, idan ba a sake su ba, za a yi babban bala'i."

Trump ya ce za a yi babban bala'i idan ba a saki mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza ba. / Hoto: AFP

Ƙarin labarai 👇

0231 GMT — Kafofin watsa labaran Saudiyya suna ci gaba da caccakar Netanyahu bisa kalaman da ya yi a kan masarautar

Kafofin watsa labaran Saudiyya sun caccaki Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu bisa kalaman da ya yi a kan masarautar tare da sukar shugaban Amurka Donald Trump saboda shirinsa na ƙwace Gaza da neman tilasta wa Falasɗinawa ficewa daga yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Saudi Press Agency ya shafe kwana na biyu yana wallafa rahotanni da ke ambato wasu ƙungiyoyin ƙasashen duniya da Ƙungiyar Ƙasashen Larabawa da Musulmai suna yin Allah wadai da kalaman Netanyahu.

Through televised reports and posts on X, Kazalika gidan talbijin na Al-Ekhbariya TV ya riƙa watsa rahotanni na talbijin da kuma a shafinsa na X inda ya soki Netanyahu da kuma yin fatali da shirin Trump na korar Falasɗinawa daga yankinsu.

TRT World