Ana yi wa tsohon shugaba Trump zarge-zarge da dama ciki har da na boye takardun sirrin gwamnatin Amurka. Hoto/AA

Zargin da ake yi wa tsohon shugaban Amurka Donald Trump kan sakaci da wasu muhimman takardu a gidansa na Florida ya kara jan hankali kan daya daga cikin tuhume-tuhume da suka yi fice a Ma’aikatar Shari’ar Amurka a tsawon shekaru.

Zargin da gwamnatin tarayyar Amurka ke yi wa Trump na nuni da hatsari mafi muni ga tsohon shugaban kasar, kasa da wata uku bayan da aka tuhume shi da laifuka 34 da suka danganci yin karya kan wasu bayanai na kasuwanci.

Ga wasu daga cikin zarge-zargen, da binciken da lauyoyin masu shigar da kara suka yi da kuma yadda zargin da ake yi wa Trump ya sha bamban da na sauran ‘yan siyasa wadanda ake yi musu irin wannan tuhumar.

Wadanne zarge-zarge ake yi kuma me Trump ke cewa?

Ana tuhumar Trump da zarge-zarge bakwai wadanda ke da alaka da sakaci da takardun sirri na gwamnati, kamar yadda mutum biyu da ke da masaniya kan zargin suka bayyana duk da cewa ba a ba su damar yin magana a bainar jama’a ba.

Lauyan Trump, James Trusty ya shaida wa kafar watsa labarai ta CNN a ranar Alhamis cewa tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban kasar ta hada da zargin rike takardun sirri kan tsaron Amurka da yin kafar ungulu ga tsarin shari’a da bayar da takardun bogi da kuma shirya makirci.

Trump, a manhajar shi ta watsa labarai ta Truth, ya kira ta “BAKAR RANA ga jama’ar Amurka.” A wani bidiyo da ya wallafa, ya ce “Ina da gaskiya kuma za mu tabbatar da hakan sosai da sosai kuma cikin sauri."

Bayan mintuna 20 da sakin labarin, nan take kwamitin yakin neman zaben 2024 na Trump din ya fitar da sanarwar cewa suna bukatar kafa gidauniya ta neman taimakon kudi.

Me zai faru a gaba?

Ma’aikatar Shari’ar Amurka ba ta fito nan take ta tabbatar da batun tuhumar ta Trump ba. Trump ya bayyana cewa an umarce shi ya gurfana a gaban kotu ranar Talata da rana a Miami.

Babu tabbaci ko Trump yana da shirin hallara a gaban kotun da kuma yadda lamarin zai kasance.

A lokacin da alkalin gundumar Manhattan ya tuhume shi kan zargin da ake yi masa a New York, Trump ya mika kansa ga hukumomi kuma an yi shari’ar kofofi a garkame inda suka zauna shi da lauyoyinsa a teburin wadanda ake zargi.

Ta yaya aka soma wannan tuhumar?

Jami’an hukumar da ke kula da bayanan kasa da ajiye su ta tuntubi wakilan Trump a 2021 a bazara bayan sun gano cewa akwai wasu takardu na musamman daga lokacin da yake kan mulki da suka bace daga wurin da suke adana bayanai.

Kamar yadda dokar Amurka kan takardun bayanai na shugaban kasa ta tanada, takardun Fadar White House ana daukar su a matsayin kadarorin gwamnatin Amurka kuma dole a ajiye su.

Wani wakilin Trump ya shaida wa hukumar adana bayanan a Disambar 2021 cewa an gano takardun sirrin a gidan tsohon shugaban da ke Mar-a-Logo.

A Janairun 2022, hukumar ta karbo akwatuna 15 na takardun bayanai daga gidan Shugaba Trump da ke Florida, inda daga baya ya shaida wa Ma’aikatar Shari’ar Amurka cewa suna dauke da bayanai na matukar sirri.

A watan Mayu, hukumar FBI da Ma’aikatar Shari’a sun rubuta wasika inda suka bukaci a kawo sauran takardun bayanan da ke hannun Trump.

Masu bincike, wadanda suka je kai ziyara wurin da takardun suke bayan makonni domin karbar su, an ba su kusan gommai uku ne kawai da kuma wata takarda ta rantsuwa daga lauyoyin Trump da ke nuna cewa an mayar da takardun da suka bace.

Gidan Trump na Mar-a-Lago da ke Florida. Hoto/reuters

Sai dai wannan bayanin sai ya rikide ya zama karya. Domin kuwa bayan an bayar da takardar izinin bincike, jami’an sun koma gidan Trump da ke Mar-a-Logo a Agustan 2022 inda suka kwace sama da akwatuna 33 dauke da takardu 11,000 daga wani daki da wani ofishi, ciki har da wasu takardun sirri guda 100.

A jimlace, kusan takardu 300, wadanda wasun su na matukar sirri ne, aka gano daga wurin Trump tun bayan da ya bar mulki a Janairun 2021.

Ta yaya mai bincike na musamman ya shiga lamarin?

A bara, Babban Antoni Janar na Amurka Merrick Garland ya dauki Jack Smith, wani kwararre da ke bincike kan batun laifukan yaki, inda yake da masaniya kan batutuwan cin hanci domin ya jagoranci bincike kan samun takardun sirrin Amurka a hannun Trump da kuma wani bincike na musamman da ke da alaka da lamarin da ya faru a 6 ga watan Janairu da kuma kokarin kawo matsala ga zaben 2020.

Zaben da aka yi na Smith na da alaka da irin rawar da ya taka wurin bincike kan wani tsohon shugaban Amurka.

Shi kansa Garland, Shugaba Joe Biden ne ya zabe shi.

Ana zabar masu bincike na musamman a shari’o’i na musamman wadanda ma’aikatar shari’a ke ganin jama’a da dama na da ra’ayi kanta da kuma samun wani wanda yake wajen gwamnati domin ya zo ya gudanar da bincike a kai.

Kamar yadda dokar kasar ta bayyana, dole ne mai bincike na musamman ya kasance mutum “mai daraja da mutunci kuma ba ya nuna son rai wurin yanke hukunci,” da kuma “matukar masaniya kan dokar hukunta laifuka da tsare-tsare na ma’aikatar shari’a.”

Shin Biden da tsohon mataimakin shugaban kasa Mike Pence ba su da takardun sirri a hannunsu?

Eh, suna da su, sai dai lamarin ya bambanta matuka da na Trump. Bayan an gano takardun sirri na Biden da kuma na Pence a gidansa na Indiana, lauyoyinsa sun shaida wa hukumomi halin da ake ciki inda suka yi gaggawar shirya yadda za a mayar da kayayyakin.

Haka kuma sun amince da hukumomi su je su yi karin bincike kan takardu. Sai dai babu alamu na ko daya daga cikinsu ya san da zaman takardun kafin aka gano su, haka kuma babu hujja da ta fito fili da ke nuna cewa Biden ko Pence sun yi kokarin boye wasu abubuwa da aka gano.

Hakan yana da muhimmanci domin ma’aikatar shari’ar na duba niyyar mutum kan batun yanke hukunci kan wanda ake zargin.

Shin tuhumar da ake yi wa Trump za ta hana shi takarar shugaban kasa?

A’a, tuhumar da ake yi masa ko kuma kama shi da laifi ba za ta iya hana Trump takarar shugabancin ko cin zaben Amurka ba a zaben 2024.

Kuma kamar yadda shari’ar ta New York ta nuna, zargi kan aikata laifuka na taimaka masa wurin samun kudi a gidauniyarsa.

Gidauniyar tasa ta bayyana cewa ta samu sama da dala miliyan 4 a cikin sa’o’i 25 bayan da aka sanar da tuhumar, inda adadin ya wuce fiye da wanda aka tara bayan da FBI ta kaddamar da bincike a gidan Trump da ke Mar-a-Logo.

AP