An bukaci Hollywood ta nuna yadda ake amfani da bindiga saboda yawan harbe-harbe da ake yi a Amurka

"Ya kamata Hollywood ta nuna yadda ake amfani da bindigogi a shirye-shirye da fina-finanta na talabijin a daidai lokacin da ake yawan fama da tashin hankali sakamokon harbe-harbe da bindiga a Amurka"

Wannan magana na kunshe ne a cikin wani rahoto da cibiyar bincike da tsare-tsaren finai- finai ta Hollywood “USC Annenberg’s Norman Lear Center for Hollywood”, Health and Society ta fitar.

“Gargaɗi mai amfani: Ka'idojin amfani da Bindiga wa Kafofin yada Labarai” ya kunshi bayanai da kididdigar da suka bayyana cewa fiye da shekara 20, makamai na bindigogi su ne sanadin mutuwar kananan yara da matasa a Amurka.

"Idan gidajen talabijin za su iya rungumar nuna yadda za a kare kai daga amfani da bindiga, za mu ga mutane a Amurka sun fi samun kwanciyar hankali wajen tsare bindigoginsu a gida," a cewar Daraktar shirye-shirye ta Cibiyar Norman Lear, Kate Folb a wata zantawa da ta yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters

Folb, wacce ta kwashe shekaru da dama tana nazari kan alakar nishadi da al'umma, ta ce nuna sakon yadda za a iya adana bindiga kawai akan allo zai yi tasiri sosai.

Ka’idojin dai sun fayyace tasirin matsalar bindigogi a Amurka ta hanyar zayyana illoli da tashin hankalin da hakan ke haifawa a tsakanin al’umma da kuma yawan harbe-harbe da shirye-shiryen yara tare da ba da shawarwari don inganta hanyoyin gabartawa ba tare da sadaukar da tsarin ba da labari ba.

Daruruwan furodusoshi da daraktoci da kuma marubuta sun amince

An samar da rahoton ne tare da goyon bayan kungiyar Brady Campaign to Prevent Violence, wanda bayan kisan gillar da aka yi wa wasu yara da malamai a Uvalde da ke jihar Texas, shekara daya da ta wuce, kungiyar ta rubuta wata budaddiyar wasika inda ta dau alwashin nuna hanyoyin samar da kariya daga bindiga ta kan alluna.

Fiye da daraktoci da furodusoshi da kuma marubuta 300 ne suka rattaba hannu kan wannan wasika.

Folb ta ce Cibiyar Lear Norman za ta gabatar tare da gudanar da tarurruka wajen bayyana hoton yadda za a samu kariya daga bindiga kan alluna tare da Hollywood bayan marubutan sun samu matsaya kuma za a bayyana hakan a taron bukukuwan nishadi da aka saba yi.

Cibiyar Nazari ta Norman na yin bincike ne kan zamantakewar al’umma da tattalin arziki da al'adu da kuma tasirin nishadi, kazalika ta nemi shawarwari da dama kan ayyukan gidajen talabijin daga ciki har da shirin "Grey's Anatomy" da "This is us," da "Euphoria."

Mai gabatarwa kuma marubuci wanda ya sha samun lambar yabo, Norman Lear ya yi farin ciki kan samar da ka’idojin da kuma manufar da aka sa a gaba.

"Na yi matukar farin ciki da kuma alfahari kan cewa Cibiyar da ke amsa sunana ita ce ta fitar da wannan rahoto kan samar da kariya daga bindiga da kuma masana'antar nishadi," in ji Lear.

"Yadda za a bayyana tasirin illar bindigogi ga lafiyar al’umma a kan allo zai taimaka wajen nuna yadda yakama a mallaki bindiga."

TRT World