aza na fuskantar matsala a fannin lafiya yayin da tan 170,000 na shara ta taru / Hoto: AA

Litinin, 24 ga Fabrairun 2025

1310 GMT — Hukumomin Falasdinu sun yi gargadi game da matsalar lafiya da muhalli a cikin Gaza yayin da tarin datti ke taruwa yayin da yankin ke ciga da kasancewa cikin takunkumin Isra'ila.

"Birnin Gaza na fuskantar babban bala'i na kiwon lafiya da muhalli saboda tarin sharar da ya kai tan 170,000 a kan tituna da wuraren zubar da shara na wucin gadi," in ji karamar hukumar Gaza a cikin wata sanarwa.

Ta zargi Isra'ila da hana tawagogin kananan hukumomi isa babban wurin zubar da sharar da ke gabashin birnin bayan lalata kashi 80 na injinan karamar hukumar a hare-haren bam da Isra'ila ta kai.

Ƙaramar hukumar ta bayyana cewa kungiyoyinta na jigilar kai sharar da ke kan tituna da wuraren zama zuwa wuraren zubar da shara na wucin gadi a cikin birnin.

0906 GMT –– MDD ta nuna damuwa kan rikicin da ake yi a Gabar Yamma da kiraye-kirayen mamayar yankin

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce "ya yi matuƙar damuwa" kan ta'azzarar rikici a Gabar Yammacin Kogin Jordan da kuma cin zarafin bil'adam a Gaza.

A yayin da Guterres ke jawabi a taron Kwamitin Kare Hakkin Dan'adam karo na 58 a Geneva, ya ce "Na yi matuƙar damuwa da ta'azzarar rikici a Gabar Yammacin Kogin Jordan da Yahudawa 'yan kama wuri zauna suke ingizawa da kuma kiraye-kirayen mamaya."

"A yankin Falasdinawa da aka mamaye, take hakkin bil'adama ya karu" tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023 bayan hare-haren Hamas da "kuma mace-mace da barna da Isra'ila ta jawo a Gaza," in ji shi.

Da yake bayyana tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinu a matsayin "mai hatsari," ya bukaci cewa: "Dole ne ko ta halin ƙaƙa mu guji sake barkewar tashin hankali. Al'ummar Gaza sun sha wahala sosai."

Ya kara da cewa "Lokaci ya yi da za a tsagaita wuta na dindindin, da sakin dukkan sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, da samar da mafita ta ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, da kawo karshen mamayar, da kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, tare da Gaza a matsayin muhimmin bangare."

Ƙarin bayani👇

1021 GMT — Harbe-harben sojin Isra'ila sun tayar da gobara a gidajen Falasdinawa a Rafah

Gidajen Falasɗinawa dama sun kama da wuta bayan da sojojin Isra'ila suka yi harbe-harbe a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, in ji shaidu.

A cewar shaidu, jirage marasa matuƙa da tankokin yaƙi sun buɗe wuta a tsakiyar Rafah, lamarin da ya jawo gidaje da dama suka kama da wuta.

Hakazalika an bayar da rahoton cewa sojojin Isra'ila sun yi luguden wuta a yankunan gabashin birnin Gaza, sai dai ba a samu asarar rai ba.

An kai sabbin hare-haren ne duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da ta musayar fursunoni da aka cimma a Gaza a watan da ya gabata, wacce ta ɗan dakatar da mummunan kisan kiyashin da Isra'ila ke yi inda ta kashe fiye da mutum 48,300 tare da mayar da yankin kufai.

Hukumomin Falasdinawa sun ba da rahoton keta yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila ta yi tun daga ranar 19 ga watan Janairu sama da 350, ciki har da kashe mutane 92 da jikkata wasu 822 a hare-haren Isra’ila.

0745 GMT –– Tankokin yaƙin Isra'ila sun kutsa Gabar Yamma

Tankokin yaƙin Isra'ila sun shiga cikin Gabar Yammacin Kogin Jordan a karon farko cikin gomman shekaru, lamarin da hukumomin Falasdinu suka kira da "mummunan kutse", bayan da ministan tsaro ya ce dakarun za su kasance a wasu sassan yankin har tsawon shekara ɗaya, kuma dubban Falasdinawa ba za su iya komawa can ba.

Wakilan kamfanin dillancin labarai na AP sun ce sun ga tankokin yaƙi da dama suka kutsawa cikin Jenin.

Ministan Tsaron Isra'ila, Israel Katz ya ce shi da Firaminista Benjamin Netanyahu sun ba da umarnin cewa sojoji "su zafafa ayyukansu don kawar da ta'addanci" a dukkan sansanonin 'yan gudun hijira a Gabar Yammacin Kogin Jordan.

TRT World