Kasashen Turkiyya da Jordan da Qatar da Masar sun yi Allah wadai da kutsen da Ministan Tsaron Isra'ila, Itamar Ben-Gvir ya yi a harabar Masallacin Kudus da ke Gabashin birnin Kudus din.
Ministan mai tsattsauran ra'ayi ya kutsa da karfin tuwo cikin wurin da ake yawan samun hatsaniya, da sanyin safiyar Lahadi karkashin kariyar 'yan sandan Isra'ila, karo na biyu kenan da ya yi hakan tun bayan kama aikinsa da gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu a karshen shekarar da ta gabata.
Yayin da ya kutsa kai cikin wurin, Ben-Gvir ya yi ikirarin cewa Isra'ila ce ta mallaki wajen a wani sakon bidiyo da ya nada daga bakin harabar masallacin.
Turkiyya ta yi tur da kakkausar murya kan wannan abu da ministan na Isra'ila ya yi, tana mai kiran hakan da take dokokin kasa da kasa, a wata sanarwa da ta fitar.
Ankara ta yi kira ga Isra'ila da ta yi abin da ya dace tare da kawo karshen duk wani salo na tsokana da ya ci karo da take dokokin kare martabar Masallacin Kudus Mia Daraja da dokokin kasa da kasa suka tanada.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Jordan ta bayyana kutsen da Ben-Gvir ya yi cikin Masallacin Kudus a matsayin "ta da hatsaniya mai hadari".
Wannan "mataki ne na tunzura jama'a da aka yi Allah-wadai da shi, kuma wata babbar barazana ce da ba a yarda da ita ba," in ji kakakin ma'aikatar, Sinan Majali a cikin wata sanarwa da aka fitar.
Ya ce kutsen "ya take hakkin dokar kasa da kasa, da kuma dadadden tarihi da shari'o’i a Birnin Kudus da wurarensa masu tsarki."
Wannan wuri ya bai wa Musulmai damar yin ibada a harabar Masallacin Kudus tare da bai wa mabiya sauran addinai damar kai ziyara wurin.
Majali ya yi gargadi da cewa "Ci gaba da take doka da kuma kai hare-hare kan wurare masu tsarki na mabiya addinin Musulunci da Kiristanci a birnin Kudus, tare da batun fadada matakan sulhu na bai daya kan rikicin mamayen yankuna da ake yi da kuma yawan hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa, duk na iya ci gaba da haifar da tashin hankali."
Ya yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa don kawo karshen irin wadannan ayyuka.
Kakakin ya yi kira ga Isra'ila da ke rike da iko da ta gaggauta dakatar da duk wasu ayyuka na keta haddi a cikin Masallacin Kudus da kuma dukkan matakan da take dauka na sauya matsayin tarihi da shari'a a wurin mai tsarki.
'Hari kan miliyoyin al'ummar Musulmai'
Ita ma Qatar ta bi sahu wajen yin Allah-wadai da kutsen da ministan na Isra'ila ya kai wurin mai tsarki.
"Yunkurin cutar da addini da dadadden wajen ibada na Masallacin Kudus ba wai hari ne kan Falasdinawa kadai ba, har ma da miliyoyin Musulman duniya," a cewar sanarwar da Ma'aikatar Harkokin wajen Qatar ta fitar.
Sanarwar ta bayyana Isra'ila "da alhakin" duk wani tashin hankali da ya barke sakamakon yawan cin zarafi da kutsawa cikin Masallacin Kudus mai albarka da kuma tsananta dokoki kan al'ummar Falasdinawa da kasarsu da kuma addininsu na Musulunci da na Kiristanci."
Damuwar Amurka kan matakin 'mai tayar da hankali'
Amurka ta ce ta damu da ziyarar tsokana da Ministan Tsaron Isra'ila mai tsautsaran ra'ayi ya kai Masallacin Kudus.
“Bai kamata a yi amfani da wannan wuri mai tsarki don ayyukan siyasa ba, kuma muna kira ga dukkan bangarorin da su mutunta addinansu,” a cewar mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Matthew Miller a wata sanarwa da ya fitar.
Kutse cikin Masallacin da Ben-Gvir ya din na zuwa ne kwana uku bayan da shi da dubban Yahudawa masu tsattsauran ra'ayin kishin kasa suka yi wani tattaki a tsohuwar birnin.