Limamai da manyan malaman Musulunci sun fitar da sanarwar hadin gwiwa kan auren jinsi inda suke bayyana cewa ana kulla alakar tara wa da juna kawai ta hanyar aure, kuma tsakanin mace da namiji.
Sanarwar da aka fitar a ranar 23 ga Mayu mai taken "Bayyana Bambance-Bambance: Fayyace Dokokin Zaman Jinsi da Tarayya a Musulunci", na da manufar bayyana matsayin Musulunci kan "sharuddan kulla auratayya.
"Yayin da kuma "ake bayyana nauyin da ke kanmu na zama lafiya da wadanda addinansu suka bambanta da namu."
Ilimi da Hikimar Ubangiji
Sanarwar ta haskaka manyan rukunan Musulunci, wanda su ne mika wuya ga Allah sannan a san ilimi da hikimarSa.
Ta jaddada cewa ta hanyar addinan da aka saukar daga sama ne ake samun halayya ta gari, kamar yadda yake bayyane karara a Alkur'ani Mai tsarki da koyarwar Annabi Muhammad.
Malaman sun sake tabbatar da wadannan sharudda:
"Ta hanyar mika wuya ga Allah, muna bayyana cewa Shi kadai ne ya mallaki dukkan Ilimi da hikima. A saboda haka, daga wannan mika wuya za a fahimci yadda ta hanyar shiriyar da ta sauka daga sama ne kadai ake samun dabi'u na gari, ba wai daga tunani ko abubuwan da ke tashe a zamantakewa ba."
Aure
Malaman sun bayyana cewa Musulunci ya halasta a yi saduwa tsakanin mace da namiji ta hanyar aure kadai, kuma hakan zai faru ne tsakanin mace da namiji kadai.
Alkur'ani Mai Tsarki ya la'anci alakar saduwa tsakanin jinsi guda, kuma ya haramta duk wata alaka ta tara wa kafin aure ko kuma ba tare da wanda aka kulla aure da shi ba. Wadannan sharudda sun samu amincewa ga dukkan al'ummar Musulmai.
"Ta hanyar doka daga Ubangiji, ana kulla alakar saduwa ne kawai bayan an daura aure, kuma auren tsakanin mace da namiji kawai ake kulla shi."
'Yan adam sun hada da mata da maza
Game da jinsi, Malamai da Limaman sun jaddada cewa Musulunci ya bayyana 'yan adam a matsayin mace da namiji, wadanda suke da matsayi guda a gaban mahaliccinsu.
A lokacin da mata da maza suke da siffofin halitta da rawar da suke takawa daban da juna, Malaman sun jaddada cewar kwaikwayon kamannin jinsin da ba naka ba, haramun ne a Musulunci.
Sun yi kira ga Musulmai da su girmam hikimar Allah da ya yi halitta.
"Allah Ya bayyana 'yan adam maza da mata sannan ya bayyana cewa 'Ya halicci ('yan adam) daga mace da namiji sannan ya sanya su suka zama a kabilu da al'ummu ta yadda za ku zo ku san juna.' "(Quran, al-Ḥujurāt: 13; ku duba kuma al-Najm: 45)."
Ayyuka da ji na jiki
Sanarwar ta kuma bambance tsakanin ji da jiki, motsi da siffantuwa a Musulunci.
A lokacin da daidaikun mutane suke da alhakin kalamai da ayyukansu a Musulunci, Addinin Musulunci ba ya kama su da kuskure da ji da jikin da suka yi.
Malaman sun kuma bayar da muhimmanci wajen cewa ayyukan sabo na mutum ba za su bayyana ko shi waye ba.
Sun ce an haramta Musulmi ya dinga alfahari da kamanta kansa da siffofi na zunubin yake aikatawa.
"Musulunci ya rarrabe tsakanin ji da jiki, ayyuka da siffantuwa. A lokacin da daidaikun mutane suke da alhakin kalamai da ayyukansu a Musulunci, Addinin Musulunci ba ya kama su da kuskure da ji da jikin da suka yi," in ji sanarwar.
Hakki a kundin tsarin mulki na yin addini
A lokacin da ake ta muhawara tsakanin jama'a tare da rashin fahimta, malaman sun zayyana cewa, nuna kin amincewa da masu ra'ayin LGBTQ, ba ya nufin kin aminta da wani mutum.
Sun tabbatar da gwagwarmayar da suke yi don samun zaman lafiya, tare da amincewa da hakkin da kundin tsarin mulki ya bai wa kowa.
Sun kuma fayyace cewa zama lafiya da juna ba ya farlanta sai mun yarda da juna, da aminta da tabbatarwa da habaka ko bukin wata dabi'a ta wani daban.
Mun yi watsi da zabi mara kyau tsakanin amincewa da matsin lambar al'umma don karbar ra'ayin da ya saba wa addininmu, ko fuskantar tuhumar ci da addini."
Kira ga mahukunta
Haka zalika, sanarwar ta yi kira ga mahukunta da su yi aiki tare da kare hakkin mutane da ke kundin tsarin mulki na kowa ya yi addinin da yake so ba tare da nuna kyama da kyara ba.
Ta bukaci mahukunta da su kalubalanci duk wata doka da za ta ci karo da wadannan hakkoki, da za ta bayar da gudunmowa ga yanayin kin amincewa da mabiya addinin da ba naka ba.
"Muna kira ga mahukunta da su kare hakkokin da kundin tsarin mulki ya ba mu na gudanar da addininmu cikin 'yanci, ba tare da tsoro ko hantara ba, kuma su kalubalanci duk wata doka da za ta tauye hakkokin al'ummun da suke bin wani addini."
Sako ga Musulmai masu fafutuka
A karshen sanarwar, malaman sun mika sakon tausayi da fahimta ga Musulmai wadanda watakila suna gwagwarmaya tare da bukatun da suke ba na Musuluncin ba.
Sun tunatar da mutane game da batun tuba wa Allah da neman gafara, suna kiran su da su bayar da fifiko ga bautar Allah sama da bukatunsu, sannan su zama masu kame kawunansu.
"Ga wadanda suke tare da mu kuma suke gwagwarmarmaya da bukatun da suka keta haddin dokokin Allah: su sani cewa ko wanda ya fi kowa aikata daidai yana kuskure kuma kowanne Musulmi, duk sabonsa, yana da damar a gafarta masa."
Tare da wannan sanarwa, manyan Limamai da Malamai sun yi kokarin fayyace matsayi da dokokin musulinci game da sharuddan saduwa da jinsi, a yayin da kuma suke kira ga zama lafiya da juna tare da girmama addinai daban-daban da kuma hakkokin da kundin tsarin mulki ya bai wa mutane.
Hadaddiyar muryarsu ta zama wata shiriya ga Musulmai da suke fama da wannan batu a duniyar nan ta yau da ke sauyawa cikin sauri.