Shugaba Joe Biden na Amurka da ‘yan jam’iyyar Republican a majalisar dokoki sun cimma matsaya kan kara yawan bashin da gwamnati za ta iya ci don kawar da fadawa mummunan yanayi.
Ga wasu bayanai da kamfanin dillancin labarai na AFP ya tattara game da yarjejeniyar, wadda ke bukatar amincewar majalisar dokokin da kanta ya rarrabu.
Shin akwai bangaren da ya yi nasara?
Bayan kwanaki ana tattaunawa mai zafi, yarjejeniyar ta bai wa kowanne bangare ikirarin samun nasara.
Biden ya kira yarjejeniyar ‘Sarayar da hakki’ inda Shugaban majalisar da ‘Republican ke da rinjaye, Kevin McCarthy ya kira ta da “Abin da al'ummar Amurka suka cancanci samu”.
A daren Lahadin da ta gabata aka fitar da shafi 99 na yarjejeniyar kuma za a amince da ita bayan muhawarar da za a yi a kwanaki masu zuwa.
Ba a amince da wasu bukatu daga kowanne bangare ba, kamar bukatar da ‘yan Democrat suka mika ta janye wasu kura-kuran ka’idojin ci da biyan basussuka, da kuma kawar da dokar harajin makamashi mai tsafta da ‘yan Republican suka nema a yi.
Matsayin yarjejeniyar
A baya ana kiran ta Dokar Kasafin Kudi ta 2023, kuma ta nemi da a kara yawan bashin da Amurka za ta iya ci a shekara biyu zuwa dala tiriliyan 31.4. Hakan na nufin Biden ba zai bukaci sake tattaunawa da majalisar ba kafin zaben watan Nuwamban 2024 ba.
Yarjejeniyar ta kuma takaita yanke kudade da kashe-kashen kudaden gwamnatin tarayya wanda zai dadadawa ‘yan Republican, amma ba ta amince da yanke kudaden da yawa ba wanda masu ra’ayin rikau suka so ba, kuma wanda ‘yan Democrat masu rajin kawo cigaba za su iya amincewa.
Kashe kudade
Yarjejeniyar ta amince da kashe kudaden da ba na sojoji ba a matsayin bai daya a 2024. Ta kuma takaita karin kaso 1 a shekarar 2025, kamar yadda kudirin dokar ya tanada.
Yarjejeniyar ta kuma kebe shirye-shiryen gwamnatin Biden na kara yawan kudaden sojoji da ‘yan mazan jiya duba da hauhawar farashi.
Karbar Haraji
Yarjejeniyar ta kuma tanadi ka’idojin fadada kudaden da ake tattarawa na haraji a cikin gida.
A shekarar da ta gabata, Majalisar dokokin Amurka ta amince da dala biliyan 80 don habaka Ayyukan Harajin Cikin Gida.
Yarjejeniyar adadin bashin da za a ci ta yanke dal biliyan goma 10 da za a kashe a wasu bangarorin.
Kudaden Covid da ba a kashe ba
Yarjejeniyar ta kuma bukaci kwashe wasu kudade da majalisar dokokin ta ware lokacin annobar Corona amma kuma ba a yi amfani da su ba.
Sanarwar da ofishin Mccarthy ta fitar ta bayyana cewa yarjejeniyar za ta karbe biliyoyin da ba a kasha ba na Corona, amma ba a bayyana a ina za a kashe kudaden ba.
Babu wasu sauye-sauye da za a yi ga tallafin kula da lafiya, shirin gwamnati na inshorar lafiya da yake taimaka wa ‘yan Amurka marasa galihu.
Ka’idojin gudanar da aikin
Yarjejeniyar ta tanadi ka’idojin gudanar da aiyuka ga mutanen da suke karbar tallafin abinci ko walwalar iyali, wata nasara ce ta bangaren Republican.
An shirya kawar da yawan shekarun manyan mutanen da ba su da yara kafin su samu damar karbar tallafin abincin daga shekara 49 zuwa 54.
Bayan mika bukatar ‘yan Democrat, an tsame ‘yan mazan jiya da wadanda ba su da matsuguni daga wannan ka’ida.