Wani tsohon dan fursuna Bafalasdine, wanda aka sake shi a wani bangare na musayar fursunoni na shida, ya samu tarba daga 'yan'uwa yayin da ya isa asibitin European da ke Khan Younis a kudancin Gaza a makon jiya. / Hoto: AFP

Juma'a, 21 ga watan Fabrairun 2025

1300 GMT — Isra’ila za ta saki fursunonin Falasdinu 602 a ranar Asabar, ciki har da Falasdinawa 50 da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai da kuma wasu 60 da aka yanke musu hukuncin zama na tsawon shekaru a gidan yari, kamar yadda ofishin yada labaran gidajen yarin Falasdinu ya bayyana.

Sakin wani muhimmin bangare ne a kashi na farko na yarjejeniyar musaya, wanda ya biyo bayan mika sunayen wasu ‘yan Isra’ila 6 da bangarorin Falasdinawan suka yi garkuwa da su a ranar Asabar.

A cikin wata sanarwa da ofishin yada labaran ya fitar, ya tabbatar da cewa, baya ga Falasdinawa 50 da aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai, da 60 da aka yanke musu hukunci mai tsauri, za a kuma saki Falasdinawa 47 daga yarjejeniyar Shalit ta 2011, wadanda aka sake kama su.

Bugu da kari, ana shirin sakin Falasdinawa 445 na Gaza wadanda aka tsare bayan harin 7 ga Oktoban 2023.

1144 GMT — Hamas ta yi watsi da barazanar Netanyahu kan gawar Shiri Bibas

Hamas ta yi watsi da "barazanar" da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi na cewa sai kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta gani, bayan da ya zarge ta da keta yarjejeniyar tsagaita wuta ta hanyar ƙin mayar da Shiri Bibas da aka yi garkuwa da ita.

A cikin wata sanarwa da kungiyar Hamas ta fitar ta ce "Mun yi watsi da barazanar da Benjamin Netanyahu ya yi a matsayin wani bangare na kokarinsa na inganta martabarsa," in ji kungiyar Hamas da ta yi kira ga mahukuntan Isra'ila da su mayar da gawar Bafalasdiniyar da kungiyar ta miƙa a ranar Alhamis, a zaton cewa ta Bibas ce.

1005 GMT — Ga alama gawar Shiri Bibas ta cakuɗe da gawawwakin wasu mutanen daban — Hamas

Wani jami’in Hamas ya shaida wa AFP cewa mai yiwuwa gawar Shiri Bibas da aka yi garkuwa da ita ta “cakuɗe a bisa kuskure” da gawawwakin wasu da ke ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine a Gaza bayan kashe su da aka yi.

"Watakila bisa kuskure gawar Misis Bibas ta cakuɗe da gawawwakin wasu da aka gano a karkashin baraguzan gini," in ji jami'in da ya nemi a sakaya sunansa, inda ya kara da cewa kungiyar na "bincike" lamarin.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da Isra’ila ta yi cewa daya daga cikin gawawwakin da Hamas ta miƙa mata a ranar Alhamis ba ta Bibas ba ce kamar yadda Hamas ɗin ta faɗa.

Ƙarin labarai 👇

1054 GMT — Hamas ta saki sunayen Isra'ilawan da za ta sake a ranar Asabar

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta sanar da sunayen ‘yan Isra’ila shida da take garkuwa da su waɗanda za ta sake a ranar Asabar a mataki na 7 na yarjejeniyar musaya da Isra’ila.

1054 GMT — Jami'in Gaza ya ce sau fiye 350 Isra'ila na take yarjejeniyar tsagaita wuta

Shugaban ofishin yada labarai na gwamnati a Gaza ya sanar da cewa sau fiyesama da 350 Isra'ila ta keta yarjejeniyar tsagaita da Isra'ila ta cim ma a ranar 15 ga watan Janairu.

A cikin wata sanarwa da Isma'il al-Thawabteh ya fitar ya ce: ya ce "Fiye da sau 350 Isra'ila ta saɓa wa yarjejeniyar tsagaita wuta tun lokacin da aka rattaba hannu kan yarjejeniyar, wanda hakan ke nuna ƙarara tana ci gaba da saba alkawuran da ake yi da ita da kuma bijire wa kasashen duniya.

Tun bayan sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta, sojojin Isra'ila sun kashe tare da raunata Falasdinawa da dama ta hanyar hare-hare ta sama da suka hada da jiragen yaki da jirage marasa matuka, da harbe-harbe kai tsaye.

Sauran laifukan sun hada da kutsen da Isra'ila ta yi a yankunan kan iyaka da ke gabashin Gaza.

TRT World