Jakadan Amurka a Isra'ila Thomas Nides ya ce gwamnatin kasarsa na kokarin daidaita alaka tsakanin Isra'ila da Saudiyya.
A wata hira da ya yi da tashar yada labaran Isra'ila i24, Nides ya ce gwamnatin Biden na kokarin fadada yarjejeniyar Abraham tsakanin Isra'ila da kasashen yankin Larabawa.
A watan Satumba na 2020, Amurka ta shiga tsakani a yarjejeniyar Abraham da ta share fagen kulla alaka da kasashen Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Morocco da kuma Sudan.
"Ina aiki a kowace rana tare da 'yan Bahrain da ‘yan Moroko da ‘yan Hadaddiyar Daular Larabawa da ‘yan Masar da Jodan kan hanyoyin inganta alaka da Isra'ila," in ji Nides.
Ya kara da cewa "Muna son ganin an daidaita tsakanin Saudiyya da Isra'ila, muna ganin yana da matukar muhimmanci, kuma muna aiki tare da Isra'ila don cimma hakan."
Ya zuwa yanzu babu wani martani ko bayani daga mahukuntan Saudiyya kan kalaman jami'in diflomasiyyar na Amurka.
Yarjejeniyar Abraham
A ranar Litinin wata cibiyar bincike da ke nazari kan ayyukan Isra'ila a Amurka ta ‘’Washington Institute for Near East Policy’’, ta ce sakamakon binciken jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan ya nuna cewa kashi 40 cikin 100 na Saudiyya ne ke goyon bayan dangantakarsu da Isra'ila.
Binciken ya kara da cewa kashi 20 cikin 100 na 'yan kasar Saudiyya ne kawai ke kallon yarjejeniyar Abraham a matsayin "kyakkyawan sakamako ga yankin Gabas ta Tsakiya".
Saudiyya dai ba ta da wata huldar diflomasiyya da Isra'ila sannan tana adawa kan daidaita al'amura da ke tsakani kasashen biyun har sai gwamnatin Isra’ila ta kawo karshen mamayar yankunan Falasdinawa da aka kwashe tsawon shekaru ana yi.
Masar da Jordan su ne kasashen Larabawa na farko da suka kulla huldar diflomasiyya da Isra’ila a shekarar 1979 da 1994.
A 2020 an samu karin wasu kasashe hudu da suka bi sahu wajen kulla hulda da isra’ila bayan sanarwar yarjejeniyar Abraham, kasashen kuwa sun hada da kasar Morocco da Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da kuma Sudan.