Wasu manyan likitocin fida a Saudiyya sun yi nasarar raba wasu ‘yan-biyu ‘yan Nijeriya da aka haifa a manne da juna.
Mai magana da yawun Shugaba Buhari na Nijeriya Malam Garba Shehu wanda ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter ranar Juma’a ya ce “Alhamdulillahi an kammala tiyatar raba ‘yan-biyun da ke manne da juna cikin nasara.”
Dama tun a ranar Alhamis Malam Garba Shehu ya fara wallafa batun yi wa Hassana da Hussaina tiyata a Asibitin Kwararu na Sarki Abdulaziz da ke Riyadh, babban birnin Saudiyyan.
"An shafe awa 14 ana gudanar da gagarumin aikin raba ‘yan-biyun," in ji mai taimaka wa shugaban Nijeriyar kan watsa labarai.
Yaran, wadanda aka haifa a watan Janairun 2022 a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, sun hade ne ta ciki da kugu da hanta da hanji da mafitsararsu.
Daga nan ne aka mayar da su Babban Asibitin Kasa da ke Abuja inda suka shafe kusan wata takwas ba tare da an yi musu tiyata ba saboda rashin kudi, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.
A sanarwarsa ta farko, Malam Garba Shehu ya ce a ranar 9 ga watan Nuwamba ne aka tafi da yaran da iyayensu birnin Riyadh a bisa umarnin Sarkin Saudiyya Salman.
Masauratar Saudiyyan ce ta dauki nauyin komai na aikin, kamar yadda Malam Garba ya ce.
Tawagar likitocin da ta yi aikin
Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya SPA ya ce an gudanar da tiyatar ne a mataki takwas karkashin jagorancin wata tawagar kwararrun likitocin fida 36 da kuma mambobin tawagar ma’aikatan lafiya ta musamman da ke sa ido kan aikin 85.
Shugaban tawagar Dr. Abdullah Al-Rabeeah ya bayyana cewa an yi tiyatar ne a karkashin umarnin gwamnatin Saudiyya.
Wannan shi ne karo na 56 da ake irin wannan tiyata a karkashin wani shiri na Saudiyya n araba ‘yan-biyun da ake haifa manne da juna, in ji babban likitan.
Shiirin na Saudiyya ya samu nasarar aiwatar da irin wannan aiki sau 130 daga kasashe 23 a cikin shekara 33 da suka wuce, yana mai jaddada muhimmancin da gwamnatin Saudiyya ke bai wa ayyukan jin-kai a fannin lafiya.