Abu biyar da suka kamata ku sani kan AIkin Hajjin 2023

Abu biyar da suka kamata ku sani kan AIkin Hajjin 2023

An yi amannar cewa Hajjin bana na daga cikin manya da aka taba yi a tarihi.
An yi amannar cewa Hajjin bana na daga cikin manya da aka taba yi a tarihi. / Photo: AP

Za a iya cewa kusan duk wani Musulmi a fadin duniya zai yi fatan a ce a yanzu haka yana cikin miliyoyin da za su gudanar da aikin Hajjin 2023.

An yi amannar cewa Hajjin bana na daga cikin manya da aka taba yi a tarihi.

Ga wasu abu biyar da ya kamata mu sani game da Aikin Hajjin 2023.

Na farko

Aikin hajjin bana zai kasance mafi girma a tarihi kamar yadda Ministan Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya, Tawfiq al Rabiah ya bayyana.

Rahotanni sun ce mahajjata fiye da miliyan biyu da rabi ne ke sauke farali a bana, daga kasashe 160 na duniya.

Tun shekarar 2019 ba a sake aikin Hajjin da ya kai na bana girma ba, inda mutum miliyan 2.5 suka halarta a lokacin.

Wani jami'i a Ma'aikatar Hajji da Umarar ya ce "A bana, za a gudanar da aikin Hajji mafi girma atarihi, idan har abubuwa suka tafi yadda muke so.

"Yawan mahajjatan zai zarce miliyan 2.5," in ji jami'in wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda ba a ba shi damar magana da kafafen watsa labarai ba.

Na biyu

Kafin annobar cutar korona, kudin karamar kujerar Hajji bai wuce naira miliyan 1.5 ba, amma a bana, sai kana da a kalla miliyan uku kafin ka samu damar sauke faralin.

A wasu kasashen kuwa, a kalla dala 5,000 ce za ta ishi kowane mutum daya gudanar da aikin hajji.

Kasar Saudiyya tana samun biliyoyin daloli a duk shekara a dalilin Aikin Hajji.

Alal misali ko a bangaren samun kudaden shiga kasar na samun makuden kudade.

Wani dan kasuwa a Saudiyyan Samir al-Zafni ya ce dukkan otel-otel din da suke Makka da Madina sun cika makil har zuwa satin farko na watan Yuli.

"A bana babu wani daki da ya saura da ba a dauke shi ba a otel dinmu 67 da muke da su," ya ce.

Na uku

Rikicin da ake yi na Sudan ya yi tasiri matuka ga aikin hajjin bana, wanda ya sa jirage musamman wadanda suka taso daga Nijeriya da wasu kasashe ba su iya bi ta sararin samaniyar Sudan, sai dai su sauya hanya.

Hakan ya ja tafiya Saudiyya daga Nijeriya ya zama awa bakwai a maimakon awa hudu saboda sai an yi zagaye.

A da daga Nijeriya, sai jiragen su bi ta sararin samaniyar Chadi sai kuma Sudan, sannan su tsallaka Bahar Maliya su shiga birnin Jiddah.

Na hudu

Wannan ne karo na farko da za a gudanar da Aikin Hajji gadan-gadan tun bayan annobar korona.

A shekarar 2020, mutum 10,000 ne kawai suka gudanar da AIkin Hajji, saboda tsananin yaduwar da cutar korona ta ke yi a lokacin.

A 2021 kuwa mutum 59,000 ne suka yi, sai kuma a 2022 da mutum miliyan daya suka gudanar.

Abin murnar shi ne yadda aka kawar da dokokin takaitawar a wannan shekara ta 2023.

Na biyar

Ana gudanar da Aikin Hajjin a daidai lokacin da ake tsananin zafi inda ake hasashen tsananin zafin zai iya kaiwa maki 45 a ma’aunin salshiyas.

Amma duk da wannan tsananin zafi da ake fuskanta, alhazan na cikin farin cikin samun damar gudanar da wannan ibada ne.

"Ina cikin ranaku mafiya kyau da na taba gani a rayuwata," in ji Saeed Abdel Azim, wani mahajjaci mai shekara 65 dan kasar Masar.

"Mafarkina ya zama gaskiya," a cewar mutumin wanda ya shafe shekara 20 yana tara kudin zuwa hajjin.

TRT Afrika da abokan hulda