Mutanen da ke cikin jerin wadanda aka sanya wa ido suna fuskantar kalubale iri-iri. Hoto: AA

Wani rahoto da kungiyar Musulmai a Amurka CAIR ta fitar ya bayyana cewa mafi yawan mutanen da ke cikin jerin wadanda hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta sanya wa ido sunayen Musulmai ne.

Rahoton wanda aka yi wa take da "Shekaru Ashirin sun yi Yawa, kira kan neman a dakatar da ayyukan sa ido na hukumar FBI," ya yi cikakken bayani game da yadda hukumar ke amfani da bayanan tantance ayyukan ta'addanci, da ya ce ana kai hari kan Musulmai.

Kungiyar kula da dangantakar Amurka da al’ummar Musulmai CAIR ce ta fitar da rahoton a ranar Litinin.

Bayan wani dan kasar Switzerland da ke kai kutse ta yanar gizo ya gano irin wannan shigar ta intanet sakamokon wallafa shi da aka yi na baza ta a wani jirgin sama na kasar, kungiyar CAIR ta gudanar da cikakken bincike sama da mutane miliyan 1.5 da aka samu.

"Sama da sunaye 350,000 da aka shigar cikin jerin wadanda aka sanya wa ido, sun hada fassarar sunan Mohamed ko Ali ko Mahmoud sai wasu karin sunaye 50 da suka fi bayyana, wadanda duk sunayen Musulmai ne.

Daga cikin jerin sunayen da muka yi bitarsu, mun kiyasta cewa fiye da mutum miliyan 1.47 da aka shigar sun fi shafar Musulmai ne – a jumlace, fiye da kashi 98 cikin 100 kenan," a cewar rahoton.

Rahoton ya yi nuni da cewa a tsawon shekara 20, jerin sunayen da hukumar FBI ta fitar ya sanya al’ummar Musulmai cikin mawuyacin yanayi.

"Sai dai a nan gaba miliyoyin sunayen da FBI za ta fitar ba za su kasance Musulmai ba. Duba da irin ayyukan ta'addanci da ke dada karuwa, wata rana hukumar za ta gano wasu sabbin mutane.

"Kuma a nan gaba mutanen za su kasance 'yan uwanmu Amurkawa ne, wannan rahoto na zaman gargadi ne a gare su,” in ji rahoton.

Kungiyar Musulman ta kuma yi kira ga Shugaba Joe Biden da ya dauki mataki kan wannan al’amari.

Mutanen da ke cikin jerin sunayen suna fuskantar kalubale iri-iri, gami da kayyade tafiye-tafiyensu da batutuwan da suka shafi shige da ficensu da tashin hankali a gamuwarsu da 'yan sanda da kuma sanya musu iyaka wajen shiga gine-ginen gwamnati da dai sauransu.

A wani lamari da ya faru a baya-bayan nan, an ga yadda Hukumar Binciken Sirri ta Fadar White House ta hana Magajin Garin Prospect Park na New Jersey, Mohamed Khairullah shiga wajen bikin karamar sallah da aka shirya a fadar.

An danganta hana shi shigar da aka yi da cewa sunansa yana cikin jerin mutanen da hukumar FBI ta sanya wa ido.

TRT World