Hukomomi a kasar Saudiyya sun ce Alhazan duniya sun sauka lafiya daga Arafa bayan shafe tsawon yini suna gudanar da ibadu da addu'o'i a ranar Talata.
Tuni alhazan suka kama hanyar Muzdalifa inda a can ake so su hada sallolin magariba da isha'i, sannan su yada zango har zuwa asuba inda za su kama hanyar tafiya wajen jifan Shaidan.

Ana so mahajjata su tsinci duwatsun da za su yi jifa da su a wajen. Sannan an yi wa marasa lafiya da tsofaffi rangwame inda za su iya wucewa wajen jifa a cikin daren ba tare da kwana a Muzdalifa ba, a cewar malamai.
Ministan Aikin Hajji da Umara na Saudiyya Dr. Tawfiq Al-Rabiah a ranar Talata ya ce alhazai 1,845,045 daga kasashen 150 ne suka yi tsayuwar Arafan.

Kamfanin dillancin labarai na Saudiyya ya ambato ministan yana cewa an yi jigilar alhazai zuwa Arafa an kumma kammala lafiya.

Jaridar Saudi Gazette ta ruwaito Hukumar Kididdiga ta Kasar na cewa alhazai daga kasashen Larabawa su ne mafi yawa a bana, inda suka kai 346,214, wato kashi 21 cikin 100.

Sai kuma alhazan kasashen Afirka ban da na Larabawa da ke nahiyar, da yawansu ya kai 221,863, kashi 13.4 cikin 100.

Mahajjatan yankunan Turai da Amurka da Australiya da sauran kasashen da ba a ba su rukuni ba sun kai 36,521, wato kashi 2.1 cikin 100.
