On upcoming talks between US President Donald Trump and his Russian counterpart Vladimir Putin on a potential end to the war in Ukraine, Erdogan said he hoped the meeting paves the way to a "positive outcome." / Photo: Reuters Archive

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana amincewa da aka yi da ƙaurar Yahudawa daga yankunansu a matsayin abin da ba a amince da shi ba baki ɗaya, inda yake martani kan kalaman Shugaban Amurka Donald Trump.

"Muna sa rai Trump zai cika alƙawarin da ya ɗauka kafin zaɓe. Ya kamata ya ɗauki matakai domin samar da zaman lafiya ba fara yaƙi ba," kamar yadda Erdogan ya shaida wa manema labarai a ranar Juma'a a cikin jirginsa a lokacin da yake dawowa daga Islamabad, bayan ya kammala wani rangadi a ƙasashe uku a yankin Asia.

"Gaza rauni ce a cikin zukatanmu. Muna aiki ba ƙaƙƙautawa domin sauƙaƙa wannan raunin da kuma magance shi. Abin takaici, har yanzu ƙasashen Musulmi sun ƙi haɗa kai su ɗauki matakin da ya dace kan lamarin."

Haka kuma Erdogan ya kuma yi magana dangane da irin tasirin da Yahudawa masu tsatsauran ra'ayi ke da shi a kan tsare-tsare harkokin wajen Amurka, inda ya yi gargaɗin, "Ɗaukar ƙarairayin Yahudawa da kuma yin katsalandan ga al'amuran wannan yanki ba zai haifar da komai ba face zurfafa raunukan da ake da su. Wannan ba tafarki ne mai kyau."

Matsayarsa kan yaƙi da ta'addanci

A game da Syria, Erdogan ya jaddada muhimmancin ikon mallakar yankuna, yana mai cewa, "Domin tabbatar da hadin kai da kwanciyar hankali, yana da muhimmanci ga gwamnati ta mallaki dukkan kasar."

Har ila yau, ya jaddada matsayar Turkiyya kan kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin: "Ba mu bar kungiyoyin da ke barazana ga kasarmu samun mafaka ko damar tsira a arewacin Syria ba, kuma ba za mu taba ba."

"Dole ne su fahimci cewa ba su da wuri a nan. Idan ba haka ba, ba za mu ji tsoron ɗaukar mataki don bayyana musu wannan gaskiyar ba."

TRT World
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince