Sojojin Isra'ila na ci gaba da cin zarafi da kashe Falasɗinawa duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimmawa. / Hoto: Reuters

Lahadi, 16 ga Fabrairun 2025

0152 GMT — Sojojin Isra'ila sun sace yara biyu Falasɗinawa a Yammacin Kogin Jordan

Sojojin Isra'ila sun yi garkuwa da wasu yara biyu Falasɗinawa a lokacin da suka kai samame a wurare daban-daban a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ilar ta mamaye, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Falasɗinu na WAFA ya bayyana.

An tsare Ubade Gassan Azim da kuma Zayd Nur Ferhat a samamen da sojojin Isra'ila suka kai a wani ƙauye da ke Nablus.

Haka kuma sojojin na Isra'ila sun yi amfani da bama-bamai masu ƙara da hayaƙi mai sa hawaye a lokacin da suka kai samame a kusa da birnin Hebron.

Asabar, 15 ga Fabrairun 2025

1123 GMT — Isra'ila ta fara sakin fursunoin Falasɗinawa

Isra'ila ta fara sakin fursunonin Falasdinawa 369 da fursunoni, ciki har da 36 da aka yanke musu hukuncin daurin rai da rai.

Wata motar ƙirar bas da ke ɗauke da fursunoni na farko da aka sako ta isa birnin Beitunia da ke Yammacin Kogin Jordan, inda suka samu tarba daga ɗumbin 'yan uwa da magoya bayan.

An ga alamun rashin lafiya a tattare da wasunsu, kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce nan da nan an tafi da huɗu domin duba lafiyarsu.

0809 GMT —Kungiyar Hamas ta sako wasu ‘yan Isra’ila uku ƙarƙashin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas ta miƙa mutanen Isra'ila uku da take tsare da su ga kungiyar agaji ta Red Cross waɗanda suka haɗa da Yair Horn, Sagui Dekel-Chen da Alexander Troufanov.

0741 GMT — Motocin Red Cross sun isa wurin musayar fursunoni

Motocin kungiyar agaji ta Red Cross sun isa wurin da za a yi musayar fursunoni a Khan Younis na Gaza, kamar yadda wani bidiyo ya nuna.

Hamas na shirin mika wa kungiyar agaji ta Red Cross, Yair Horn, Sagui Dekel-Chen da kuma Alexabder Troufanov wadanda Isra'ila ta yi garkuwa da su, bayan kokarin shiga tsakani da Masar da Qatar suka yi, ya taimaka wajen ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Hamas da Isra'ila da ta dakatar da fadan kusan wata guda.

0721 GMT — Hamas ta shirya musayar fursunoni a karo na shida da Isra’ila

Bangaren kungiyar Hamas da ke ɗauke da makamai ya fara shirye-shiryen yin musayar fursunoni da Isra'ila a karkashin kashi na daya na yarjejeniyar tsagaita bude wuta da ta fara aiki a ranar 19 ga watan Janairu.

A cewar wakilin Anadolu, an girke mambobin ƙungiyar a Khan Younis da ke kudancin Gaza a shirye-shiryen miƙa mutanen Isra'ila da aka yi garkuwa da su ga kungiyar agaji ta Red Cross ta kasa da kasa.

TRT Afrika da abokan hulda