Dan majalisar dokokin Isra’ila kuma mamban Jam’iyyar Likud – makusancin Firaministan Benjamin Netanyahu ya janyo guna-guni da bacin rai a duniyar Musulmai kan shawarar da ya bayar cewa a raba Masallacin Kudus da ke Gabashin Birnin Kudus din da aka mamaye tsakanin Musulmai da Yahudawa.
A karkashin shawarar ta mamban Knesset Amit Haveli, bangaren kudu na masallacin zai zama mallakin Musulmai masu ibada, yayin da Yahudawa kuma za su dauki bangaren tsakiya da arewacin Masallacin, ciki har da kubbar karfe mashahuriya, wadda aka fi kira da Qubbat Al-Sakhra.
Bayanan da kafafen yada labarai suka ruwaito na cewa Halevi na son a kwace matsayin kula da waje na uku mafi muhimmanci ga Musulmai a duniya daga hannun Jordan – matakin da zai iya lalata zaman lafiyar da aka dade da shi a Gabas ta Tsakiya.
Halevi ya ce “Zunubi ne ga tarihi” a bai wa kasar waje kula da wajen da yake cikin kasar Isra’ila.
Halevi na kuma son a dinga bai wa Yahudawa damar zagaya dukkan yankunan Masallacin da shiga kofofinsa kamar yadda ake bai wa Musulmai, maimakon a bar musu kofar Mughrabi da ke kudu maso-yammacin Masallacin.
A lokacin da ba a san shi sosai ba kamar sauran mambobi masu tsagwaron son rai, Halevi na ta kokarin bayyana kansa da daga martabarsa ta hanyar daukar matakin sanar da shirye-shiryensa don jan hankalin masu tsaurin ra’ayi.
A watan da ya gabata, ya bi sahun dubban masu tsaurin ra’ayi ‘yan kishin kasa da suka yi gangamin murnar ranar da Isra’ila ta kwace garin mai tsarki a 1967.
‘Ingiza hatsaniya’
A lokacin da ba a da tabbacin ko gwamnati za ta amince da shawarwarin na Halevi, tuni dai shawarar ta cimma manufarta ta janyo hatsaniya a tsakanin Falasdinawa Musulmai.
Ya yi ikirarin cewar tun da Kubbar na bangaren tsofaffin wuraren ibada na farko da na biyu, to sai wajen ya zama mallakin Isra’ila.
Ya ce “Wannan ne yanki mafi yawa na tsaunin, kuma abu mafi fifiko ga Yahudawa saboda tsarkin wajen”.
Halevi ya kuma ce Musulmai masu ibada za su iya ci gaba da Sallah a bangaren Kudancin Kudus.
Ya jaddada cewa “Idan suka yi ibada a nan, hakan zai sanya dukkan tsaunin mai tsarki ba zai zama mallakar Musulmai ba. Bai taba zama hakan ba, ba zai zama ba kuma.”
“Za mu dauki bangaren arewa tare da yin ibada a can. Dukkan tsaunin na da tsarki a wajen, kuma inda kubbar karfe take nan ne dakin bautarmu yake. Wannan ne zai zama mahangarmu. Wannan kalami ne na kasa kuma na tarihi,” in ji Halevi.
Amma wannan muhawara ba ta yi wa Musulmai dadin ji ba, ciki har da Falasdinawa.
A yanar gizo, Musulmai sun dinga kira da a nuna tirjiya ga Haleevi.
Wani mai amfani da Twitter ya rubuta “Sabon mataki na bangare daya da ba ya cikin dokokin kasa da kasa”.
Musulmai na kiran wajen bautar da sunan “Haramussharif” ko kewayen Al Aqsa.
Sun amince da dukkan wajen na da tsarki, dukkan Masallacin da kewayensa, kubbar dutse ne da aka gina a lokacin khalifancin Umayyawa karkashin Sarki Abdulmalik.
Falasdinawa masu zargin Isra’ila da kokarin “Yahudantar” da gabashin Jerusalem, inda Kudus yake, sannan suna kokarin goge Musulunci da Larabawa daga yankin.
Kutsa kai Masallacin Kudus
Kewayen Masallacin Kudus ya zama wajen da dakarun Isra’ila da ‘yan kama guri zauna ke yawan kai wa hari tsawon shekaru. Kuma wadannan abubuwa na rura wutar rikici ne kawai musamman a ‘yan watannin nan.
A watan Afrilu, sama da Yahudawa ‘yan kama guri zauna 1,500 ne suka kutsa Masallacin Kudus da ke Gabashin Kudus da aka mamaya a yayin ranar hutu ta Yahudawa ta Passover.
A yayin al’amarin, Musulmai masu ibada a masallacin sun zargi mahukuntan Isra’ila da kutsa kai cikin kewayen masallacin.
A tarihi, Jordan ce ke kula da bangaren da Musulmai ke ibada a masallacin da ke Gabashin Birnin Kudus.
A 1994 ta sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Isra’ila, wadda ta tabbatar da rawar takawa wajen zaman lafiyar kewayen Masallacin na Kudus.
Idan har Halevi zai samu yadda yake so, to za a sauya wannan mataki. Kuma ba lallai Netanyahu ya nuna tirjiya sosai ba game da hakan.
Sashe na 9 na yarjejeniyar ya bayyana cewa dole ne Isra’ila “Ta yi aiki da wannan yarjejeniya” ta Masarauta game da “Wajen Ibadar Musulmai da ke Jerusalem” kuma “A lokacin da ake tattaunawar daukan matakin karshe, Isra’ila za ta bayar da fifiko ga rawar da Jordan ke takawa tsawon tarihi.”
Wata yarjejeniya da aka kulla a 2013 ta ayyana yadda mahukuntan Falasdinu suka amince da rawar da Jordan ke takawa a wajen ibadar Musulmai da Kiristoci a Jerusalem.
A hakikanin gaskiya, masu suka na bayyana gwamnatin Netanyahu ba ta aiki da wadannan yarjeniyoyi na kare martabar wajen da barin sa yadda doka ta tanada.
A kokarin da yake na kara yawan magoya, Netanyahu na kusanta tare da hada kai da masu tsaurin ra’ayin addini daga cikin Yahudawa, wadanda ke kira da a kwace wannan matsayi da Jordan ke da shi, wanda suke kira “Kuskure a tarihi”.
An ruwaito Halevi na cewa “Wannan mummunan kuskure ne. Ya zama dole a rushe wannan abu. Na san cewa yarjejeniya ce tsakanin kasashe, amma ya zama lallai mu kawar da ita. Tana bukatar sauyi ko da hakan zai dauki lokaci.”
A lokacin da Musulmai ke shan wahala daga gwamnatin masu tsaurin ra’ayi ta Netanyahu a yankunan da aka mamaye, wannan mataki zai kara janyo karuwar hare-haren Yahudawa a kan Musulmai ne kawai.