Wani bidiyo wanda a cikinsa ake zargin Yahudawa suna tofa yawu a ƙasa kan wasu Kiristoci masu wucewa dauke da katakon da aka gicciye a Gabashin Birnin Kudus da aka mamaye ya jawo ce-ce-ku-ce da Allah wadai.
Tofar da yawun, wanda Kiristocin da ke zaune a birnin suka bayyana a matsayin abin damuwa, na daga cikin lamari na baya-bayan nan na ƙiyayyar addini, wanda ya sa har Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar suka fusata.
'Yan sandan Isra'ila a ranar Laraba sun ce sun kama mutum biyar wadanda suke da alaka da lamarin inda suka kafa wani kwamiti na musamman na bincike domin magance ƙaruwar ƙorafen-ƙorafen Kiristoci marasa rinjaye a yankin.
Ba a bayyana ko su wane ne mutanen da aka kama ba.
Tun bayan da gwamnati mai ra'ayin 'yan mazan jiya ta soma mulki a bara, an ta nuna damuwa tsakanin malaman addini kan yadda ake samun ƙaruwar cin mutuncin Musulmai da Kiristoci.
Bayan mamaye ta a 1967, Isra'ila ta mamaye Gabashin Birnin Kudus har da tsohon birnin, wani yunƙuri da kasashen duniya ba su taba amincewa da shi ba.
Tsohon birnin na Kudus ya kasance daya daga cikin wuraren da ake yakin Isra'ila da Falasdinawa, sannan ake zaman fargaba tsakanin mabiya addinan.
Mutane da dama sun bayyana cewa wasu jami'an gwamnatin Yahudawa daga ciki har da Ministan Kudi Bezalel Smotrich da Babban Ministan Tsaro, Itamar Ben Gvir sun karfafa gwiwar Yahudawa domin yin tsattsauran ra'ayi.
Akwai kusan Kiristoci 15,000 a Birnin Kudus a halin yanzu, wadanda akasarinsu Falasdinawa ne da ake ganin an mamaye su.
Ofishin Netanyahu a ranar Talata ya jaddada cewa Isra'ila "tana iyakar kokarinta domin tabatar da 'yancin addini a duka wuraren bauta."
"Ina Allah wadai da duk wani kokarin barazana ga masu bauta, kuma za mu jajirce domin daukar matakin kan hakan," in ji shi.
Bidiyon tofa yawun wanda wani dan jaridar Isra'ila na jaridar Haaretz ya dauka, na nuna wani rukuni na Kiristoci masu sauke farali suna fara wani tattaki.
A bidiyon, an ga Kiristocin dauke da wani makeken katako na giciye suna fita daga wai gini wanda suka yi amannar shi ne Yesu ya dauka kafin gicciye shi.
A lokacin da suke kan hanya, Yahudawan wadanda ke sanye da bakaken kaya da bakaken huluna sai suka ci karo da Kiristocin masu ibada.
A nan ne Yahudawan suka rinka tofar da yawu a gefen Kiristocin masu wucewa.
Domin kara ruruwar wannan wuta, sai Elisha Yered, wanda daya daga cikin riƙaƙƙun Yahudawa ne kuma tsohon mai bayar da shawara ga wani dan majalisa a gwamnatin Netanyahu ya fito ya ƙare masu tofa yawun inda ya ce tofa yawu ga malaman Kiristoci a coci "al'ada ce ta Yahudawa".
Yered wanda ake zargi da hannu a kashe wani dan Falasdinu mai shekara 19 na karkashin daurin talala.
Duk da cewa bidiyon da kalaman Yered sun bazu a shafukan sada zumunta, lamarin ya kara girma. Ministan Harkokin Wajen Amurka Eli Cohen ya bayyana cewa tofa yawu "ba ta cikin dabi'ar Yahudawa."
Ministan harkokin addini na Isra'ila Michael Malkieli, shi ma ya bayyana cewa tofa yawun "ba ya cikin koyarwar Attaurah."