Mahafiyar wani Bafalasdine da dakarun Isra'ila suka kashe a Gabar Yammacin Kogin Jordan yayin da take nuna alhinin kisansa ranar  17 ga watan Agusta, 2023. (Hoto: AFP)

Daruruwan fursunoni Falasdinawa da ke daure gidajen yarin Isra'ila sun soma yajin cin abinci na sai-abin-da-hali-ya-yi, a cewar wata kungiyar kare hakkin dan adam.

Fursunoni kusan 1,000 da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila daban-daban sun soma yajin cin abinci ne da misalin karfe bakwai na maraice "domin bijire wa rashin mutuncin hukumomin gidajen yarin", a cewar wata sanarwa da Ahmed al Kudra, daraktan ofishin the Palestinian Prisoners Press Office, da ke bibiyar halin da Falasdinawa daurarru ke ciki, ya fitar ranar Alhamis.

Kudra ya yi kira ga Falasdinawa su hada kai sannan su "fantsama kan tituna" domin nuna goyon baya ga fursononin.

Ya bukaci Falasdinanawa da ke zaune a Gabar Yammacin Kogin Jordan su yi zanga-zanga domi bijire wa "wulakancin" da ake yi wa fursunonin.

An soma tayar da jijiyoyin wuya bayan hukumomin gidan yarin Negev da ke kudancin Isra'ila sun kai samame a yanki na uku da na hudu na gidan yarin sannan suka kwashe wasu fursunoni suka kai su wani yankin, a cewar wata sanarwa ta daban ta hadin-gwiwa da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka fitar.

Har yanzu hukumomin Isra'ila ba su ce komai a kan wannan batun ba.

Akwai Falasdinawa kusan 5,000 a gidajen yarin Isra'ila, a cewar alkaluman da Falasdinawa suka fitar, cikin su har da akalla fursunoni 1,200 da ake tsare da su ba tare da an tuhume su da aikata wani laifi ba.

Falasdinawan da ke daure a gidajen yarin Isra'ila sun kwashe shekaru suna bijire wa mummunan halin da suke ciki da kuma kira da a sake su.

TRT World