Mazauna Falasdinu na bukatar lasisi kafin fita neman magani. Hoto/Reuters

Irin takunkumin da Isra’ila ta saka wa Falasdinu da kuma karuwar takunkumi kan kudi na tasiri matuka kan tattalin arzikin Falasdinawa da kuma hana su samun damar kiwon lafiya, kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana.

A wani rahoto mai taken “Racing Against Time” wanda Bankin Duniya ya wallafa, ya ce tattalin arzikin Falasdinu baki dayansa na kasa da abin da ya kamata, inda ake fargabar rashin samun ci-gaba a matsakaicin kudaden da ‘yan kasar ke samu.

Talauci na karuwa a yankunan Falasdinu, inda daya bisa hudu na Falasdinawa ke rayuwa a cikin talauci, kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana.

Takunkumin da Isra’ila ta saka kan jigila da kasuwanci a Gabar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye, da rufe hanyoyi da aka yi a Zirin Gaza da kuma rabuwar kai da aka samu tsakanin yankunan Isra’ila biyu na daga cikin dalilai da dama da suka saka tattalin arzikin Falasdinu a cikin barazanar tattalin arziki, in ji rahoton.

“Takunkumi kan kudi na tasiri matuka kan kiwon lafiya a Falasdinu da kuma musamman kan yadda za ta yi fama da matsalar cututtuka marasa yaduwa,” in ji Stefan Emblad, daraktan Bankin Duniya na Yamma da Kogin Jordan da Gaza.

Bukatar fita waje neman maganin cutar daji ko ciwon zuciya ko haihuwa da sauransu na fuskantar cikas sakamakon wasu matsaloli na gudanarwa, in ji sanarwar.

“Lamarin ya fi kamari a Gaza, inda take fama da karin karancin kayayyakin kiwon lafiya, marasa lafiya na wahala wurin samun damar fita waje domin neman lafiya a lokuta da dama,” in ji sanarwar.

“Alkaluman bincike sun nuna cewa mamayar Gaza na da tasiri kan mace-mace, inda wasu marasa lafiya ke mutuwa saboda tsawon lokacin da ake dauka kafin samun damar fita.”

Dubban Falasdinawa daga Gabar Yamma da Kogin Jordan da Zirin Gaza suke tsallakawa zuwa Isra’ila a duk shekara domin neman lafiya, sakamakon karancin kayayyakin aiki a Falasdinun.

Isra’ila ta mamaye Gabar Yamma da Kogin Jordan tun a 1967, wanda wuri ne da ke dauke da Falasdinawa miliyan uku.

Ta mamaye wurin ne a lokacin wani yaki na kwanaki shida inda a lokacin ne ta mamaye Zirin Gaza.

A bara, Isra’ila ta bayar da dama ga sama da mutum 110,000 daga Gabar Yamma da Kogin Jordan su je kasar neman magani, kamar yadda ma’aikatar tsaron Isra’ilar ta bayyana.

Sama da mutum 17,000 da aka ba damar sun fito ne daga Gaza, inda sama da mutum miliyan 2.3 suke zama.

AFP